Me ya sa wasu ke zuwa bahaya nan take bayan cin abinci?

    • Marubuci, Siraj
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Tamil
  • Lokacin karatu: Minti 4

Matsuwar jin bahaya mintoci kaɗan bayan kammala cin abinci, matsala ce da mutane da dama ke fuskanta a kowace rana.

Wannan ya aza ayar tambaya cewa ko abincin da muka ci ya narke yadda ya kamata?

A cewar ƙwararru kan lafiya, dalili guda ka wanna matsala shi ne cin abinci kaɗan ko kuma yawan abinci a wurin aiki da kuma cin abin da ka fi so lokaci da kake hutu.

Amma tambayar ita ce, shin babu matsala ne idan aka je bahaya da zarar an kammala cin abinci, ko kuma alamce ta ciwo? Ko matsala ce yin bahaya da yawa a rana?

A wannan labari, za ku samu amsoshin waɗannan tambayoyi tare da taimakon ƙwararrun lafiya da kuma bincike.

Ƙwararren likita kan ciki da ke Chennai a Indiya, Dakta Mahadevan ya ce, "Ana kiran zaƙuwar ji bahaya nan take bayan cin abinci da 'gastrocolic reflex'. Sai dai mutane da dama ba sun yi wa lamarin cewa idan aka ci abinci nan take yana komawa kashi gurguwar fahimta, amma ba haka yake ba."

Shin abinci na komawa bahaya nan take?

A cewar wani bincike, yana ɗaukar sa'a 10 zuwa 73 kafin a yi kashin abinci da aka ci.

Sai dai, wannan lokaci ya dogara kan abubuwa da dama, kamar shekarun mutum, jinsi, nauyi da kuma irin abinci da ake ci.

Idan abinci ya kai ga ciki, yana wucewa zuwa cikin hanji sannan ya narke zuwa kashi. Hakan ne yake sa mutum ya ji yana son fitar da bahaya.

Idan kashi ya wuce, ana samun wuri a babban hanji, abin da ke ƙara inganta narkewar abinci.

Dakta Mahadevan ya ce, "wannan abu ne da jiki ya saba yi, wanda aka fi gani a wurin ƙananan yara. Wannan shi ya sa a yawan lokuta ƙananan yara ke kashi da zarar sun gama shan madara.

Wannan na faruwa ne mintoci kaɗan zuwa sa'a ɗaya bayan cin abinci. A cewar wani bincike, am fi ganin wannan yanayi a wurin yara, yayin da yake afkuwa a hankali a wajen manya.

Likitan ya bayyana cewa ba matsala bane idan aka ji haka, amma idan aka kasa sarrafa kai ko kuma zaƙuwar na da ƙarfi sosai, to alama ce ta matsala da ke alaƙa da ciwo ciki ko kuma ciwon hanji.

Dakta Mahadevan ya ƙara da cewa 'matsalar bahaya' babbar matsala ce da ke shafar ciki, amma za a iya magance ta.

Yaya alamomin suke?

A cewar Hukumar Lafiya ta Birtaniya, matsala ko wahala yayin bahaya, abu ne da yake shafar ciki. Alamomin sun haɗa da:

• Ciwon ciki ko zafi, inda mutum zai riƙa jin matsuwar yin kashi

• Yawan sinadarin gas da gyambon ciki

• Amai da gudawa da yawan bahaya

• Jin ciki bai ragu ba ko da bayan an yi bahaya

A cewar, shawara NHS ta bayar, ta ce idan waɗannan alamomi suka ki tafiya sama da mako huɗu, to akwai buƙatar ganin likita.

Babu ƙarara kan abin da ke janyo wannan matsala, sai dai waɗannan abubuwa za su iya janyo matsalar ta tsananin ciwon ciki:

• Shan barasa

• Saka sinadarin caffeine (a cikin shayi da gahawa)

• Abincin da aka sarrafa

• Gajiya da damuwa

• Yawan amfani da magungunan kashe ƙwayoyin bacteria.

Wasu ƙarin matsaloli da tsananin ciwon cikin yake haddasa ya haɗa da:

• Matsalar sinadarin gas

• Gajiya da rashin ƙarfin jiki

• Yawan jin amai

• Ciwon baya

• Jin fitsari akai akai

• Mutum ya ji kamar bai gama yin fitsari ba

A cewar wani bincike, kashi biyar zuwa goma na al'ummar duniya na fama da matsalar ciwon ciki. Mutum ɗaya cikin uku da ke da matsalar na kuma fama da matsalar ciwon damuwa.

Dakta Mahadevan ya ce, "Za a iya magance waɗannan alamomi ta hanyar sauya irin abincin da ake ci da kuma salon rayuwa, har ma da samun hutu. Idan alamomin suka tsananta, ya fi kyau a je a ga likita."

Shin wannan zai iya zama alama ta ciwon hanji?

Likitan da ya ƙware kan ɓangaren ciki, Dakta Ravindran Kumaran ya ce, "Wasu mutane na da ɗabi'ar zuwa bahaya da zarar sun gama cin abinci na tsawon shekaru. Idan hakan bai janyo musu matsala ko rashin tsukuni ba, to ba wata matsala ba ce. Amma idan matsuwar jin kashi ta ƙaru sannan ta ki tafiya, to yana da kyau a mayar da hankali."

Dakta Ravindran ya ce, "mutanen da ke zuwa aiki ko makaranta a kowace rana na ganin babu wata matsala zuwa bahaya akai akai. Idan suka tuntuɓe mu, muna ba su shawarar sauya salon rayuwa. A ɗaya gefe, babu wata ka'ida na sau nawa ya kamata a je bahaya a rana. Idan ciwon ciki ya tsananta a nemi shawarar likita."

Da yake ƙara nanatawa kan lamarin, Dakta Mahadevan ya ce, "Idan ka ga sauyi a bahayarka, kada ka yi wasa. Alal misali, yawan tashi da daddare don yin bahaya zai iya zama sauyi mai haɗari. Zai iya kuma zama alama na wasu cutuka."