Me ya sa wasu matan Afirka ta Kudu ke son a yi musu kishiya?

Asalin hoton, Nhlanhla Phillips
- Marubuci, Khanyisile Ngcobo
- Aiko rahoto daga, BBC News, Zuurbekom
- Lokacin karatu: Minti 6
Amarya, Evelyn Sekgalakane, tana ƙyalƙyali cikin fararen tufafinta a lokacin da ta shiga cikin majami'a riƙe da hannun Shirley Molala, wadda za ta zamo kishiyarta ta uku a wani bikin aure-aure masu yawa cikin wani cocin Afirka ta Kudu da ke ƙarfafa gwiwar auren mace fiye da ɗaya.
A bayansu, ga ango nan Lesiba Molala wanda ya auro wata matarsa ta biyu yayin wani gagarumin biki a wani cocin Pentecostal da ke kudu maso yammacin birnin Johannesburg.
Bikin amaren da za su je gidan yawa na cikin ɗaurin aure 55 da aka yi ranar shagalin Easter - inda aka sha gagarumin ruguntsumi cike da farin ciki.
Bakwai daga cikin ɗaure-ɗauren auren, amare ne da za su je gidan kishiya - amma sauran duka a shirye suke, sun yarda a yo musu kishiya nan gaba.
"Allah ne [ya yarda] da auren mace fiye da ɗaya," wannan amon ne yake tashi daga faɗin makeken zauren da ya cika maƙil da 'yan biki. Auren mace fiye da ɗaya al'ada ce da ta yarda namiji ya zauna zaman aure da mace fiye da guda ɗaya kuma a lokaci ɗaya.
Shirley, wadda ita ce ta biyu a gidan Molala, ta auri mijinta ne tsawon shekara 25, kuma ta faɗa min kafin wannan babbar rana cewa: "Ina son zama da kishiya saboda hakan yana cikin koyarwar Baibul" - inda ta kafa hujja da sassan Tsohon Alƙawari na Littafin Mai Tsarki.

Asalin hoton, Nhlanhla Phillips
Uwargidan mijinsu ce da kanta, wadda daga bisani ta riga mu gidan gaskiya ta zaɓo ta a matsayin kishiyarsu.
Matar mai shekara 48 ta bayyana cewa yayin da aka fara yunƙurin ƙara auren bisa tafarkin addini, abu ne mai sauƙi a kalli amarya a matsayin ƴar'uwa kuma ƙawa.
"Mu [matan gidan mu uku] kanmu a haɗe yake muna ɗasawa da juna har ta kai mukan yi anko."
Kafin nan sai jami'an cocin sun duba tufafin ƴan biki a bakin ƙofa don tabbatar da duk mahalartan sun yi shigar mutunci - babu ɗamammun kaya, ba a barin mata da riga maras hannu ko waɗanda suka sa wando, kuma jazaman ne sai mace ta rufe gashin kanta.
"Na gane auren mace fiye ɗaya lokacin da na shiga cocin inda na gane cewa ba a yarda da ko zuwa zance wurin mace ba. Kuma saboda na fahimci cewa mace ɗaya ba za ta ishe ni ba, kuma na yi tunanin cewa to da na je na riƙa cin amanar aure, ba gwamma na ƙaro aure ba," in ji Lesiba Molala, ɗan shekara 67.
Ana yin irin wannan ɗaure-ɗauren aure masu yawa ne sau uku cikin shekara a babbar shalkwatar cocin da ke wani ƙaramin gari mai suna Zuurbekom - lokacin bikin Easter da kuma cikin Satumba, sai kuma a watan Disamba.

