Me ya janyo karyewar farashin kayan abinci a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Bayan ƴan Najeriya sun shafe shekaru suna kokawa kan tashin farashin kayan abinci da na masarufi, a yanzu bayanai na nuna yadda kayan abinci ke ci gaba da faɗuwa a kasuwanni.
Yanzu haka buhunan kayan amfanin gona, kamar masara da waken soya na ci gaba da faɗi, wani abu da ake ganin zai iya sassauta tsadar rayuwa da al'ummar ƙasar ke ciki.
Wasu matakan tattalin arziƙi da gwamnatin ƙasar ta fito da su - kamar cire tallafin man fetur da sauye-sauye a ɓangaren kuɗi - sun sanya kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa al'umma cikin garari.
Sai dai masu hada-hadar kayan noma da BBC ta zanta da su sun nuna cewa yanzu (Watan Fabarairu) akan sayar da buhun masara kan farashin da ya kama daga 48,000 zuwa 50,000 a wasu kasuwanni da ke arewacin Najeriya.
Hakan na zuwa ne duk kuwa da cewa a farkon kaka an sayar da buhun masarar a farashin da ya kai kimanin naira 60,000.
Sai dai duk da cewa al'umma da dama na nuna farin ciki kan lamarin, wasu na nuna shakku kan tasirin hakan a nan gaba.
BBC ta tattauna da masana da kuma ɓangaren gwamnati kan dalilan da suka haifar da saukar farashin na hatsi:
Lokacin girbi
Wani malamin gone kuma masani kar kasuwancin hatsi a jihar Kaduna, Abubakar Isiyaku ya ce dalili na farko shi ne wadatuwar hatsi a kasuwa sanadiyyar fitowar kaya da gonaki.
"Yanzu lokaci ne na kakar kayan abinci, kasancewar an girbe amfanin gona, kuma a bisa al'ada a duk lokacin da aka fito da kaya daga gona za ka ga sun yi arha.
A irin wannan lokaci ne ma ƴan kasuwa ke sayen abinci suna ɓoyewa saboda arharsu, domin su sayara a gaba a lokacin da abincin ya yi tsada," in ji Abubakar.
Ya ƙara da cewa ko bayan daminar bara, an sayar da masara a farashi mai arha, wanda ya kama daga naira 23,000 zuwa 25,000.
Ya bayyana cewa lokacin da kayan abinci suka fi tsada shi ne lokacin da hatsi suka koma gona, kamar watannin Yuli da Agusta da kuma Satumba.
"A bara an sayar da buhun masara kan kuɗin da ya kai naira 45,000 zuwa 55,000 a watannin Yuli da Agusta lokacin da abinci ya yi tsada."
To sai dai Abubakar ya ce wani abin da ya ba su mamaki shi ne yadda farashin buhun masarar ya sauko daga yadda yake a farkon kaka (kimanin naira 60,000) zuwa farashin da ake samu a yanzu (naira 46,000 zuwa 50,000)
Shigo da baƙuwar masara
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saukowar farashin ya sanya manoma da masana harkar noma kamar Abubakar Isiyaku suka yi ittafakin cewa matakin da gwamnatin Najeriya na bai wa wasu ƴan kasuwa damar shigo da masara ƙasar shi ne babban dalilin faɗuwar farashin.
A cikin watan Yulin 2024 ne gwamnatin Najeriya ta sanar da cire haramcin karɓar haraji kan wasu kayan da ta bayar da umarnin shigo da su ƙasar.
Gwamnatin ta ce ta bayar da damar ne domin samar da sauƙi ga al'umma sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi.
Kayan abincin sun haɗa da shinkafa shanshera ko samfarera (wadda ba a gyara ba), da masara, da alkama, da kuma wake.
Wannan matakin ya bai wa wasu ƴan kasuwa damar shigo da masara daga waje, kuma ya sanya farashin ya sauka a kasuwanni.
Shugaban manoma masara a jihar Katsina, Lawal Garba Kurfi ya ce "mun fahinci kamar cewa gwamnatin tarayya ta ba wasu kamfanonin da wasu ƙungiyoyi masu ta'ammuli da masara da kamfanoni damar shigo da masara daga ƙasashen waje, masarar da ake shigowa da ita ta fi tamu sauƙi, shi ya sa kamfanonin suka raja'a a kanta, ba su sayen wadda muka noma."
Tallafin gwamnati
To sai dai bayanai daga ma'aikatar noma ta Najeriya sun bayyana cewa saukar farashin kayan abinci ya faru ne sanadiyyar tallafin da gwamnati ta bayar.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa "a gaskiya abubuwan da suka sanya farashin hatsi ya sauka suna da yawa, ba wai shigo da masara daga waje ne kawai ba".
Majiyar ta ce gwamnatin tarayyar ƙasar ta taimaka wa manoma a daminar da ta gabata da tallafi, wanda a cewarta hakan ne ya sanya hatsin suka yi sauƙi.
Daga cikin hujjojin da ta bayar shi ne tallafin kuɗi da aka bai wa manoman alkama, da raba taki sama da buhu miliyan ɗaya da kuma rage farashin iri da na kayan noma.
Fargaba
To sai dai Abubakar Isiyaku ya bayyana cewa manoman Najeriya na fargaba game da abin da zai faru matuƙar masarar da aka shigo da ita ta ci gaba da kankane kasuwar hatsi a Najeriya.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwar manoma za su tafka asara saboda ba za su iya mayar da kuɗin da suka kashe a daminar da ta gabata ba wajen noma.
"Idan zan ba ka misali, na kashe naira 45,000 a kan duk buhun masara da na noma a daminar da ta gabata, idan na ce zan sayar da ita a farashin da ake sayar da buhun masara a yanzu (naira 46,000 zuwa 50,000) ba zan mayar da kuɗina ba.
"Wannan ba ƙaramar barazana ce gare mu ba, domin ba za mu mayar da kuɗin da muka kashe ba."
Ya ƙara da cewa har yanzu manoma suna kuka da tsadar taki da sauran kayan noma, saboda haka nan idan aka tafi a haka, lamarin zai jefa manoman masara a Najeriya cikin mawuyacin hali.











