Me ya kamata mace ta yi idan mijinta zai yi mata kishiya?

Hannun amarya da ango

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙarin aure, duk da cewa halas ne a addinin Musulunci, wanda mabiyansa suka fi yawa a ƙasar Hausa, amma abu ne da ke ƙunshe da ƙalubale daban-daban, daga ɓangaren maza da kuma mata.

A yawan lokuta lamarin kan haifar da zaman tankiya tsakanin ma'aurata, duk da cewa wani lokacin kuma akan yi abin salin-alin, wani lokaci ma har da tallafin uwargida.

Ƙarin aure na daga cikin abubuwa da ke taka rawa wajen mutuwar aure tsakanin ma'aurata a arewacin Najeriya, inda matsalar ta yi ƙamari.

Sau da yawa hakan na faruwa ne idan aka samu rashin jituwa, ko dai da mijin ko kuma da matar da za ta shiga gidan daga baya.

Amma tambayar ita ce: me ya kamata mace ta yi idan ta samu labarin mijinta zai yi aure?

'Na yi yaji lokacin da mijina zai ƙara aure'

Hajiya Fatima, wadda mijinta ya yi mata kishiya ta ce lokacin da ya faɗa mata zai ƙara aure, ta shiga yanayi na damuwa saboda tsananin kishi.

"Da ya fara faɗa min cewa zai ƙara aure, na ji kishi sosai, na nuna masa ba na son ya ƙara aure, har na ɗauke masa magana tsawon kwanaki ko da zai canza ra'ayi, amma a'a, har yaji na yi, duk da haka ban canza ra'ayinsa ba." in ji Fatima

"Ganin ya riga ya yanke hukunci, kuma ba zai canza ra'ayinsa ba, kawai sai na koma gidana amma kuma na buƙace shi da ya raba mana gida kuma hakan ya yi, yanzu haka har an yi shekara 7 da auren kuma yana shirin ƙaro ta uku." in ji ta.

'Yadda na ji labarin mijina zai min kishiya a wurin ƙawata'

Wata da BBC ta tattaunawa da ita ta ce a waje ta ji labarin ƙara auren mijinta.

"Kawai jin labarin zai ƙara aure na yi daga wajen wata ƙawata da ta ji labarin daga mijinta wanda ya ce a zaman majalisa shi ma ya ji labari.

Ta ƙara da cewa ta san tabbas tana da kishi amma tun da suka yi aure ba ta taɓa aikata wani abu da bai kamata ba saboda kishi saboda tasan tanadin addinita game da ƙarin aure.

"Wallahi da na jin labarin daga waje, ban ji dadi ba, ji na ji kamar ya wulaƙanta ni, bai martaba ni ba, saboda bai fito ya faɗa min ba, nasan ina da kishi, amma hakan ba zai saka na yi wani abu da bai dace ba, shi ma ya san hakan," kamar yadda ta yi bayani.

'Yadda na faɗa wa matata zan mata kishiya'

Gadon da aka raba wa matan da aka yi wa auren gata a jihar Kano, arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

BBC ta kuma tuntuɓi wani magidanci wanda ya nemi a ɓoye sunansa kuma ya bayyana yadda matarsa ta ɗauki labarin zai ƙara aure.

"Matata ta kasance ma'aikaciya ce, tana yawan fita aiki, kuma ni aiki na daga gida nake yi, saboda haka yawanci na fi ta zama a gida, shekararmu biyar da aure, kuma har yanzu Allah bai ba mu haihuwa ba."

"Da na faɗa mata na samu wata ina so na ƙara aure, ba ta ƙalubalanci hakan ba, ainihi ma ƙarfafa min gwiwa ta yi saboda ta kasance kodayaushe tana cikin ba ni haƙuri na rashin kasancewarta a kullum, kuma ta san ana matsa min da na ƙara aure."

"Tun da na faɗa mata, sai ta ce ba komai, Allah ba da sa'a kuma Allah sa tana da hali mai kyau."

Me ya kamata uwargida ta yi?

Dr Hajiya Zainab Abdullahi, ƙwararriya ce a harkar aure kuma mai bai wa ma'aurata shawara ta lissafa jerin shawarwari ko abubuwa da ya kamata mace ta yi a lokacin da mijinta zai ƙara aure:

  • Mace ta sa a ranta komai zai iya faruwa, mijinta zai iya tashi lokaci ɗaya ya ce zai ƙaro mata kishiya.
  • Mace ta kwantar da hankalinta: Kada ki bari fushi ko kishi ya rinjayi zuciyarki.
  • Tattaunawa da miji cikin hikima.
  • Neman shawarwari daga ƙwararru da malamai saboda kwanciyar hankalinki.
  • Addu'a da dogaro ga Allah.
  • Mace ta kula da kanta, da lafiyarta da tunaninta da kuma 'ya'yanta
  • Mace Musulma ta sani cewa addini ya bai wa namiji damar ƙara aure

Dr Zainab ta ce shirya kai da hakuri da addu'a da tattaunawa na daga cikin manyan hanyoyin da mata za su iya amfani da su domin kare kansu daga damuwa da ɓacin rai idan mijinsu na shirin ƙara aure.

Ƙarin aure ba sabon abu ba ne a al'adun Hausawa kuma Musulunci ya halatta shi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda mace za ta fuskanci wannan lamari da kuma hanyar da maza za su bi wajen shirin ƙara aure.