Wane ne zai jagoranci ƙasar Falasɗinawa idan ta samu ƴanci?

    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic Correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 8

A farkon wannan wata ne, Cibiyar Chatham House ta gayyaci wani jami'in diplomasiyyar Falasɗinawa mai suna Husam Zomlot domin wata tattaunawa.

A baya-bayan nan ƙasar Belgium ta bi sahun Birtaniya da Faransa da wasu ƙasashen Turai wajen alƙawarta amince da kafuwar ƙasar Falasdinu a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York n Amurka. Kuma Dakta Zomlot ya bayyana ƙarara cewa hakan gagarumin ci gaba ne.

"Abin da za ku gani a birnin New York wataƙila shi ne yunƙuri na ƙarshe na amincewa da masalahar kafa ƙasashe biyu,'' in ji shi.

"Ka da mu barin hakan ya kasa faruwa."

Makonni bayan haka, a yanzu hakan na neman tabbata. Birtaniya da Kanada, waɗanda dukansu tsoffin abokan Isra'ila ne, sun ɗauki gabarar tabbatar da hakan.

Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ne ya bayyana matsayar ƙasar cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

A cikin bidiyon, Mista Starmer ya ce ''Sakamakon ƙaruwar yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya, mun ɗauki matakin amincewa da maslahar ƙasashe biyu''.

"Wannan na nufin Isra'ila mai aminci da tsaro, sannan kuma a kafa ƙasar Falasdinu''.

Fiye da ƙasashen duniya 150 ne a baya suka amince da kafa ƙasar Falasɗinu, to amma ana ganin samun amincewar Birtaniya da sauran ƙasashen duniya babban ci gaba ne.

"Falasɗinu ba ta taɓa zama mai ƙarfi baya, kamar yadda ta samu yanzu,'' in ji Xavier Abu Eid, tsoon jami'in Falasɗinawa.

"Duniya na taruwa don mara wa Falasɗin baya," in ji shi.

To amma akwai tambayoyi masu sarƙaƙiya da ke buƙatar amsa, ciki har da wace ce Falasdinu kuma ta cancanci zama ƙasa?

Taron Montevideo na shekarar 1933 ya lissaf wasu sharuɗɗa huɗu na zama ƙasa.

To amma Falasdinawa ka iya ikirarin samu biyu kawai daga ciki: Yawan al'umma mazauna yankin (kodayake yaƙin Gaza ya ɗaiɗaita alu'ummar yankin) da kuma damar shiga dangantakar ƙasashe - kamar yadda Dakta Zomlot ya bayyana.

To amma a ta cika ƙa'idar samun ''keɓantattun iyakoki'' ba

Yayin da har yanzu ba wata yarjejeniya da ke nuna iyakokin yankin (sannan babu zaman lafiya), Yana da wahala a iya sanin makomar Falsdinawa.

Ga su Falasɗinawan kansu, Yankin nasa ya kunshi manyan ɓangarori uku - Gabashin Birnin Ƙudus da Gaɓar Yamma da kuma Zirin Gaza. Kuma dukansu Isra'ila ta yaƙe su a yaƙin kwana shida na shekarar 1967.

Isra'ila ta raba tsakanin Gaɓar Yamma da Zirin Gaza na tsawon kusan shekara 75, tun bayan samun ƴancin kan Isra'ila a 1948.

A Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, wanzuwar sojojin Isra'ila da matsugunan Yahudawa na nufin hukumar Palasɗinawa - wadda aka kafa bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo a shekarun 1990 - tana gudanar da kusan kashi 40% na yankin.

Tun daga shekara ta 1967, An riƙa faɗaɗa matsugunan Yahudawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, lamarin da ya dagula rikicn siyasa da na tattalin arzikin yankin.

A halin da ake ciki kuma, Gabashin Birnin Ƙudus, wanda Falasɗinawa ke ɗauka a matsayin babban birnin ƙasar, ya sha fama da matsugunan yahudawa, wanda sannu a hankali ya raba birnin daga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Tabbas makomar Gaza, na cikin halin rashin tabbas. Bayan kusan shekara biyu na yaƙi, da Hamas ta janyo saboda harin watan Oktoban 2023, da dama cikin yankunan sun ruguje.

