Yanwasan da United za ta sayar don yin garambawul, Gyokeres ya yanke shawara kan makomarsa

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na shirin siyar da Marcus Rashford, Jadon Sancho da Antony, Liam Delap na tattauna da United da Chelsea yayin da Jamie Vardy ke daf da komawa Valencia.

Manchester United ta ba da himma don ganin ta sayar da 'yan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, da Jadon Sancho, mai shekara 25, da kuma dan wasan Brazil Antony, mai shekara 25, a matsayin wani bangare na sake fasalin kungiyar. (Manchester Evening News)

Duk da rashin buga gasar cin kofin zakarun Turai, Manchester United za ta yi watsi da duk wani yunkuri na son daukar kyaftin dinta Bruno Fernandes, yayin da bayanai ke cewa Al-Hilal ta Saudiyya na son siyan dan wasan tsakiyar na Portugal, mai shekaru 30, kafin gasar cin kofin duniya (GiveMeSport)

Tsohon dan wasan Leicester City dan kasar Ingila Jamie Vardy, mai shekara 38, yana daf da komawa Valencia ta Spain. (Sun)

Newcastle United ta doke Barcelona da Real Madrid wajen siyan dan wasan gefe dan kasar Sipaniya Antonio Cordero mai shekaru 18 daga Malaga. (Thronicle)

Dan wasan gaban Ipswich Town dan kasar Ingila Liam Delap, mai shekara 22, ya tattauna da Chelsea da Manchester United kan yuwuwar komawa a bazara. (Fabrizio Romano)

Kawun Viktor Gyokeres ya ce dan wasan dan kasar Sweden, mai shekara 26, ya yanke shawarar watsi da komawa Manchester United ko Arsenal, yayin wata liyafar cin abinci ta yan uw ada abokin arziki (Sun)

Tottenham na fatan nasarar da suka samu a gasar cin kofin zakarun Turai za ta taimaka wajen shawo kan dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi mai shekaru 24 ya koma kungiyar a bazara. (GiveMeSport)

Shugaban Tottenham Daniel Levy ya godewa Ange Postecoglou a wani jawabi da ya yi bayan nasarar da kulob din ya samu a gasar cin kofin Europa kuma ya yi imanin cewa kofin na iya sanya Spurs a kan hanyar da za ta kai ga kololuwa. (Metro)

Tsohon dan wasan gefe na Liverpool Albert Riera, mai shekara 43, yana kan gaba a jerin masu son zama kocin Hull City na gaba. (Talksport)