Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Halin da mata ƴan jarida suka tsinci kansu a ciki ƙarƙashin Taliban
- Marubuci, Sana Safi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women
- Marubuci, Alex Lewis
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women
- Lokacin karatu: Minti 7
"Ranar 15 ga watan Agustan 2021, na tashi daga bacci ke nan na kunna wayata domin ganin labaran abubuwan da ke faruwa a duniya, kawai sai na ga wani ɗan Taliban a kan kujerar da nake gabatar da labarai."
Shabnam Dawran ta kasance tana aiki ne da gidan talabijin na gwamnatin Afghanistan, wato RTA - sa'ilin da dakarun ƙasashen yamma suka fice daga ƙasar.
Lokacin da Taliban, wadda ke da ra'ayin mazan jiya ta ƙwace mulki ta yi alƙawarin cewa za ta bar mata su ci gaba da karatu da kuma ayyukan gwamnati da kuma rayuwa kamar kowa.
Kwana uku bayan haka, Dawran ta yi ƙoƙarin tabbatar da gaskiyar alƙawarin na Taliban inda ta tafi aiki da nufin gabatar da labaran dare. Sai da ta isa gab da ɗakin gabatar da shirye-shirye ne wani ɗan ƙungiyar Taliban ɗauke da bindiga ya dakatar da ita.
Ta kwashe kimanin minti 30 tana gardama da shi domin ta samu damar shiga ta gabatar da labarai:
"Jikina na ta rawa domin wannan ne lokaci na farko da na taɓa yin gaba da gaba da ɗan Taliban ɗauke da bindiga. Kawai sai ya ce min 'Ki barn wurin nan. Ki bar wurin nan yanzun nan. Idan ba ki tafi ba zan harbe ki'."
Daga ƙarshe dai ta juya. Amma ya zuwa yanzu an tursasa wa dubban ƴan jarida barin ayyukansu.
Ƙungiyar kare hakkin ƴanjarida ta Reporters without Borders ta ce takwas cikin goma na ƴan jarida mata sun yi watsi da ayyukansu a kan tilas.
Waɗanda suka ƙi watsar da ayyukan nasu kuma na fama da cin zarafi takunkumai.
Sai dai har yanzu wasu daga cikinsu na ci gaba da fafutika a ciki da wajen ƙasar wajen ganin an ji muryarsu.
A ƙarƙashin shirin BBC na zaɓen mata 100 a duniya waɗanda suka yi fice, mun tattauna da wasu ƴan jarida mata waɗanda ke aiki a cikin Afghanistan kan yadda suke yin rayuwa a irin wannan yanayi.
Ga wasu daga cikin bayanin da suka yi mana.
Labarin Shabnam
Kasancewar ta girma ne a Kabul, Shabnam Dawran ta saba da ganin abubuwa masu hatsari - ta tsallake wasu hare-haren ƙunar bakin wake biyu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ƙawayenta.
Ta kuma saba da yin abubuwan da take ganin su ne mafita, inda take samun goyon bayan iyalanta waɗanda suka yarda da ita kan cewa tana da ƴancin samun ilimi.
Bayan ta fusata da matakin da Taliban suka ɗauka na hana ta gudanar da aiki, ta sha alwashin bayyana wa duniya 'ainahin' ƴan Taliban ɗin da ta yi arangama da su.
Ta hanyar taimakon ƴar uwarta, ta naɗi bidiyo kan abubuwan da suka faru da ita, inda ta bayyana Taliban a amatsayin maƙaryata, ta wallafa a shafinta na X.
A cikin sa'o'i biyu bidiyon nata ya yaɗu a shafukan intanet, inda mutane da dama a fadin duniya suka kalla tare da tofa albarkacin bakinsu, ciki har da Hillary Clinton. Gidajen jaridu na duniya suka yi ta ƙoƙarin ganin sun tattauna da ita.
To amma a wannan lokacin ne kuma ta faɗa cikin haɗarin shiga hannun hukuma yayin da ƴan Taliban suka fara bi gida-gida suna bincike.
Dawran, wadda ba ta taɓa tafiya zuwa ta ƙasar waje ba kafin lokacin, dole ta sa ta ta fice daga ƙasar kwanaki kaɗan bayan karɓar mulkin Taliban.
Labarin Ariana
Ya zuwa shekarar 2021, mata masu aikin jarida sun kai 1,400 a Afghanistan. Amma yanzu ana hasashen cewa yawansu ya ragu zuwa kimanin 600. Yawancin waɗanda suka daina aikin sun yi hakan ne saboda tsoro.
Yawancin waɗanda muka tattauna da su, ba su so a bayyana sunayensu na ainahi, ko asalinsu ko kuma inda suke zama saboda gudun a kai masu farmaki.
Ɗaya daga cikinsu mun kira ta da suna Ariana, wadda ta yi aiki a ɗaya daga cikin gidajen rediyon da ke bunƙasa a kudancin ƙasar, inda jagoran Taliban ke da zama.
Kafin 2021, Ariana na da ƴancin tafiya zuwa duk inda take so ita kaɗai, takan je ƙauyuka domin tattaunawa da mutane duk kuwa da cewa tana da ƴaƴa.. Ba abu ne mai sauƙi ba - ta jure hantara da nuna bambancin wajen albashi da kuma matsaloli na tsaro - amma ta yi aikinta duk da haka.
