Kane ya zura ƙwallo a kowacce ƙungiyar Bundesliga su 18

Lokacin karatu: Minti 1

Harry Kane ya kafa tarihin cin ƙwallaye da yawa a Bundesliga cikin sauri, bayan da Bayern Munich ta je ta caskara Holstein Kiel 6-1 ranar Asabar.

Tsohon ɗan wasan Tottenham ya zura uku rigis a wasan, ya haura Erling Haaland mai tarihin da tazarar karawa takwas, kafin ya zura 50 a raga a Bundesliga.

Ƙwallo ukun da ya zura a ragar Holstein Kiel ranar Asabar, kenan ya ci 50 a wasa 35 jimilla, sai a karawa ta 43 Haaland ya zura 50 a raga a Bundesliga.

Kane ya koma buga Bundesliga kan fara kakar bara daga Tottenham a matakin mai cin ƙwallaye kan £86.4.

Ya ci ƙwallo 36 a karawa 32 a bara, wanda ya lashe ƙyautar takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a zura ƙwallaye a raga a gabaki ɗayan gasar lik ta Turai.

Haka kuma ƙyaftin ɗin tawagar Ingila ya bayar da takwas aka zura a raga a bara, amma Bayern Munich ta kasa lashe Bundesliga na 12 a jere, wanda Bayer Leverkusen ta ɗauka ba tare da rashin nasara ba a gabaki ɗayan kakar bara.

Har yanzu Kane na fatan lashe babban kofi a tarihin tamaularsa, wanda shi ne kan gaba a ci wa Ingila da Tottenham ƙwallaye da dama a tarihi.

Shi ne yake rike da tarihin Bundesliga, wanda ya zura ƙwallaye da yawa a gasar a kakarsa ta farko, ya kuma kafa wani tarihin a wasa uku da fara kakar bana.