Fadhila Lamiɗo ce gwarzuwar gasar Hikayata ta 2025

Lokacin karatu: Minti 2

Fadhila Lamiɗo ƴar asalin jihar Kaduna ce ta zama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2025.

An bayyana gwarzuwar ne a taron na bana wanda aka yi a ranar Alhamins 11 ga watan Disamba a birnin tarayya Abuja.

Fadhila marubuciya ce daga jihar Kaduna, kuma matar aure ce mai ƴaƴa uku, sannan ta lashe gasar ne da labarinta mai suna "Tsalle Ɗaya,"

Jamila Lawal Zango ce ta zo ta biyu da labarinta na "Gobena." sai marubuciya Hafsat Sani Tanko wadda ta zo ta uku a gasar ta bana da labarinta na "Samarin Shawo."

A wajen taron na bana, tsohon shugaban sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, wanda shi ne ya jagoranci assasa gasar shekara 10 da suka gabata, ya ce an ƙirƙiri gasar ne domin karfafa gwiwar marubuta mata tare da fito da fasaharsu.

Ya ce yana alfahari tare da farin cikin ganin wannan shekarar da gasar ta cika shekara 10.

Yadda aka tantance labaran Hikayata ta bana

Game da yadda yadda aka tantance tare da fitar da gwarazan da labaransu suka fi inganci, shugabar kwamitin alƙalan gasar, Farfesa Asabe Kabir ta ce sun yi aiki cikin tsanaki ne wajen fitar da su.

A cewarta, bayan marubuta da dama da suka shiga gasar, "sai aka zaɓa wasu guda 30. Sai alƙalai mu uku muka zauna muka tantance, muka zaɓi guda uku."

Ta ce sun tantance labaran ne ba tare da sani kowace marubuciya ba, "sannan mu kanmu alƙalan ba mu taɓa haɗuwa ba."

Ta ce a ƙarshe sun yi taron ƙarshe ne ta intanet, domin tantance tare da cire na farko da na biyu da na uku.

Muhimmanci karatun mata

A wajen taron, an tafka muhawara kan muhimmancin ilimin mata, inda Farfesa Abdullah Uba Adamu da Rahama Abdulmajid da Dr Ibrahim Sheme da Fatima Zahra Umar suka tattauna kan maudu'in.

Da take jawabi, Rahma ta ce daga cikin abubuwan da suka janyo taɓarɓarewar ilimin mata a arewa, akwai rashin mayar da hanakli, inda a cewartsa, maza suna tunanin rashin ilimin mace ya fi muhimmanci kan ta samu ilimin.

A nasa jawabin, Sheme cewa ya yi, "ina so in kalla abin ta fuskar al'ada ne. Asali Bahaushe har mazan ma bai yarda su yi karatu ba ballantana mace, da ƙyar aka fara amincewa."

Ya ce bayan wannan ma akwai matsalar tsaro da talauci da suke taka rawa wajen daƙile neman ilimi a yankin.

Fatima Zahra Umar cewa ta yi kusan kashi 60 na duniya mata ne, inda ta ce an killace su sannan ba sa samun wakilci wajen ɗaukar matakan da suka dace.

Shi kuma Abdallah Uba cewa ya yi yana a jami'ar BUK da yake koyarwa, kusan kashi 90 na ɗaliban da yake koyarwa mata ne, sannan ya ƙara da cewa al'adar Bahaushe yana son mata masu cikakkiyar biyayya ne, wanda hakan ya sa suke ɗar-ɗar da karatun mata.