An tabbatar da wanzuwar mummunar yunwa a Birnin Gaza

    • Marubuci, Tom Bennett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Birnin Gaza da kewayensa ya faɗa cikin mummunar yunwa, kamar yadda wata hukumar da MDD ke goyon baya ta ayyana.

Hukumar ta IPC, wadda gwamnatoci da hukumomin duniya ke dogara da ita wajen gano matakan yunwa a fadin duniya a yanzu ta ɗaga halin yunwa da ake fama da shi a Gaza zuwa mataki na biyar - wanda shi ne mafi muni.

Hukumar ta ce sama da rabin al'ummar Gaza na cikin "matsanancin" yanayi wanda ya ƙunshi "mummunar yunwa da talauci da kuma mutuwa."

Isra'ila na ci gaba da taƙaita yawan agajin da ke shiga yankin Gaza. Sannan ta ce rahoton hukumar ya dogara ne da "ƙarairayin Hams", inda ƙasara a baya ta musanta cewa babu yunwa a yankin.

Wannan musu da Isra'ila ta yi tamkar ƙaryata abubuwan da sama da ƙungiyoyin agaji 100 da shaidu da kuma hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da dama suka ambato ne.

Rahoton na IPC ya bayyana ƙangin yunwar a matsayin "wanda ɗan'adam ya haddasa" sannan ya ce ana bukatar "mataki na gaggawa" in ba haka ba za a samu "ƙaruwar" mace-mace sanadiyyar yunwa.

Ta ce wannna ne hali mafi muni da aka shiga tun bayan da ƙungiyar ta fara sanya ido kan tsananin rashin abinci da abinci mai gina jiki a Gaza, kuma wannan ne farkon lokacin da aka ayyana ƙangin yunwa a Gabs ta Tsakiya.

Hukumar ta kuma yi hasashen cewa tsananin yunwar za ta faɗaɗa zuwa biranen Deir al-Balah da Khan Younis a tsakanin tsakiyan watan Agusta zuwa ƙarshen Satumba.

A tsakankanin wannan lokaci, ana sa ran kusan kashi ɗaya cikin uku - kimanin mutane 641,000 za su fuskanci mummunan yanayi a mataki na 5 na yunwa, yayin da yawan mutanen da ke cikin mataki na 4 zai ƙaru zuwa miliyan 1.14.

IPC ba ta da ikon ayyana ƙangin yunwa a hukumance - gwamnatocin ƙasashe da kuma Majalisar Dinkin Duniya ne ke yin hakan. To sai dai wannan sabon bayani - wanda ba kasafai ake ganin hakan ba - zai iya sanyawa Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana.

A matsayin martani kan rahoton, shugaban hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya ce yunwar abu ne da za a iya kauce mawa, inda ya ce an gaza shiga da abinci zuwa yankin Falasɗinawa ne "sanadiyyar hanawar da Isra'ila ke yi da gangan."

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce: "A lokacin da babu wani bayani da zai iya bayyana gaskiyar uƙubar da ake ciki a Gaza, yanzu kuma ga wannan batu: ƙangin yunwa".

Ya bayyana lamarain a matsayin "ba ɓoyayyen abu ba," sai dai abin da "uƙubar da mutum ya haddasa, kuma hakan na nuna gazawar bil'adama".

Ya ƙara da cewa akwai "nauyin da ke kan Isra'ila a ƙarƙashin dokokin duniya - ciki kuwa har da tabbatar da cewa abinci da kayan kiwon lafiya sun isa ga al'ummar Gaza".

Rahoton IPC na zuwa ne yayin da Isra'ila ke shigar ƙaddamar da gagarumin harin soji a yunƙurinta na ƙwace iko da Birnin Gaza.

Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza ne a matsayin martani kan harin da ƙungiyar Hams ta jagoranta kan yankin kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, lokacin da aka kashe kimanin mutum 1,200 tare da yin garkuwa da 251.

Tun daga wancan lokaci an kashe aƙalla mutum 62,122 a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hams ta sanar.

An tarwatsa kusan dukkanin al'ummar Gaza fiye da sau ɗaya, kuma an yi ƙiyasin cewa an lallata sama da kashi 90% na gine-ginen da ke Gaza. Haka nan kuma an lalata tsarin kiwon lafiya da ruwa da kuma tsaftar muhalli na yankin.