Me ya sa Amurka ke ƙoƙarin hana mutumin da ya kitsa harin 9/11 amsa laifi?

- Marubuci, Alice Cuddy
- Aiko rahoto daga, Guantanamo Bay
- Lokacin karatu: Minti 6
Mutumin da ake zargi da kitsa harin ta'addancin da aka kai Amurka a ranar 11 ga watan Satumba wanda aka fi sani da 9/11, ba zai amsa laifi ba a ranar Juma'a, bayan da gwamnatin Amurka ta yi ƙoƙarin hana ci gaba da yarjejeniyar amsa laifi da aka cimma a shekarar da ta gabata.
Khalid Sheikh Mohammed, da ake masa laƙabi da KSM, zai gabatar da wata buƙata a wata kotun sauraron laifukan yaƙi a gidan yarin Guantanamo Bay a kudu maso gabashin ƙasar Cuba, inda ya shafe kusan shekara 20 tsare a gidan yarin sojoji.
Mohammed shi ne mafi shahara wajen aikata laifi a gidan yarin na Guantanamo kuma ɗaya daga cikin na ƙarshe da aka tsare a sansanin.
Sai dai da yammacin ranar Alhamis, kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya ta dakatar da zaman sauraron shari'ar da aka tsara yi wanda a nan za a duba buƙatun gwamnati na soke yarjejeniyar amsa laifi ga Mohammed da wasu mutum biyu da ke da hannu a harin, wanda ta ce zai iya yin illa babba a gare ta da kuma jama'a.
Tawagar alƙalai uku ta ce bai kamata a yi tunanin tsaikon a matsayin wani hukunci kan cancanta ba, amma an yi ne domin bai wa kotu lokaci na samun ƙarin bayanai da kuma sauraron bahasi game da hanzarta shari'ar.
Jinkirin na nufin a yanzu batun zai koma ƙarƙashin gwamnati mai jiran gado ta Donald Trump.
Me aka tsara yi a wannan makon?
A wani zaman sauraron shari'ar da safiyar ranar Juma'a, an tsara Mohammed zai amsa laifin kai hare-haren ranar 11 ga watan Satumban 2001 bayan da masu kutse suka ƙwace iko da aƙalar wasu jirage tare da karkatar da su inda suka faɗa kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke New York da ma'aikatar tsaron Amurka da ke wajen Washington. Wani jirgin kuma ya faɗa kan wani fili a Pennsylvania bayan da fasinjojin suka bijire wa masu kwacen jirgin.
An tuhumi Mohammed da laifukan da suka shafi haɗin baki da kisa inda aka lissafa mutum 2,976 cikin takardar tuhumar.
A baya ya ce shi ne ya kitsa hare-haren na "9/11 daga farko har ƙarshe" - inda ya yi tunanin ya horar da matuƙan jirgi da za su tuƙa jiragen da za su kutsa cikin gine-gine da kuma gabatar da shirin ga Osama bin Laden, jagoran ƙungiyar al-Qaeda, a tsakiyar shekarun 1990.
An tsara zaman shari'ar ta ranar Juma'a a wani kotu da ke sansanin Guantonamo inda iyalan waɗanda harin ya halaka da kuma ƴan jarida za su zauna suna kallon yadda zaman zai wakana.

Asalin hoton, Khalid Sheikh Mohammed
Me ya sa waɗannan abubuwan ke faruwa shekara 23 bayan hare-haren 9/11?
An shafe fiye da shekara 10 ana zama gabanin sauraron shari'ar, da aka yi a wata kotun soji da ke sansanin sojojin ruwa, da tambayoyi suka ƙara dagula bayanin ko cin zarafin da Mohammed da sauran waɗanda ake zargi suka fuskanta a lokacin da suke tsare a Amurka ya lalata hujjoji.
Bayan kama shi a Pakistan a 2003, Mohammed ya shafe shekara uku a wani gidan yarin hukumar leƙen asiri ta Amurka inda ake azabtar da shi ta hanyar kwarara masa ruwa yayin da aka rufe masa baki da hanci da nufin samun bayanai. An yi masa haka ne sau 183.
Akwai kuma dabarar tatsar bayanai da ta haɗa da hana shi barci da kuma tilasta masa yin tsirara.
Karen Greenberg, wadda ta rubuta littafin "The Least Worst Places": Yadda sansanin Guantanamo ya zama gidan yari mafi haɗari a duniya, ta ce kasancewar an azabtar da waɗannan mutane ya ƙara daɗa sarƙaƙiyar tuhume-tuhumen," in ji ta.
Me yarjejeniyar amsa laifin ta ƙunsa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ba a saki cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da aka cimma da Mohammed da mutanen da suka taya shi aikata hare-haren ba.
Mun san cewa yarjejeniyar na nufin ba zai fuskanci shari'a kan hukuncin kisa ba.
A wani zama da aka yi a ranar Laraba, tawagar lauyoyinsa sun tabbatar da cewa ya amince ya amsa tuhume-tuhumen da aka yi masa. Mohammed ya yi magana a kotun ta hannun lauyoyinsa yayin da suke nazari kan yarjejeniyar, suna yin ƴan gyare-gyare ga wasu kalmomin mai gabatar da ƙara da alƙali.
Idan aka tabbatar da yarjejeniyar kuma kotu ta amince da ita, matakai na gaba da za a ɗauka sun haɗa da naɗa masu taimaka wa alƙali soji da za su saurari shaidu a zaman shari'ar.
A zaman na ranar Laraba, lauyoyi sun bayyana haka amtsayin wata hanyar sauraron shari'a a bainar jama'a inda mutanen da suka tsira da iyaan waɗanda aka kashe za su samu damar bayar da bahasi.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, iyalai za su kuma samu damar yi wa Mohammed tambayoyi, da za a buƙaci ya amsa tambayoyinsu bisa gaskiya ba tare da noƙe-noƙe ba, in ji lauyoyi.
Ko da an amince da yarjejeniyar, zai kasance watanni da dama gabanin zaman shari'ar inda za a yanke hukunci.

