Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa kallo ya koma kan Kwankwaso?
A makon nan sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne yake ta faman amo a muhawara da tattaunawa a kafafen sada zumunta da ma a zahiri.
Mahawarar dai ba za ta rasa nasaba da wasu muhimman abubuwa da suka faru ba da suka haɗa da saukar takwaransa tsohon gwamnan jihar ta Kano, Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC na kasa da haɗakar ADC da kuma rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Wasu na ganin lokaci ya yi da Kwankwaso zai shiga jam'iyyar APC tun da abokin hamayyarsa a siyasance wato Abdullahi Ganduje ya bar shugabancin jam'iyyar, a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin zawarcin tsohon ministan tsaron da Shugaba Tinubu ke yi.
Tun bayan kafa jam'iyyar haɗaka ta ADC, da irin jiga-jigan ƴan siyasar ƙasar da suka rinƙa tururuwa zuwa cikin jam'iyyar, ya sa ƴan siyasa kama sunan Kwankwaso dangane da inda zai karkata.
Sannan kuma akwai masu ganin rasuwar Buhari za ta bai wa Kwankwaso damar cike giɓin da marigayi tsohon shugaban ƙasar ya bari a siyasar arewacin Najeriya.
Wane muhimmanci Kwankwaso yake da shi a siyasa?
Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna jan zarensu kuma suka shiga cikin zuciyar matasa.
Masana na cewa tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗansiyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa da ya sa wa suna wanda kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai tsohon gwamnan na Kano wanda ya samar da aƙidar siyasa mai suna Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.
Sannan kuma Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne gwamnan da bayan ya faɗi a ƙoƙarin neman wa'adi na biyu ya sake komawa kujerar bayan shekaru huɗu, inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado na lokacin.
Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin-gado, Nasiru Yusuf Gawuna.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a 2023, inda ya samu kuri'u fiye da 900,000 a jihar Kano, wadda ta fi yawan ƙuri'ar da kowanne daga sauran ƴan takarar jam'iyyun suka samu a jiha ɗaya tilo, ciki kuwa har da jam'iyya mai mulki ta APC.
Me ya sa jam'iyyu ke zawarcin Kwankwaso?
Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, CAS, ya ce ƙuri'ar da Kwankwaso ya samu shi kaɗai a jihar Kano a takarar da ya yi ta shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a 2023 ta ƙara masa martaba.
"Duba da ƙuri'un da ake ganin an kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata da kuma yawan ƙuri'un da Kwankwaso ya samu da kuma irin tazarar da ke tsakaninsa da ita jam'iyyar APC ɗin da ma yadda jam'iyyarsa ta NNPP ta yi nasara a matakin jiha, hakan ka iya sa jam'iyyar APC tunanin kwashe waɗannan ƙuri'un maimakon kashi 25 kawai.
Haka su ma sauran jam'iyyun musamman na haɗaka da suke kira ga Kwankwaso da ƴan hamayya irinsa da su shiga a yi tafiyar da su, babban abin da suke kwaɗayi shi ne waɗannan dandazon ƙuri'un na Kano" In ji Malam Kabiru Sufi.
Ko Kwankwaso zai koma APC?
Rahotanni da bayanai da ke karo da juna na nuna Kwankwaso na tattaunawa da Shugaba Tinubu a asirce duk da cewa ɓangaren Kwankwason ya sha musanta hakan.
Ko kalaman da Sanata Rabi'u Kwankwason ya yi da yammacin ranar Alhamis ɗin nan sun nuna kamar babu zancen zawarcin nasa zuwa jam'iyyar APC, duk da dai masu fashin baƙi na yi wa kalaman kallon na siyasa.
"Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan.
Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi." In ji Rabi'u Musa Kwankwaso.
Bugu da ƙari, a ranar Alhamis ɗin dai tsohon gwamnan ya kuma karɓar wasu gomman ƴan siyasa da aka ce ƴan jam'iyyar APC ne da suka sauya sheƙa zuwa NNPP, wani abu da ke nuna madugun Kwankwasiyyar na shirin zama daram a jam'iyyarsa ta NNPP.
A baya ma an ji Kwankwason yana cewa babu yadda za a yi ya koma APC, abin da ya bayyana da tamkar aikata "saɓo" irin na siyasa.
A kwanakin baya ma, Alhaji Buba Galadima wanda jigo ne a tafiyar Kwankwasiyya ya shaida wa BBC cewa ba za su je ko'ina ba walau APC ko kuma jam'iyyar haɗaka ta ADC, inda ya ce sai dai a zo a same su a jam'iyyarsu ta NNPP.
"Wannan duk ba wani abu ba ne illa siyasa kuma shi jagora yana yi ne domin ƙara wa kansa daraja.
Idan ya samu tayi mai kyau wanda ya dace da aƙidarsa ta taimakon talakawa to me zai hana ya koma APC? Ai dama domin jama'a ake yi. Mu ƙafar jagora ƙafarmu." In ji wani ɗan Kwankwasiyya da ba ya son a ambaci sunansa.
Zaɓi uku da suka rage wa Kwankwaso
Malam Kabiru Sufi ya ce a yanzu haka yadda al'amura ke tafiya zaɓi uku ne suka rage wa Kwankwaso.
"Ko ya zauna a jam'iyyar ta NNPP ya ci gaba da taka rawa irin wadda ya taka - ma'ana yin takarar shugaban ƙasa kuma ya sa ƴan takarar a muƙamai a jihar Kano da sauran jihohi da dama.
Ko kuma ya koma ita jam'iyyar APC ɗin wadda kamar ake ganin tana zawarcinsa bisa la'akari da ɗimbin ƙuri'un da za su iya samu a Kano.
Ko kuma ya koma jam'iyyar haɗaka ta ADC domin haɗa kai da ƴan hamayya wajen ganin sun yi wa jam'iyya mai mulki ta APC illa."
Abu uku da za su iya faruwa idan Kwankwaso ya koma APC
Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, CAS, Kano, ya ce komawar Kwankwaso jam'iyyar APC da ya bayyana shigarta da "saɓo" irin na siyasa ka haifar da abubuwa guda uku.
- Idan har ya kasance Kwankwaso ya koma APC, to magoya bayansa za su bi shi duk inda ya shiga tun da wannan ne iƙirarin da suke yi.
- Sai dai kuma akwai mutanen da ba mabiyansa ba ne amma kuma suna ƙaunar salon siyasarsa za su ji babu ɗadi saboda yadda suka san shi da jajircewa da ƙin bin Yerima a sha kiɗa kuma tagomashinsa zai ragu.
- Sannan kuma wataƙila komawar tasa a samu abin da ake kira kwarkwasa fid da mai giji inda komawarsa ka iya tilasta wasu ƴan jam'iyyar su fice su bar jam'iyyar.