Hasashen masana kan makomar APC bayan babban taronta

RULING PARTY IN NIGERIA

Asalin hoton, APC

Lokacin karatu: Minti 2

Masana siyasa a Najeriya sun fara tsokaci a kan matakin da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ɗauka na goyon bayan zarcewar shugabanta na riƙo, Abdulllahi Umar Ganduje a matsayin shugaba mai cikakken iko.

Taron ƙoli na jam'iyyar da aka yi a ranar Laraba ne ya sanar da matsayar jagororin jam'iyyar a game da kujerar shugabancin, wadda aka yi ta hasashen za ta koma wani yankin ƙasar ba wanda Ganduje ya fito ba.

Shugabannin jam'iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci babban taron ƙolinta da ya gudana jiya Laraba a birnin Abuja ne suka kaɗa ƙuri'ar goyon baya ga mulkin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sanarwar jam'iyyar APC ta ce taron ya ɗauke matakin ne ta la'akari da irin nasarorin da jam'iyyar ta samu a zaɓukan da aka yi a ƙarƙashin shugabancin Ganduje, da yadda ake ci gaba da samun mutanen da ke ficewa daga wasu jam'iyyun ƙasar suna komawa APCn.

To ko ya ya masana siyasa ke kallon wannan mataki?

Farfesa Abubakar Kari, masanin siyasa ne, kuma malami a jami'ar Abuja ya ce daman a wannan jamhuriyar shugaban asa ne ke da iko kan shugabancin jam'iyya, saboda haka duk wanda yake so ya ci gaba da to shine zai yi mulkin jam'iyya.

"Ga bisa dukkan alamu Tinubu yana jin daɗin mulkin Ganduje, ya kuma faɗi ƙarara, kamar yadda shima Gandujen ya nuna cewa babu wani gwani sai Tinubu, in ji Farfesa Kyari.

Kafin yanzu dai, akwai wasu ƴaƴan jam'iyyar APC musamman daga yankin Arewa ta Tsakiya masu faɗi tashin ganin shugabancin jam'iyyar ya koma yankin su, saboda a cewar su, hakan ne adalci ta la'akari da yyarjejeniyar da jam'iyyar ta ƙulla a baya.

To ko yankin Arewa ta tsakiyan ya haƙura ta waccan fafutuka kenan?

Sanata Salihu Mustapha mai wakiltar Kwara ta tsakiya yana cikin jiga-jigan jam'iyyar daga yankin ya ce ana duba cancanta ne ba wai yanki ba a siyasance, "Za ku dubi wanene zai fi dacewa da jam'iyyarku a wannan lokacin, idan lokacin siyasa ya zo in ya kamata a kai wani ɓangaren domin a samu goyon bayan ƴan ƙasa to dole ne zamu yi hakan."

Farfesa Abubakar Kari na ganin cewa a halin yanzu, kusan ana iya cewa bakin alƙalami ya bushe, " Masu tinanin shugabanci zai koma wancan bangaren to babu alamun haƙarsu za ta cimma ruwa."

"Wasu ƴaƴan jam'iyyar sun fara fanɗarewa, kamar irin su Nasiru El'rufa'i da Amaechi, da wasu ɗaiɗai ku irinsu wasu kuma suna ta gunaguni, mai yiwuwa guiwarsu za ta yi sanyi, amman indai fadar shugaban ƙasa ta ci gaba da marawa Ganduje baya to kamar yadda hausa ke cewa wanda bai san liman mai yiwuwa sai dai ya nemi wani masallaci"

Masana dai na ganin cewa za a ci gaba da taso da wannan batu daga lokaci zuwa lokaci, kuma nasarar kowanne ɓangare ta dogara ne da irin ƙoƙarinsa wajen kamun ƙafa daga manyan masu faɗa a ji a tafiyar da harkokin mulki a matakin tarayya.