Ƙasar da masu zaɓe suka yanke ƙaunar samun ci gaba

Manomiya a Bangladesh
Bayanan hoto, Miliyoyin mutane a Bangladesh na fama da talauci da hauhawar farashin kayayyaki

Taka 500 kacal na kudin Bangladesh Noor Bashar yake samu a kowacce rana, kwatankwacin dalar Amurka 4.50, wannan rabin abin da yake buƙata kenan na ciyar da iyalinsa mai mutum tara.

Samunsa ka iya raguwa idan aka ci gaba da samun hauhawar farashin kayan masarufi a Bangladesh.

"Mutane na matuƙar shan wuya," in ji wani lebura, wanda ke zaune a Cox's Bazaar, nisan kilomita 400 daga kudancin babban birnin ƙasar Dhaka.

"Idan na ce zan sayi kifi, to ba zan samu kuɗin kayan kamshin girki ba. Idan na sayi kayan dandanon girki, ba zan iya sayan shinkafa ba."

Bangladesh, dai na da yawan al'umma miliyan 170, kuma tana fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Kasar da a baya ta ke da tagomashin tattalin arziki a yanzu ta koma faɗi tashi, alkawuran bunƙasar tattalin arziki da ingantuwar rayuwa sun bi shanun sarki, yayin da take cikin hatsari sakamakon matsalar sauyin yanayi.

Sai dai masu kaɗa ƙuri'a a ranar Lahadi ba su da wani ƙwarin gwiwa ko fata kan zaɓen, ko zai inganta rayuwarsu.

"Babban abin da ke gabana, shi ne ciyar da iyalina. Babu abin da ya shafe ni da siyasa, saboda ba shi zai ciyar min da iyali ba. Ni fa kullum tunani na shi ne yadda zan biya basukan da na ci a wurin jama'a," in ji Mista Bashar.

Lebura a Bangladesh
Bayanan hoto, Noor Bashar, leburan da ke fadi tashin ciyar da iyalinsa mai mutum 9
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da alama jam'iyyar Awami League ta Sheikh Hasina, za ta kara faɗaɗa madafun ikonta a wannan zaɓen, wanda babbar jam'iyyar adawa ta Bangladesh Nationalist Party (BNP) ta yi kira ga magoya bayanta su ƙauracewa.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Ms Hasina, ta kama dubun-dubatar 'yan adawa da magoya bayansu, wani mataki da masu fafutuka suka yi allawadai da shi.

Ga masu zaɓe da dama, sun sadakar jam'iyya mai mulki ta ma ci zaɓen, saboda babu wata gagarumar adawa ko kwakkwaran abokin takara. Da dama na fargabar za a shiga yanayin matsi idan Hasina ta zarce a karo na hudu fiye da lokutan baya.

"Ban damu da wannan zaɓen ba. Dan me zan damu? sakamakon zaɓen mai kyau ko maras kyau ba zai sauya min rayuwa ba," inji wani maigadi Gias Uddin, da ke aiki a gabar tekun Chittagong.

Magidancin mai shekara 57, ya ce ɗan abin da yake samu baya isar sa ciyar da iyalai da ɗaukar nauyinsu. Sau biyu kaɗai ake ɗora girki a gidansa a kowacce rana.

Ya jima da daina sayen kifi ko nama saboda sun yi tsada, yawancin lokuta ya kan tattara sauran naman da mutane suka ci ko kifi domin ya kai wa 'ya'yansu su maida mugun yawu.

Mai zabe a Bangladeshi
Bayanan hoto, Gias Uddin a Chittagong, ya ce bai damu da zaɓen ba tun da ba zai sauya masa rayuwa ba

Iyalai da dama na rayuwa ne ƙarƙashin alfarmar bashin 'yan uwa da abokan arziki da abin sadaka.

"Na ci bashin taka 200,000. Ban ma san yaushe zan biya bashin ba. Allah ne kadai ya san lokaci," inji Mista Uddin.

"Yanayi ne mai tsauri, da tashin hankali, wasu lokutan na kan ji ina ma dai na mutu."

Mulkin mulaka'u

Wasu ƙwararru na ganin salon mulkin mulaka'un da ake yi a kasar babbar barazana ce ga Bangladesh, wanda ya zamo abin ɗaukar hankalin duniya musamman lokacin da akai wa ƙasar laƙabi da 'yar baiwa ta fuskar tattalin arziki.

Dawo da martabar arzikin ƙasar na daga cikin gagaruman aikin da ke gaban gwamnati, kamar yadda ƙwararre kan tattalin arziki Debapriya Bhattacharya ya bayyana.

"Zai yi matukar wuya, saboda gwamnati ba ta da ƙarfin siyasar da za ta yi ko samun fitattun 'yan siyasar da za su daidaita lamura."

A 'yan shekarun nan, tattalin arzikin Bangladesh ya bunkasa.

An samu bunƙasa ta fuskar masana'antun tufafi, halin tagayyarar da ma'aikata ke ciki, da korar ma'aikata ya jefa miliyoyin cikin talauci da rashin aikin yi.

