Me ya haifar da rikici tsakanin PDP da APC a jihar Osun har da rasa rayuka?

Asalin hoton, BBC Yoruba
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta nemi gwamnatin ƙasar ta ƙakaba dokar ta-ɓaci a jihar Osun sakamakon rikicin siyasar da ya janyo mutuwar mutum shida.
Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ta Osun ta ce kiran a saka dokar ta-ɓaci wani abu ne da ke nuna gazawa daga ɓangaren jam'iyyar ta APC.
Jam'iyyun biyu dai na ta sa-in-sa tare da ɗora laifi ga junansu dangane da rikicin da ya haifar da rasa rayukan mutum shida.
Tuni dai sifeto janar na Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi umarni da a aike da ƙarin rundunar ƴansandan domin kwantar da tarzomar.
Tambayar da ƴan Najeriya ke yi ita ce, shin mene ne ya janyo rikicin?
Abin da ya janyo rikicin

Asalin hoton, BBC Yoruba
Rikicin dai ya taso ne sakamakon wani hukuncin kotun ƙoli ta yi ranar Litinin a Akure, wanda ya mayar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin jihar Osun na jam'iyyar APC da aka cire a 2022.
Jam'iyyar APC ta ce hukuncin kai tsaye ya mayar da shugabannin ƙananan hukumomin, to amma gwamnatin jihar wadda ta jam'iyyar PDP ce ta musanta cewa hukuncin ya dawo da mutanen da aka cire a 2022.
Bisa dogaro da wannan hukunci ne ya sa jam'iyyar ta APC mai hamayya a jihar ta ɗauki matakin yin amfani da ƙarfi wajen karɓe iko da hedikwatar ƙananan hukumomin da abin ya shafa, al'amarin da ya janyo rikici tsakaninsu da magoya bayan jam'iyyar PDP da suka yi tirjiya.
Hakan ne ya janyo mutuwar mutum biyar kamar yadda rahotanni suka ce, biyu a garin Iragbiji a ƙaramar hukumar Boripe, wasu mutum biyun a ƙaramar hukumar Olaoluwa sannan mutum ɗaya a ƙaramar hukumar Isokan.
Dukkannin jam'iyyun biyu na iƙrarin cewa an kashe musu mutane a rikicin bayan gomman da suka jikkata.
Sai dai gwamnan jihar ta Osun Ademola Adeleke ya ce ƴan jam'iyyarsa ta PDP, mutum biyar ne suka rasa ransu a rikicin.
Wane hali ake ciki yanzu a jihar Osun?

Asalin hoton, Ademola Adeleke/X
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya umarci al'ummar jihar walau ma'aikatan gwamnati ko kuma ƴansiyasa da su ƙaurace wa ofisoshin ƙananan hukumomin.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamna Adeleke ya ce ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin al'ummar jiharsa.
Ita kuma rundunar ƴansandan Najeriya ta sha alwashin hukunta duk waɗanda suke da hannu a rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, Muyiwa Adejobi ta ce sifeto janar na ƴansandan Najeriya ya bayar da umarnin ƙara yawan ƴansanda a jihar sannan kuma ya lashi takobin ganin an gurfanar da duk mai hannu a rikicin gaban kuliya.