Asalin hoton, Nhlanhla Phillips
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wani ɓangare na bikin, na ci karo da matan Molala uku, amarya Evelyn na cike da murna, tana ta farin ciki game da adon da ta caɓa: "Ai! Na faɗa miki, ba za ki iya gane ni ba!"
Ba a dai saba ganin ɗaure-ɗauren aure da yawa lokaci daya ba a Afirka ta Kudu, haka ma ƙara aure. Ko da yake, ba a haramta tsarin auren mace fiye da ɗaya ba a ƙasar, amma ana yi wa irin wannan aure rijista ne a matsayin na-gargajiya, da ba a yin bikinsa a coci.
Cocin International Pentecostal Holiness (IPHC) dai na ɗaya daga cikin abin da aka sani da cocin Afirka mai zaman kanta, wadda aka bai wa damar gudanar da irin wannan auratayya, matuƙar dai hukumomi sun yi wa auren rijista.
Cocin IPHC dai, tana karantar da fa'idar auren mata da yawa kuma tana ƙarfafa gwiwar yinsa, sannan batun ya riƙa samun bunƙasa a tare da cocin tun lokacin kafuwarsa a Soweto cikin 1962 har zuwa sa'ar da ya kai yawan mabiya miliyan uku da dubu ɗari yanzu a faɗin kudancin Afirka.
Lesiba Molala ya yi auren farko ne a 1991, shekara shida bayan ya shiga cocin. Matar ita ma mamba ce a cocin, lamarin da ya zama wani muhimmin abu ga waɗanda ke neman matar aure a cocin.
Bayan shekara tara, Mista Molala da matarsa sun zauna inda suka tattauna kan niyyar ƙara yawan iyalinsa, kuma bayan ya nema, sai ma'auratan suka tsayar da magana a kan Shirley 'yar shekara 23.
Ita ma amarya Evelyn wato matar Lesiba Molala ta uku an fara ƙoƙarin ƙaro ta ne a watan Fabrairu bayan wani tsari da cocin ya shimfiɗa. Ta ce ba shakka ta ɗauki lokaci kafin ta amince da tunanin shiga gidan kishiyoyi, ko da yake sauƙin halin Shirley ya sa ta saki jiki.

Asalin hoton, Nhlanhla Phillips
Auren mace fiye da ɗaya, al'ada ce ta tun tale-tale a tsakanin wasu al'ummomin Afirka ta Kudu, amma batu ne da ke raba kan jama'a yanzu a ƙasar.
A shekarun baya-bayan nan shirye-shiryen talbijin masu nuna harkokin rayuwa sun ba da ƙarin haske kan zaman gidan kishiyoyi - lamarin da ya haifar da muhawara game da ko har yanzu irin wannan zaman iyali na da tasiri.
Farfesa Musa Xulu, wani ƙwararre kan fannin addinai a Hukumar Kare Haƙƙin Al'ummomi, Harsuna da Addinai da kuma Al'adun Afirka ta Kudu ya ce abu ne da ya zama ruwan dare a ci karo da iyalan da suka ɗaiɗaita a farkon shigowar annobar cuta mai karya garkuwar jiki, wadda ta galabaita Afirka ta Kudu.
Lamarin dai tuni ya lafa, ko da yake har yanzu "wata babbar matsala ce" kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Cocin IPHC dai na tabbatar da cewa masu niyyar aure ala dole sai an yi musu gwajin cuta mai karya garkuwar jiki.
Ya kuma yi tanadin cewa jazaman ne masu niyyar aure su faɗa wa juna sakamakon gwajinsu, sannan su yanke shawara a kan ko za su ci gaba da shirye-shiryen aurensu, kuma a bai wa cocin kwafin sakamako ta adana.
Irin wannan "tsage gaskiya" ya kuma rage yawan mutuwar auren da akasari ke faruwa idan wani ɓangare ya gano cewa an yaudare shi.
Da yawan ma'aurata ba su san juna ba kafin a yi musu baiko - kamar yadda lamarin yake da Freddy Letsoalo, ɗan shekara 35, da Rendani Maemu mai shekara 31.
Su ma an daura musu aure ne a garin Zuurbekom lokacin bikin Easter - dukkansu shi ne aurensu na fari.
Freddy Letsoalo ya ce ya fara ganin amaryarsa ne lokacin bikin wani abokinsa kusan shekara goma da ta wuce. Tun daga nan soyayya ta ƙullu a tsakani.

Asalin hoton, Nhlanhla Phillips
A lokacin da masu niyyar auren suka yi ƙawance a shafin sada zumunta na Facebook daga bisani, an taƙaita alaƙarsu zuwa murnar zagayowar ranar haihuwa - hakan ce ta yi ta faruwa har zuwa watan Disamban 2024 lokacin da Freddy Letsoalo ya fara sanar da iyalinsa daga nan kuma sai shugabancin cocin game da niyyarsa.
Burin Rendani Maemu ya cika kuma da ka gan ta tana cike da annuri kafin fitowar ta daga coci bayan ɗaurin aure tare da ƙawayen amarya su tara.
Yayin da ma'auratan a yanzu suka mayar da hankali ga sabuwar rayuwarsu a tare, duka a shirye suke su rungumi kishiya idan damar da ta dace ta kawo kanta nan gaba.
"Na sani idan akwai dama mijina zai so ya ƙara aure," cewar amaryar Freddy Letsoalo.
"Na yi imani da zama da kishiya."
Hangen da mai yiwuwa ya ci karo da tunanin wasu 'yan Afirka ta Kudu.