An yi ƙiyasin cewa kashi 80 cikin 100 na kayan da ake fitar da shi daga ƙasar ya sanya ta taka matakin ta biyu mafi girma a duniya ta fannin, yayin da China ke sahun gaba.

Amma a shekarar 2022, tattalin arzikin ƙasar ya fara tangal-tangal, saboda halin da duniya ta samu kai na annobar korona.

Mutane suka fara fantsama tituna lokacin da asusun ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar ya rarake, saboda rikita-rikitar da aka shiga kan makamashi.

Zuwa watan Nuwamba 2022, tashin farashin kayayyaki ya kai kusan kashi 10 cikin 100, sai dai wasu na cewa adadin ya fi haka.

A shekarar 2023, Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, wanda a baya ya yi hasashen kuɗin shigar da Bangladesh ke samu za su bunƙasa, har ta yi gogayya da ƙasasshe kamar Singapore, yanayin da ya sa Hong Kong ta amince da ba ta bashin dala biliyan 4 da miliyan 700 domin bunkasa arzikinta.

Sai dai ƙwararru sun gargaɗi matsalolin da Bangladesh ke fama da su, ba za a taɓa warwaresu cikin sauki ba. Yayin da dalilan cikin gida suka taimaka kamar rashin shawara mai inganci kan abin da ya shafi tattalin arziki.

Mastsalar cin hanci da rashawa ita ma ta taka rawa, kuma babu abin da gwamnati ke yi kan hakan.

Kungiyar yaƙi da rashawa ta Transparency International ta sanya Bangladesh a matsayin ƙasa ta 12 cikin ƙasashe 180 da cin hanci da rashawa ya yi wa katutu.

"Jam'iyya mai mulki ba ta da wani shirin kawar da cin hanci da rashawa. Bayan an kammala zaɓe, masu ido da kwalli da ɗaidaikun mutane za su ci gaba da sharafinsu,"inji Dr Bhattacharya.

Yayin da bashin da ake bin ƙasar ke ƙaruwa, 'yan ƙasa da talakawa ne za su ci gaba da ji a jikinsu na matsin tattalin arziki, in ji Ali Riaz, babban jami'i a cibiyar Atlantic Council's South Asia Center.

"Babu wani binciki ko daidaito a ƙasar da jam'iyya daya ce ke jan ragmarta. Babu wanda zai nuna wa gwamnati yatsa, kan yadda ta ke kashe kudi," in ji farfesa Riaz.

Matsalar sauyin yanayi

Matsalar sauyin yanayi babban abin dubawa ce. Bisa ƙiyasi sama da kashi 3 na Bangladesh na kan ruwa ne, kamar yadda cibiyar da ke sa ido kan illar sauyin yanayi ta bayyana.

Akwai hasashen tumbatsar teku da tafkuna za su raba mutum miliyan 35 da muhallansu a gundumomin da ke gaɓar teku, wannan kuma kwata ne cikin al'umar ƙasar miliyan 170.

Karuwar guguwa da mamakon ruwan sama mai iska na ƙara barazana a yanzukunan ƙasar, musamman kudu maso yammacin gundumar Satkhira, wadda ta yi fice wajen noman kayan marmari da na lambu a wasu keɓantattun lokuta.

"Rashin ruwan sha da wuyar da ya ke yi wata babbar matsala ce a yankinmu. Saboda ruwan da ya kewaye mu mai dandanon gishiri ne," inji Shampa Goswami, mazauniyar yankin.

Sai dai sauyin yanayin ba shi ne babbar damuwar a gangamin yaƙin neman zaɓe ba, ta ce yawancin mazauna yankunan karkara ba su san abin da ake nufi da sauyin yanayi ko matsalolinsa ba.

Amma Farfesa Riaz, ya ce an baro tushiyar tun a baya lokacin kafa dimukradiyya.

"Sai fa kana da tsarin da yake duba abubuwa yadda suka dace, amma in ba haka ba babu ta inda zai dinga duba batutuwa irin wannan da kuma zai wayar da kan mutane kan abin da ake nufi da sauyin yanayi amma idan ba haka ba, ihu ne bayan hari," inji shi.

Gwamnatin Bangladesh dai ta ta'allaka ne a kan jam'iyyar mai mulki ta Awami League da ta BNP, tun bayan kawo ƙarshen mulkin soja a shekarar 1991, wasu na ganin dukkan jam'iyyun sun yi wa dimukradiyya rikon sakainar kashi.

"Duk wanda ya samu mulki, abin da wanda ya gada ya yi shi ma hakan zai yi. Zai yi wuya ka bambance wanda ya fi wani tsakanin jam'iyyun biyu''.

''Ana ƙiyasta girman Dimukradiyya a Bangladesh da waɗanda suka jagoranci ƙasar," inji AKM Mohsin, manajan daraktan cibiyar Bangladesh a Singapore.

"Idan suna kan mulki babu abin da ba sa cewa. Amma abin da Bangladesh ke buƙata shi ne jajirtattun shugabanni, da za su samar da dama ga al'umma, ba waɗanda za su yi wadaƙa da dukiyar ƙasa yadda suke so ba."