Asalin hoton, Reuters
Me ya sa gwamnatin Amurka take ƙoƙarin hana yarjejeniyar?
Sakataren harkokin wajen Amurka, Lloyd Austin ya naɗa babban jami'in da ya sa hannu kan yarjejeniyar. Amma a lokacin da aka sa hannu kan yarjejeniyar yana wata ziyara kuma rahotanni sun ce lamarin ya zo masa da mamaki, a cewar jaridar New York Times.
Kwanaki bayan nan, ya yi ƙoƙarin soke ta, inda cikin wata takarda ya ce "nauyin irin wannan mataki ya kamata ya rataya a wuyana a matsayin babban jami’in gwamnati."
Sai dai, duka alƙalan kotun soji da alƙalan kotun ɗaukaka ƙara sun yanke cewa an amince da yarjejeniyar sannan Mista Austin ya ɗauki mataki a makare.
A wani yunƙurin kuma, a makon da ya gabata, gwamnati ta nemi kotunan ɗaukaka ƙara na tarayya da su saka baki.
Bayan sanar da cimma yarjejeniyar a bara, Sanata Mitch McConnell, wanda a lokacin shi ne shugaban masu rinjaye na jam'iyyar Republican a majalisa, ya fitar da wata sanarwa da ta bayyana yarjejeniyar a matsayin jinginar da nauyin gwamnati na kare Amurka da tabbatar da adalci.
Me iyalan waɗanda suka mutu a harin suka ce?
Wasu iyalai na mutanen da aka kashe a hare-haren sun caccaki yarjejeniyar inda suka ce an yi sassauci ko kuma ba a yi ta a fayyace ba.
Da take magana da BBC, Terry Strada, wadda mijinta Tom ya mutu a hare-haren, ta bayyana yarjejeniyar a matsayin bai wa tsararrun da ke Guantanamo abin da suke so.
Ms Strada, shugabar ƙungiyar iyalan mutanen da suka mutu a hare-haren 9/11, ta ce "wannan nasara ce ga Khalid Sheikh da sauran mutum biyu, nasara ce a gare su."
Sauran iyalan sun ce matakin gwamnati ya ba su kunya saboda matakinta na baya-bayan nan na saka baki a lamarin.
Stephan Gerhardt, wanda ƙaninsa Ralph ya mutu a hare-haren, ya je Guantanamo domin kallon yadda Mohammed zai amsa laifi.
"Mece ce ribar gwamnatin Biden? To shari'ar za ta tsawaita zuwa sabuwar gwamnati. A kan me? Ku yi tunanin iyalan. Me ya sa ake jinkirta wannan lamari? in ji shi.
Mista Gerhardt ya shaida wa BBC cewa yarjejeniyar ba nasara ba ce ga iyalan, amma a cewarsa, lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen batun ta hanyar samun mutanen da laifi."
Me ya sa ake zaman shari'ar a Guantanamo?
Tun shekarar 2006 ake tsare da Mohammed a wani gidan yarin sojoji da ke Guantanamo.
An buɗe gidan yarin shekara 23 baya - ranar 11 ga Janairun 2002 - lokacin yaƙi da ta'addanci bayan hare-haren 9/11, a matsayin wuri na tsare mutanen da ake zargi a aikata ta'addanci.
Galibin waɗanda aka tsare ba a taɓa tuhumar su ba sannan gidan yarin sojojin ya fuskanci suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil‘adama da Majalisar Ɗinkin Duniya kan yadda take kula da mutanen da aka tsare. Galibin mutanen an tasa ƙeyarsu ko ma an sauya masu matsuguni a wasu ƙasashen.
Gidan yarin a yanzu yana ɗauke da mutum 15 - mafi ƙarancin adadi da aka taɓa samu a tarihin gidan. Duka mutum 15 ɗin ban da shida, an tuhume su ko ma an same su da laifin aikata laifukan yaƙi.