Amma kamar dai duk wannan bai wadatar ba, akwai sharaɗi na huɗu da aka gindaya a taron Montevideo don amincewa don amincewa da ƙasa: Gwamnati mai aiki

Kuma wannan shi ne babbar matsalar Falasɗinawa.

'Muna buƙatar sabon shugabanci'

A shekarar 1994, yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Ƙungiyar 'yantar da Falasdinu (PLO) ta haifar da kafa Hukumar Falasɗinawa ta kasa (wanda aka fi sani kawai da Hukumar Falasdinu ko PA), wanda ke gudanar da wani bangare na ikon farar hula akan Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

Tun bayan gagarumin rikicn zubar da jini da ya ɓarke a shekara ta 2007 tsakanin Hamas da babbar kungiyar PLO ta Fatah, gwamnatoci biyu masu gaba da juna ne ke mulkin Falasdinawa a Gaza da kuma Gaɓar yammacin Kogin Jordan, wato Hamas a Gaza da kuma hukumar Palasɗinawa da ƙasashen duniya suka amince da ita a Gabar Yamma da Kogin Jordan, wadda Mahmoud Abbas ke jagoranta.

Wata shekara 77 tun lokacin da aka raba iyakokin ƙasar, da kuma shekara 18 ntun bayan samun rarrabuwar siyasa a yankin: Lokaci mai tsawo tun bayan da Gaɓar Yamma da Zirin Gaza suka rabu.

Ƴansiyasan Falasɗinu su kasance cikin ruɗu na tsawon lokaci, wanda hakan ya sa Falasɗinawa suke taraddudi kan makomarsu, ballanta ma a fara maganar samar da cigaban ƙasar.

Zaɓen shugaban ƙasa da na ƴanmajalisu da aka yi a ƙasar shi ne a shekarar 2006, wanda hakan ke nufin duk wani ɗan yankin da bai wuce shekara 36, bai taɓa kaɗa ƙuri'a a zaɓen yankin ba.

Ɓarkewar yaƙin Gaza a watan Oktoban shekarar 2023, sai lamarin siyaa da shugabancin yankin ya ƙara shiga cikin tsilla-tsilla.

Yanayin luguden wuta da ake yi a yankin, sai ya sa gwamnatin Abbas ta zama tamkar ƴar kallo kawai.

Daɗewa a cikin matsaloli

Yankin ya daɗe yana cikin ruɗun shugabanci.

A lokacin da Yasser Arafat ya koma ƙasar daga gudun hijira domin shugabantar yankin, sai ƴansiyasar cikin gida suka yi zargin an ware su.

"Waɗanda ke goyon bayansa" daga baya sun riƙa jin haushin salon mulkin Arafat na "wariya".

Jita-jitar cin hanci da rashawa a gwamnatin ya taka muhimmiyar rawa wajen rage kimar gwamnatin PA.

Wani abu mafi muhimmanci shi ne, sabuwar gwamnatin Falasdinu da aka kafa ta fara nuna alamun rashin iya dakatar da mamayar da Isra'ila ke yi a hankali a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Haka ma ta gaza cika alƙawarin samun 'yancin kai da Arafat ya yi, wajen kafa tarihin gaisawa hannu da hannu da tsohon firaministan Isra'ila Yizhak Rabin, a farfajiyar fadar White House a watan Satumban 1993.

Sannan ba a samu ingantaccen tsarin siyasa a shekarun bda suka biyo bayan yarjejeniyar, wanda aka mamaye kamar yadda aka gaza cimma nasarar shirin zaman lafiya.

Aka kuma ci gaba da faɗaɗa matsugunan yahudawa a Gaɓar Yamma da samun tashe-tsahen hankulan masu tsattsauran ra'ayi daga ɓangarorin biyu, da siyasar Isra'ila da kuma tashin hankalin da aka yi a shekara ta 2007 tsakanin Hamas da Fatah.

"A al'amuran yau da kullum, da sabbin alkaluma, da sabbin zamun sun fito," in ji masanin tarihin Falasdinu Yezid Sayigh.

