Mece ce makomar al-Qaeda bayan kashe shugabanta?

al-Zawahiri da Osama

Asalin hoton, CNN VIA GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Osama (a dama) da magajinsa al-Zawahiri (a hagu) duka Amurka ta kashe su

Nasarar da Amurka ta bayyana kwatsam cewa ta yi, ta hallaka shugaban kungiyar al-Qaeda Dr. Ayman al-Zawahiri a karshen mako ita ce ta bijiro da wannan tambaya da ya kamata a ce an san amsarta:

Yanzu mece ce makomar kungiyar da ya bari? Shin wai ma mece ce ita wannan kungiya al-Qaeda kuma ma wai tana da wani tasiri ne a wannan shekara ta 2022.

 Idan muka yi waiwaye kan ita wannan kungiya, mu fara da sunanta Al-Qaeda wadda kalma ce a Larabci da ke nufin ‘’sansani’’.

Kungiya ce dai ta ‘yan ta’adda wadda aka haramta, wadda kuma burinta shi ne kai hari kan duk wasu muradu na kasashen Yammacin duniya a ko’ina suke tare kuma da neman ganin bayan duk wasu gwamnatoci da ke da alaka da Yamma, ko take ganin ba sa bin tafarkin akidar fassarar Musulunci da ita kungiyar ta yi, walau a Afirka suke ko a Asia.

An dai kirkiri kungiyar ne a karshe-karshen shekarun 1980 a yankin kan iyakar Afghanistan da Pakistan, daga cikin ragowar sojojin sa-kai na Larabawa, wadanda suka je can domin yakar tsohuwar Tarayyar Soviet (Rasha) da ta mamaye Afghanistan.

 A gomman shekarun da suka gabata al-Qaeda ta yi suna kusan ko’ina a duniya, inda ta kai ana yi mata kallon babbar barazana kuma abokiyar gaba ta farko ga kasashen Yamma.

 Wannan kuwa ya kasance ne saboda irin nasaraorin da ta samu na kai hare-hare na gaba-gadi ko kunar bakin-wake a kan muradun Yamma.

 Wanda hakan ya sa ta rika samun mabiya masu tsattsauran ra’ayi da ke da burin kai irin wadannan hare-hare ko da kuwa a bakin ransu ne.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

 A 1988 ta kai jerin hare-haren bam na kusan lokaci daya a kan ofishin jakadancin Amurka da ke Kenya da kuma wanda ke Tanzania, inda ta hallaka yawanci fararen hula ‘yan Afirka.

 A shekara ta 2000 ta kai hari da wani dan karamin jirgin ruwa da ta shake da bama-bamai, inda ta kara shi a jikin katafaren jirgin ruwa na yaki na Amurka (USS Cole ) a tashar jirgin ruwa ta Aden, inda ta kashe mutum 17, tare da lalata jirgin na biliyoyin dala.

 A ranar 11 ga watan Satumba shekara ta 2001, kungiyar ta kai harin da ya girgiza Amurka tare da tayar da hankalin duniya.

 Kungiyar ta yi fashin jiragen sama hudu a samaniyar Amurka, inda ta karkatar da biyu ta kara su a tagwayen ginin cibiyar kasuwanci ta duniya da ke New York.

 Harin da ya rushe wadannan tagwayen gine-gine tare da haddasa gobara a wurin.

 'Yan kungiyar sun kuma yi nasarar kara wani jirgin a kan ginin hedikwatar tsaron Amurka, Pentagon.

 Yayin da fasinjojin daya jirgin suka ci karfin ‚yan kungiyar da suka yi fashin jirgi na hudu, abin da ya kai ga faduwar jirgin a wani fili, ya hallaka dukkanin mutanen da ke cikinsa.

 A dukkanin wadannan hare-hare na ranar kusan mutum 3,000 ne suka rasa ransu.

An yi wa wannan rana da hari lakabin goma sha daya ga Satumba ‘’9/11’’

 Wannan hari ya kasance mafi muni da aka taba kai wa Amurka a cikin kasarta.

