Muhimman abubuwan da suka faru a yaƙin Sudan

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Sojojin gwamnatin Sudan sun sake karɓe iko da wurare masu muhimmanci a babban birnin ƙasar, Khartoum daga hannun mayaƙan RSF, ƙungiyar da ta kasance wani ɓari na dakarun ƙasar da ke son kawar da gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.

A ranar Juma'ar da ta gabata, an ga sojoji na murna suna daukar hoto a bakin fadar gwamnatin ƙasar.

Faɗa ya ɓarke a Sudan ne a cikin watan Afrilun 2023, lokacin da mayaƙan RSF suka ƙaddamar da hari a kan sansanonin jami'an sojin Sudan (SAF), inda suka ƙace iko da yankuna da dama masu muhimmanci a babban birnin ƙasar, ciki har da filin jirgin sama na birnin.

Dubban mutane ne suka mutu a sanadiyyar rikicin, sannan an tursasa wa miliyoyi barin gidajensu, inda suke fuskantar matsananciyar yunwa, wani abu da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin matsalar jin ƙai mafi muni a duniya.

Latsa kibiya zuwa ƙasa ko sama domin karantawa.