A lokacin da dakarun ƙasashen Yamma suka fice kuma Taliban ta ƙara ƙaimi domin karɓar mulki, bayanai sun nuna cewa yaƙin zai iya yaɗuwa har zuwa garin da take a kudanci. Surukanta sun buƙaci ta daina aiki.
Yanzu Ariana ba ta ciki fita daga gida ba - sau ɗaya kawai take fita a mako, shi ma domin ziyartar mahaifiyarta ko zuwa kasuwa.
Idan kuma za ta fita ɗin, tana ƙoƙarin kiyaye dokokin da Taliban ta gindaya.
A hukumance, dole mace ta fita da namiji muharraminta idan za ta yi tafiyar da ta kai kilomita 70. Sannan akwai wuraren da ba za su iya zuwa ba, ko muryarsu ma ba a so a ji.
Sannan uwa-uba, Ariana na fargabar halin da ƴarta mai shekara tara za ta shiga.
"Idan aka ci gaba da tafiya a haka, ba na tunanin za ta iya yin wani abu. Ba za ta wuce karatun firamare ba. Har yanzu ita ƙarama ce, amma ta fara fahimtar halin da ake ciki.
Labarin Sana
Ƴanjarida da suke aiki a Afghannistan, rayuwa a ƙarƙashin mulkin Taliban na tattare da fargaba.
Mata suna fargabar yin magana a kafafen sadarwa. Haka duk wani abu da aka yi ta waya, suna gaggawar gogewa saboda tsoron kar a ƙwace wayar, a gano wani abu da zai saka su a matsala.
Sana Ataf - ba asalin sunanta ba - tana rayuwa ne a yanki ɗaya da Ariana, kuma da sunan take amfani wajen rubuta rahotanni a jaridar Zan Times, wadda jarida ce ta mata da ke rubuta labarai a harsuna da dama na arewacin Amurka.
Sana tana rubuta yadda ake rayuwa cikin wahala a ƙasar wadda ke fama da takurarren tattalin arziki, da rashin ingantaccen kiwon lafiya, sannan an samu labaran kulle mata a gidan yari da kashe masu goyon bayan maɗigo da luwaɗi.
Ta yi amfani da jardar Zan Times wajen kawo rahoton makarantar da ake karatu a ɓoye a ƙarkashin ƙasa ta mata bayan Taliban ta hana karatun na mata.
Suna kuma kawo rahotannin zanga-zanga da kaɗa-kaɗe da raye-raye.
Saboda dokokin ne yanzu duk lokacin da za ta fita, sai ta fita tare da muharraminta. Dole a wasu lokutan take hana ɗanuwanta zuwa makaranta domin ya raka ta inda za ta je domin tattara labarai.
Amma babu wanda ya san ita ƴarjarida ce bayan ƴan gidansu.
"Ina da matsala babba tun a gida domin ƴanuwanmu da yawa da suke ƙauye ƴan Taliban ne. Ba za mu iya faɗa musu cewa ni ƴar jarida ba ce domin ina fargabar idan sun sani, zan shiga matsala."
Yadda za ta kasance nan gaba
Muna tattaunawa da wasu ƴanjarida da ke aiki a Afghanistan kan wani shiri na musamman da muka yi na 'Byline Afghanistan',
Kowanne daga cikin ƴanjarida sun bayyana abubuwa daban ne - a arewa maso gabas, wata ƴarjarida da muka zanta da ita ta bayyana mana cewa an raba ofisoshi, inda ba a yarda maza da mata su zauna a tare a ofis ɗaya ba. Idan ƴanjarida mata suna so yi tambayoyi, ko kuma za su je tattara bayanai, sai dai mazan su yi a madadinsu.
Wata ƴarjarida ta shaida mana cewa saboda fargaba, waɗanda suke so su yi magana da ƴanjarida suna taka-tsantsan domin gudun abin zai iya biyo baya idan sun karya dokokin Taliban.
Bayan ita da ƙanwarta da ƙaninta sun koma Burtaniya, kasancewar Shabnam Dawran ba ta iya Ingilishi sosai ba, sai ya kasance aikin farko ta fara shi ne a shagon sayar da kifi.
Yanzu ta koma aikinta na jarda, inda take jagorantar gabatar da labarai kan Afghanistan daga Burtaniya, a wata tasha mai suna Afghanistan International TV, wanda wani ɗankasuwa ɗan Saudiyya ya kafa.
Ta ce iyayenta da suke zaune a Afghanistan suna fuskantar barazana daga Taliban. Wasu mutane sun doki mahaifinta (wanda sojojin suka ce ba su da masaniya a kai) yanzu haka ko tafiya ba ya iya yi.
Kusan duk ƴanuwanta na kusa yanzu sun tsere daga ƙasar, amma ita, da su ɗin har yanzu suna samun saƙonni daga Taliban.
Amma a yanzu ta ce iyayenta da suke zaune a wani wuri da suke cikin aminci, a yanzu za su iya alfahari da ita a cikin ƴarjarida ƴar Afghanistan da barazanar Taliban bai hana aiki ba.
Za a iya samun ƙarin bayani a shirin BBC na musamman na 'Byline Afghanistan'.