Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe aka kafa Gaza kuma mece ce ma'anar sunan?
- Marubuci, أميمة الشاذلي
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بي بي سي نيوز عربي - القاهرة
- Lokacin karatu: Minti 7
Birnin Gaza na daga cikin birane mafi tsufa a tarihi. Ba yanki ba ne da aka samar a wannan ƙarni, amma ya kasance yana da alaƙa da da al'ummomin da suka shuɗe har zuwa yanzu.
Da wadannan kalamai, masanin tarihin Falasdinawa na Birnin Kudus Arif Al-Arif ya kwatanta Birnin Gaza cikin littafinsa da aka wallafa a 1943, inda a ciki ya samu takaitaccen bayani na abin da aka fada game da wannan birnin a adabin harsunan Larabci da Ingilishi da Faransanci da kuma harshen Turkanci.
A wani daɗaɗɗen littafin da ɗan Amurka Rabbi Martin Mayer ya buga a 1907 kan Gaza, wani Ba-Amurke kuma masani kan harsuna da al'adun mutanen Gabas ta Tsakiya da Asiya Richard Gotthiel ya bayyana birnin a cikin gabatarwar da ya yi cewa "birni ne mai ƙayatarwa don nazarin tarihi."
Gotthiel ya bayyana muhimmancinsa yana mai cewa "wurin haduwar ayarin motocin da ke jigilar kayayyaki daga kudancin yankin Larabawa da kuma gabas mai nisa zuwa Bahar Rum, sannan kuma cibiyar rarraba wadannan kayayyaki zuwa Syria da yankin yammacin Asia da Turai kuma hanya ce da ta hada yankin Falasɗinawa da kuma Masar."
Birane uku masu irin sunan
Wani abin burgewa shi ne, kundin bayanai na encyclopedia mai taken "Kamusun Kasashe" na marubuci kuma mai tafiye-tafiye Yaqut Al-Hamwi, ya ambato garuruwa uku da suke da wannan sunan a yankin, na farko shi ne yankin Larabawa wanda "Al-Akhtal" ya yi magana a kai a cikin wakensa na baka.
Na biyu shi ne wata kasa a Afirka wadda ita ce tsohon sunan Tunisia, kamar yadda Al-Hamwi ya ce an yi wani tattakin yini uku tsakanin Kairouan wanda ya fito daga wani ayarin motoci da suka nufi Aljeriya.
Game da fitaccen birnin Gaza da aka sani a tarihi, Al-Hamwi ya bayyana wurin da yake a matsayin "wani birni da ke gefen Masar, wanda daya ne daga cikin yankunan Falasdinu a yammacin Ashkelon."
Sunayen Gaza a tarihi
Tun zamanin kakanni, Larabawa na kiran shi da "Gaza" sannan a zamanin Musulunci, ana kiran shi da "Gaza Hashim" ana nuni da kakan Manzon Allah "Hashim bin Abdul Manaf" wanda ya rasu a can, kuma a cikin sa aka haifi "Imam Shafi'i", fitaccen malamin Musulunci, wanda ya yi rubutu a kai kamar haka:
"Ina kewar kasar Gaza* kuma ina fatan idan ya ci amanata bayan rabuwar, zan yi shiru.
Kamusun Girka ya bayyana cewa birnin yana da sunaye mabambanta har da "Loni" da "Minoa" da "Constandia".
Ma'anar Gaza
Eusebius na Caesar, wanda ake wa laƙabi da "uban tarihi" wanda ya yi rayuwa a karni na hudu, ya ce "Gaza" na nufin alfahari da kariya da kuma ƙarfi. Tawagar ta alakanta dalilin hakan ga yake-yaken da suka faru a ciki da kewayen birnin, lokacin da Gaza ta kare kanta, wanda shi ne ma'anar da masanin tarihin na Falasdinu ke nufi.
A wajen Saphronius, mamallakin Kamusun da aka sabunta, wanda aka fitar a 1910, "Gaza" kalma ce ta harshen Persia da ke nufin dukiyar sarauta, ma'anar da ta kusan zuwa daidai da masu cewa "Gaza" kalma ce ta Girka da ke nufin arziki.
Bayanai na cewa wani sarkin Persia ya binne arzikinsa a ciki kuma ya kaurace wa wajen, daga baya ya dawo wurin ya kuma ga arzikinsa kamar yadda ya ajiye. Ana cewa wannan bayanin ya faru a zamanin Romawa.
A Kamusun Larabci, an bayyana cewa "Gaz kaza da kaza" ma'ana ya kware a tsakanin mutanensa, wanda shi ne ma'anar da Al-Hamwi ya fada a kamusunsa yayin da yake magana a kan birnin Gaza sannan "Al-Arif" ya yi bayani cewa ma'anar na nufin wadanda suka gina Gaza sun kware a kai idan aka kwatanta da sauran wuraren da ke Bahar Rum.
