Manyan ƴan takarar shugaban ƙasar Rwanda


A ranar 15 ga watan Yulin 2024 ne al'ummar Rwanda za su je rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaban ƙasar Paul Kagame, wanda ke kan mulki tun a shekara ta 2000, zai fuskanci hamayya daga wasu ƴan takarar shugaban ƙasa biyu.
Amma duk da haka nan ana ganin cewa shugaban ƙasar shi ne wanda zai samu nasara, inda zai zarce a wa'adin shugabanci na huɗu.
A zaɓen 2017, Kagame ya lashe kashi 99% na ƙuri'un da aka kaɗa, inda bayan haka aka aiwatar da sauyin kundin tsarin mulkin ƙasar inda aka sauya dokar da ta iyakance shekarun wa'adin mulkin shugaban ƙasa.
Wannan ne ya ba shi damar ƙara tsayawa takara.
Paul Kagame zai yi takara da abokan hamayya biyu ne kasancewar hukumar zaɓen ƙasar ta soke takarar wasu ƴan takaran shida.
Ana yaba wa Kagame kasancewar ya yi ƙoƙari wajen sake gina ƙasar mai yawan al'umma miliyan 15 bayan yaƙin basasar ƙasar, wanda ya haifar da kisan kiyashi.
Sama da mutum miliyan ɗaya ne aka kashe a lokacin yaƙin.
Yanzu Rwanda ta zamo wata cibiyar hada-hadar kasuwanci a yankin tsakiyar nahiyar Afirka.