"To sai dai hakan bai samu ba.... An tarwatsa Falasdinawa a yankunan da aka mamaye, Kuma hakan ya sa samun sabbin alƙaluma ya yi wahala''.

Netanyahu da ƙasar Falasɗinu

Tun ma kafin fara yaƙin Gaza, Netanyahu ke adawa da kafuwar ƙasar Falasɗinu ƙarara.

A watan Fabrairun 2024, ya ce 'Kowa ya sani na shafe fiye da gomman shekaru ina daƙile kafuwar ƙasar Falasdinu wanda zai iya jefa wanzuwarmu cikin hatsari.''

Duk da kire-kirayen ƙasashen duniya na bai wa hukumar Falasdinwa (PA) damar ci gaba da iko da Gaza, Netanhayu ya dage cewa PA ba za ta iya da Gaza ba, yana mai cewa Abbas bai yi Allah wadai da harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba ba.

A watan Agusta, Isra'ila ta bayar da aikin gina matsugunan Yahudawa da zai raba tsakanin Gabashin Binrin Ƙudus da Gabar Yamma. An amince da gina gidaje 3,400, yayain da ministan kuɗin Isra'ila, Bezalel Smotrich ya ce shirin zai kawo ƙarshen burin kafa ƙasar Falasɗinwa ''ssaboda babu wabin da za a amince da shi, don haka ba wanda zai amince''.

Wani abu yake tabbas shi ne matsawar aka amince da ƙasar Falasdinu, to Hamas ba za a jagoranceta ba.

Amincewar ta ɗaui hankali ne a ƙarshen taron kwana uku da aFaransa da Saudiyya suka ɗauki nauyi cikin watan Yuli, ida aka amince zewa ''Dole Hamas ta kawo ƙarshen mukinta a Gaza tare da ajiye miƙa wa Hukumar Falasɗinawa makamanta''.

Taron wanda aka yi a birnin New York ya samu amincewa ƙasashen Larabawa inda kuma ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 142 suka amince da su.

A nata ɓangare, Hamas ta ce a shirye take ta miƙa ikon Gaza ga hukuma mai zaman kanta da ta ƙunshi ƙwararru.

Nuna alamun amincewar kaɗai ya wadatar?

Yayin da Barghouti ke gidan yari, Abbas ya doshi shekaru 90, An wargaza Hamas, Yammacin Kogin Jordan ta koma tsibi-tsibi, a bayyane yake cewa Falasdinu ba ta da jagoranci da haɗin kai.

Amma hakan ba ya nufin amincewar ƙasashen duniya ba shi da ma'ana ba.

Wani jami'in gwamnatin Birtaniya ya faɗa wa BBC cewa amincewar da ƙasashen duniya ke yi da kafa ƙasar Falasɗinu bai wadatar ba.

"Abin tambayar shi ne ko za mu iya samun ci gaba ta yadda taron MDD zai zama wani abu daban maimakon bikin amincewa,'' in ji shi.

A wata Agusta, Amurka ta ɗauki matakin da ba a saba gani ba na ƙin bai wa gomman jami'am Falasɗinawa biza, lamarin da ya saɓa wa dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Amurka na da ra'ayin hawa kujera na-ƙi a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na ƙin amincewa da ƙasar Falasɗinawa kuma Trump ya nace da shirinsa na "Riviera" wanda Amurka za ta karɓi iko da Gaza a gaba-gaba.

Shirin bai ce komai kan ikon da Falasɗinawa za su samu ba, sai dai ya yi magana ne kawai kan abin da ya kira ''gwamnatin Falasdinawa da ka sabunta'' sannan bai yi tanadin sake haɗa Gaza da Gaɓar Yamma ba.

Dogon burin makomar Gaza na hannun tsakanin New York da amincewar da ƙasashen duniya ke ta yi da kafuwarta da shirin Trump da kuma shirin sake gina Gaza da ƙasashen Larabawa ke yi.

Duka shirye-shiryen da ke da bambantann hanyoyi, na fatan kawo ƙarshen wahalhalun da aka shafe fiye da shekara biyu ana sha a Gaza.

Kuma duk abin da ya faru, yana buƙatar amsar tambayar, yaya ƙasar Falasdinu da jagorancinta za su kasance.