Kisan kare-dangin Rwanda: 'Na yafe wa wanda ya kashe mijina- ɗanmu ya auri 'yarsa'

- Marubuci, Yves Bucyana
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kigali
Domin warkar da kunar soyayya - wata mata ta yi kokarin yafe wa wanda ya kashe mijinta shekara 28 da suka gabata bayan kisan kare-dangin da aka yi a Rwanda, karewa ma ta yarda ɗanta ya auri 'yarsa.
Bernadette Mukakabera ta dinga bayar da labarinta a wani bangare na kokarin kawo daidaito a cikin al'ummar da ta samu rabuwar kai a 1994 lokacin da aka yanka mutum 800,000 cikin kwana 100.
"Babu abin da ya shafi 'ya'yanmu da abin da ya faru a baya. Sun fara son juna kuma babu abin da zai hana mutane son juna," Bernadette ta shaida wa BBC.
Ita da mijinta daga kabilar Tutsi suke, wanda aka kashe a cikin jirgin saman shugaban Hutu a ranar 6 ga watan Afrilun 1994.
Cikin 'yan awanni, dubban al'ummar Hutu, wata akidar tsanar juna da aka rika koyawa ta hanyar farfaganda, sai aka fara kashe-kashe wanda aka shirya a nutse, suka dinga kokarin murkushe al'ummar Tutsi da ke makwabtaka da su.
Daya daga ciki shi ne Gratien Nyaminani, wanda ke zaune a kusa da gidan Bernadette a Mushaka da ke yammacin Rwanda. Dukkansu manoma ne.
Bayan an gama kashe-kashen, mutanen Tutsi sun karbe iko, an daure daruruwan mutanen da ake zargi da hannu cikin kashe-kashen,
An daure Gratien daga baya kuma aka yi mata shari'a a wata kotu, kuma ta zama cikin wadanda ake zargi.
A sauraren karar da ake yi a karshen mako, an bai wa al'umma dama domin sauraren karara da kuma neman hujja kan zargin abubuwan da suka faru - da kuma abin da yake faruwa yanzu.

Asalin hoton, AFP
A 2004, Gratien ta shaida wa Bernadette yadda ya kashe mijinta ya kuma ba ta hakuri, kuma zaman ya yi masa afuwa.
Wannan na nufin ba zai yi zaman shekara 19 ba a gidan yari, amma ya yi shekara biyu maimakon haka.
'Na so na taimaka'
Yayin zaman kaso na shekara 10 kafin ya nemi afuwar al'umma, iyalansa sun roki a sauya abin tare da Bernadette da ɗansa Alfred, wanda yana shekara 14 lokacin da aka kashe mahaifinsa.

Asalin hoton, BBC
'Yar Gratien mai suna Yankurije Donata, wadda ba ta fi shekara tara ba lokacin da abin ya faru, ta fara zuwa gidan Bernadette domin taimakawa.
"Na yanke hukuncin in rika zuwa ina taimaka wa mahaifiyar Alfred da ayyukan gida, har da ayyukan noma saboda rage mata radadin cewa mahaifina ne ya yi sanadin mutuwar mijinta," ta gaya wa BBC.
"Ina ganin a nan ne Alfred ya fara so na, lokacin da nake taimaka wa mahaifyarsa."
"Ina matukar son halayenta - shi ya sa ban damu ba kan soyayyarta da ɗana." in ji mahaifiyar Alhfred.
Amma a wajen Gratien ba abu ba ne mai sauki - daga farko cike yake da tsoro lokacin da yake neman auren.
"Ya dade yana nanata cewa yaya kuma ta ina iyalan da na kashe wa jigonsu za su ba mu auren 'yarsu." in ji Yankurije.

A karshe dai Bernadette ta amince tare da bayyana cewa ba ta da wani haƙo a ranta da zai hana ta bayar da aure.
"Ba ni da wani abu akanta a raina kan sirikata kan abinda mahaifinta ya yi," in ji Bernadette.
An yi wa ma'auratan aure ne a wata cocin katolika a 2008.
'In babu afuwa, al'umma za ta iya rugujewa'
Coci-coci ne suka ja ragamar kokarin daidaita al'umar da rikicin ya shafa.
Coci ta fuskanci babu wani zabi da bil adama ke da shi in ba na zama tare ba, don haka akwai bukatar a yi abubuwa da yawa domin samar da zaman lafiya da fahimtar juna.
"Zarge-zargen juna kan abin da ya faru ba shi da wata ma'ana ko kadan dole mu yafi juna," in ji fada Ngoboka.
An yi sasantawa ta karshe ne cikin jama'a ga wanda ake zargi wanda aka cutar.
"Wanda aka cutar ya nuna alamun afuwa da hannunsa da kuma yafiya," in ji shi.
Mutane da dama sun je bikin cika shekara 28 da kammala wannan rikici domin koyan mu'amala da juna, lokacin Gratient bai dade da mutuwa ba.
"Gyaran zuciya ya fi mahimmanci kafin mutum ya fara rayuwa mai tsarki."
A nan ne kuma ita Bernadette ta sanar da uaren danta da 'yar wanda ya kashe mijinta.
Ta ce tana fatan labarin soyayyar Alfred da Yankurije ya zama wanda zai bai wa mutane kwarin gwiwar yafiya da sasanci anan gaba.