 Kuma shi ne ya sa Amurka ta daura damarar yaki da kungiyar da sauran wasu gwamnatocin kasashe masu alaka da kungiyar tsawon shekara 20, yakin da yake cike da takaddama.

 Bisa kafewar cewa an shirya wannan hari ne daga sansanin al-Qaeda da ke tsaunukan Afghanistan, inda gwamnatin Taliban ta ba shugabannin kungiyar mafaka, hakan ya sa Amurkar da kawayenta suka kuduri aniyar farautar ‘yan kungiyar.

 Daga nan Amurkar da Birtaniya suka mamaye wannan kasa inda suka kori gwamnatin Taliban, kuma suka kori ‘yan al-Qaeda.

 Amurkar ta dauki wata shekara goma kafin ta iya gano inda shugaban kungiyar Osama Bin Laden yake, ta kuma kashe shi a Pakistan a watan Mayu na 2011.

Sabon shugabancin kungiyar

Bayan kashe Osama Bin Laden, nan da nan kungiyar ta nada sabon shugaba, wanda ya kasance mataimakin Osaman.

 Wannan sabon shugaba shi ne Dr Ayman al-Zawahiri, kwararrren likitan ido, wanda hukumar leken asiri ta Amurka CIA, ta hallaka ta harin sama da karamin jirgi maras matuki a karshen mako.

A tsawon jagorancinsa na shekara 11 al-Zawahiri ko kusa bai samu irin fice da kwarjinin wanda ya gada ba daga wurin mabiya matasan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi da ke cike da burin aikata ta'addanci.

Kafin wani lokaci sai ya kasance kungiyar ta rika rasa mabiya, inda matasanta ke sauya sheka zuwa wata sabuwar kungiyar da kusan ta fito daga cikinta.

Wannan sabuwar kungiya mai tsattsauran ra'ayi da tsabar ta'addanci ta kira kanta Islamic State ko ISIS wato Daular Musulunci a Iraki da Syria.

Kasancewar al-Zawahiri a wani gida da ke kusa da fadar gwamnatin Afghanistan karkashin Taliban, inda Amurka ta gano har ta hallaka shi, hakan ya nuna cewa Taliban tana nan da alakarta da Al-Qaeda daram.

Samun gindin-zama a Afirka

A wuraren da a da kungiyar ta al-Qaeda ba ta da girma, a yau ta yadu inda take da 'yan mabiya nan da can a kasashen duniya, yawanci wadanda ba su da wata tartibiyar gwamnati ko kuma gwamnatin take da rauni.

Misali a Somalia, kungiyar "al-Shabab" da ke da alaka da al-Qaeda har yanzu ita ce kungiyar masu ikirarin jihadi da ke da karfi a can.

Nahiyar Afirka a yanzu ta zama wani sabon fage da kungiyoyin masu ikirarin jihadi kamar su al-Qaeda da ISIS, musamman a wurare irin su yankuna irin su Sahel da ke arewa maso yammacin Afirka ke samun gindin zama.

Sai dai ba wai kawai suna yaki ne domin kawsar da gwamnatocin da suke yi wa kallon na kafirci ba, suna ma yakar junansu ne, inda abin ke shafar farar hula da ba su da alaka da su.

Kaka-gida a Gabas ta Tsakiya

Har yanzu Al-Qaeda na ci gaba da kasancewa kungiyar ta'addanci ta Gabas ta Tsakiya.

Bin Laden dan Saudiyya ne shi kuwa al-Zawahiri dan Masar ne, wannan ya nuna shugabancin kungiyar kusan yana karkashin Larabawa ne duka.

Kuma har yanzu kungiyar na ci gaba da kasancewa da tasiri a arewa maso yammacin Syria inda a lokaci zuwa lokacin hare-haren Amurka kan kai ga maboyar shugabanninta.

Sabon shugaba

Sakamakon mutuwar al-Zawahiri, watakila a yanzu al-Qaeda ta yi kokarin sake farfado da ayyukanta karkashin wani sabon shugabancin da kuma sabbin dabaru.

Hukumar leken asirin da ba ta san abin da take yi ba ne kadai za ta zartar cewa barazanar kungiyar ta zo karshe da mutuwar shugabanta.