Dole a bar Falasɗinawa su zauna a Gaza - Blinken

Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin kasashen wajen Amurka, Antony Blinken ya ce ba zai yiwu ba a tursasa wa Falasɗinawa barin Gaza ba kuma dole ne a bar su su koma gidajensu idan yanayi ya bari.
Mista Blinken ya soki waɗansu sanarwa da ministocin Isra'ila suka fitar, inda suka nemi da a tsugunar da Falasɗinawa a wani wurin daban.
Antony Blinken dai ya je kasar Qatar a ziyararsa ta baya-bayan nan zuwa yankin Gabas ta tsakiya.
Kiran nasa dai ya biyo bayan wasu rahotanni da ke cewa an kashe kusan mutum 70 a sansanin 'yan gudun hijra na Jabalia da ke arewacin Gaza.
Wasu hotuna daga Jabalia sun nuna wasu gawarwakin mata da ƙakanan yara da ke kwance a ƙarƙashin ɓuraguzan gine-gine da aka ruguza
Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya shaida wa BBC cewa " ta hari wasu sojoji a lokacin harin" sannan kuma ba ta da "masaniyar yawan mutanen da aka kashe kamar yadda aka ce".
"A ƙoƙoarin mayarwa da Hamas martani kan hare-harenta na rashin tausayi, rundunar IDF na samame domin lalata ƙarfin Hamas na soji da iko," in ji rundunar, inda ta ƙara da cewa rundunar ta IDF "na bin dokokin ƙasa daƙasa sannan tana kiyayewa domin ganin an rage yawan mutuwar fararen hula."
Falasɗinawa fiye da 60 ne dai rahotanni suka nuna sun mutu a ranar Lahadi, a birnin Khan Younis da ke kudanci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An dai kai hare-hare masu dama a kan sansanin 'yan gudun hijra na Jabalia tun fara yaƙin da Isra'ila ta yi a Gaza sakamakon harin da Hamas ta kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
A lokacin harin, Hamas ta kashe mutane 1,200 mafi yawancinsu fararen hula sannan mayakan sun yi gargkuwa da kimanin mutum 240.
Ma'aikatar lafiya a Gaza kuma ta ce an kashe Falasɗinawa fiye da 22,000 mafi yawansu mata da ƙananan yara.
Ministan Kuɗin kasar Isra'ila mai ra'ayin riƙau, Bezalel Smotritch ya yi kira ga Falasɗinawa da su bar Gaza ga 'yan Isra'ila da ke son mayar da yankin "gona".
Wani shi ma mai tsattsauran ra'ayin ministan tsaron ƙasar ta Isra'ila, Itamar Ben-Gvir, ya aike da wasu saƙonni a wannan makon inda yake "ƙurara wa Falasɗinawa gwiwa da su bar Gaza" domin "sulhu" ga rikicin da ake yi.
Ra'ayin gwamnatin Isra'ila dai shi ne cewa daga ƙarshe al'ummar Gaza za su koma gidajensu , duk da cewa har yanzu ba ta fitar da jadawalin yadda hakan zai kasance ba sannan kuma yaushe za a yi hakan.
Yanayi dai a Gaza na ci gaba da taɓarɓarewa. Ma'aikatar Lafiya ta yankin ta ce al'amarin ya kai ga asibitoci ma ba su tsira ba.
Wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa guda uku da ke samar da kulawar lafiya sun sanar da cewa za su bar asibitin Al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza sakamakon umarnin da Isra'ila ta bayar da a bar asibitin.
Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ayyukan jinƙai, Gemma Connell ya shaida wa BBC cewa "sun damu da yanayin da ake ciki" a Gaza.
Ya ce "abin da hakan yake nufi shi ne asibitin da yake a cike maƙil fiye da yawan jama'ar da ya kamata ya ɗuka, yanzu haka ba ya samun ƙarin tallafi saboda yawan samunƙarin matattu."
Shi ma shugaban hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce an tursasawa fiye da marasa lafiya 600 da ma'aikatan lafiya da dama barin asibitoci kamar yadda darektan asibitin ya shaida.
"Kuma ba a san wurin da suke ba ya zuwa yanzu," in ji mista Tedros a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, wato Twitter.
Ziyarar dai ta mista Blinken na zuwa ne a daidai lokacin da yanayi ke ci gaba da ta'azzara a yankin Gabas ta Tskiya, inda ake fargabar cewa rikicin ka iya fadaɗa.

Asalin hoton, reuters
An kashe babban jami'i na Hamas, Saleh al-Arouri a wani harin da ake zargin na Isra'ila da ta kai a kudancin birnin beirut ranar Talata, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban na Hamas da ƙarin mutum biyar.
Hassan Nasrallah, shugaban mayaƙan Hezbollah mai goyon bayan ƙasar Iran, ya kwatanta kisan Arouri da "zaluncin Isra'ila a bayyane" da kuma ya ce ba za su ƙyale ba.
Hakan ne ya sa Hezbollah ta harba rokoki zuwa Isra'ila ranar Asabar a wani "matakin farko na martani" dangane da " kisan Arouri.
Mista Blinken ya sauka ƙasar Qatar bayan ya je ƙasashen Jordan da Turkiye da Girka. Ya kuma je Abu Dhabi da yammacin Lahadi sannan kuma zai je ƙasar Saudiyya ranar Litinin.