Yaqut Al-Hamwi shi ma ya ambato "Gaza" a matsayin sunan matar "Tyre" wanda ya gina birnin Tyre da yanzu yake Lebanon.
Wane ne ya gina Gaza?
Masanin kayan tarihi Sir Flinders Petri ya ce tsohon garin Gaza an kafa shi shekaru 3,000 kafin haihuwar Annabi Isa, a tsaunin "Tel al-Ajal" sannan mazauna wajen sun fice daga nan saboda zazzabin cizon sauro da ya addabi wajen a lokacin.
Mazauna birnin sun sauka a wuri da ke da nisan mil uku inda suka kafa sabuwar Gaza a wajen da yanzu yake. Bayanai na cewa hakan ya faru ne a lokacin Hyksos, wanda ya mulki yankin shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isa.
Akwai wadanda suka karyata wannan labari inda suka ce har yanzu Gaza tana a toshon wajen da aka san ta kuma "Tel Al-Ajl" shi ne cibiyar kasuwanci ta Gaza. Wasu sun ce Alexander the Great ya ruguza tsohuwar Gaza sannan Gaza ta yanzu ba ta da nisa daga nan, in ji Sir Pteri.
Al-Arif a cikin littafinsa ya ce "Ma'ini", wadanda bayanai suka ce su ne dadaddun Larabawa da suka dauki tutar wayewa a karni na farko kafin haihuwar Annabi Isa, sune mafi tsufa a birnin "Gaza" kuma su suka samar da shi a matsayin cibiyar kai kayayyakinsu.
Muhimmancin Gaza ga Larabawa ya samo asali ne daga batun cewa ya hada Masar da Indiya, wanda shi ne hanyar kasuwanci mafi kyau a gare su idan aka kwatanta da bi ta Bahar Maliya, a don haka aka kirkiri Gaza kuma daga nan ya yi suna a tarihi.
Kasuwanci ya soma daga kudancin kasashen Larabawa a Yemen inda cinikayyar kasar da na Indiya suka hadu, sai kuma zuwa arewacin Makkah sannan zuwa "Madina a yanzu" da Petra, kafin daga bisani ya rabu gida biyu; daya a Gaza a Bahar Rum sai na biyun kuma a hanyar hamada zuwa Taima, Damascus da Palmyra.
Daga nan ne kuma masana tarihi suka yanke cewa masarautun Ma'in da Sheba sune masarautun Larabawa na farko da suka kafa birnin Gaza. :Awiyan" da "Anaqi" wadanda bayanai ke cewa sune Falasdinawa na asali kuma an ambato su cikin tsohon littafin Bible a matsayin wadanda suka fara yada zango a Gaza, a cewar Al-Arif.
Daga baya kuma aka samu "Dianites" wadanda tsatson Annabi Ibrahim ne, sai "Adoms" wadanda manoma ne da ke zaune a kudancin Jordan da kuma "Amorites" da "Canaanites" wadanda suka bambanta a asalinsu.
Zuri'ar Kan'an
Littafin "Tarihin Gaza" ya bayyana birnin a matsayin ɗaya daga cikin dadaddun birane a duniya, wanda yan zuri'ar Kan'an daga zuri'ar Ham ɗan Nuhu, a wata ruwayar kuma birnin ya wanzu lokacin da yan kabilar Kan'an suka mamaye shi suka kwace daga hannun Amuriyawa.
Wasu na ganin yan kabilar Kan'an sun fito ne daga Gabar Al-Ajm da a yanzu aka sani da yankin Gulf na Larabawa, sannan wasu sun ce sun fito ne daga Bahar Maliya yayin da masana tarihi suka kiyasta cewa sun zauna a yankin tsawon shekaru 5,000 da suka wuce.
Sir Petri na ganin an gina wani babban yanki na katangar birnin wanda aka gano burbushinsa a zamanin zuri'ar Kan'an kuma ba a gano duwatsu masu daraja ba da suka kai girman haka bayan zamanin Kan'an.
Buraguzan birnin Kan'an da suke a karkashin ikon Hyksos an kuma gano su a karshen kudancin Ajal. An kuma gano wurin binne gawarwaki da suka samo asali tun shekarun 4,000 kafin haihuwar Annabi Isa.
Al-Arif ya ce kabilar Kan'an su ne "suka fara sanin noman zaitun a wannan kasa, da masaka da kera tukwane da hakar ma'adanai, suka kirkiro haruffa da samar da dokoki, sai yayan Isra'ilawa suka kwafi abubuwa da dama daga wajensu.
A tsawon tarihi, Gaza ta fada karkashin ikon Misrawa da yan Babyloniya da yan Syria da Girka d yan Persia da Romawa.
Masanin tarihi Arif Al-Arif ya bayyana tarihin Gaza a matsayin "daukaka" saboda ya jure wa duk wani kalubale da ya fuskanta."