Albashin N70,000 ba zai canza wa ma'aikata komai ba - Gwamnan Gombe

Lokacin karatu: Minti 1

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce albashin naira 70,000 ba zai canza komai ba, la'akari da karyewar darajar kuɗin ƙasar.

Gwamnan ya shaida wa BBC cewa kamata ya yi kowace jiha ta kafa kwamiti domin duba yadda za ta aiwatar da sabon tsarin albashin mafi ƙanƙanta ba tare da cutar da wani ɓangare ba.

Ya ce: ''Na sha faɗin cewar naira 300,000 ma bai kai ta riƙe mutum da iyalinsa ba.''

''To yanzun ma kuma haka yake, don an kai shi naira 70,000 ba zai canza komai ba, domin darajar kuɗin ƙasarmu ta karye'', in ji Gwamnan.

Gwamnan na Gombe ya kuma ce durƙushewar harkar noma ne ya jefa Najeriya cikin yunwa, da tashin hankalin da ake ciki.

Ya alaƙanta matsalar tsaron da ake fuskanta a jihohin arewa maso gabas da arewa maso yammacin ƙasar, kan taɓarɓarewar harkar noma a ƙasar.