Kasashen da aka fi zartar da hukuncin kisa a duniya

Asalin hoton, Getty Images
A makon da ya gabata ne aka zartar ma wani ba’amurke hukuncin kisa ta hanyar shaka masa iskar nitrogen.
Wani ɗan ƙasar Japan ma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan wani harin mai kan uwa da wabi da ya yi sanadin mutuwar mutum 36.
Adadin mutanen da ake zartarwa hukuncin kisan a duniya na ƙaruwa sosai, duk da cewa wasu ƙasashen sun goge hukuncin daga tsarinsu.
Ƙasashe nawa ne ke yanke hukuncin kisa?
Sabbin alƙaluman da aka samu daga Amnesty a 2022:
- Ƙasashe 55 ne ke yanke hukuncin kisa
- Tara daga cikin ƙasashen na yanke hukuncin ne ga manyan laifuka, kamar kisan mutane da dama ko laifukan yaƙi
- Ƙasashe 23 suna da hukuncin a hukumance, sai dai sama da shekara 10 ba a aiwatar da shi ba
Mutane nawa ake yi wa hukuncin duk shekara?
Alƙaluman da AMnesty take da su sun hada da na hukumomi da na kafafen yaɗa labarai da na waɗanda aka yanke wa 'yan uwansu hukuncin.
China ba ta fitar da bayanai kan yadda take yin hukuncin kisa.
Banda bayanan China, Amnesty tana da rahotannin mutum 883 da aka yanke wa wannan hukunci a fadin duniya a 2022.
Wannan ya zarce alƙaluman da aka samu a 2021 na mutum 579 da kimanin kashi 53, kuma wannan ne adadi mafi yawa da aka taba samu tun 2017.
Kazalika, adadin bai kai wanda aka samu ba a shekarun 1988 da 1989 da kuma 2015, inda aka riƙa yanke wa sama da mutum 1,500 hukuncin a kowacce shekara.

Amnesty ta ce an yanke hukunci a ƙalla 2,016 na kisa a 2022, a ƙasashe 25 a faɗin duniya.
A 2021, ƙasashe 56 sun yanke hukunci a ƙalla 2,052.
Da yawan fursunoni sun kwashe shekaru gwammai suna zaman hukuncin kisa gabanin a aiwatar da shi.
Waɗanne ƙasashe ne suka fi aiwatar da hukuncin kisa?
Ƙasashe 20 ne suka aiwatar da hukuncin kisa a 2022, idan an kwatanta da 18 da suka yanke irin hukuncin a 2021.
Amnesty ta yi amannar cewa China da fi yanke hukuncin kisa sama da duk wata ƙasa a duniya.
Saboda tana aiwatarwa mutane sama da dubu wannan hukunci a kowacce shekara, sai dai babu mai tabbatar da hakan.
Bayan China, ƙasashen da suka fi aiwatar da hukuncin sun haɗa da Iran da Saudiyya da Masar da kuma Amurka.

Ta yaya ake samu alƙaluman wadanda aka kashe a ƙasashe daban-daban?
Amnesty ta bayyana wasu ƙasashe 11 a duniya da duk shekara sai sun yanke hukuncin kisa.
Ƙasashen sun haɗa da China da Masar da Iran da Saudiyya da Amurka da Vietnam da kuma Yemen.
An kuma yi amannar Koriya ta Arewa tana yanke wannan hukunci sosai, amma dai babu wata tabbatacciyar majiya kan hakan.

Alƙaluman aiwatar da hukuncin kisa da aka samu daga Saudiyya a 2022 ya zarce na kowacce ƙasa, sama da shekaru 30.
Ƙasashe biyar da suka hada da Bahrain da Comoros da Laos da Nijar da kuma Koriya ta Kudu sun yanke wa mutane da dama hukuncin kisan a 2022, sai dai sun kwashe shekaru ba sa aiwatar da shi.
Haka kuma an samu raguwar wadanda aka yanke wa hukuncin a Amurka tun daga 1999, inda nan ne aka samu adadi mafi yawa.

Mutum nawa aka yanke wa hukuncin kan laifin ta'ammali da kwayoyi?
Amnesty ta ce akwai mutum 325 da aka yanke wa hukuncin kisa saboda ta'ammali da miyagun kwayoyi a 2022 a duka faɗin duniya:
- A Iran mutum 255
- Mutum 57 a Saudiyya
- A Singapore mutum
A 2023 Singapore ta aiwatar da hukuncin kisa kan mace a karon farko cikin kimanin shekaru 20.
Saridewi Djaman ita ce aka yanke wa hukuncin, kan safarar hodar iblis a 2018.
Ƙasashen nawa ne suka goge hukuncin kisa a tsarinsu?
Ba a amfani da hukuncin kisa a ƙasashe 112, idan aka kwatanta da 48 da ake da su a 1991.
A 2022, ƙasashe shida sun goge hukuncin kisa ko dai ba ki ɗaya ko kuma na wani lokacin.
Ƙasashen hudu da suka hada da Kazakhstan da Papua New Guinea da Sierra Leone da kuma Jamhuriar Afrika ta Tsakiya sun goge hukuncin baki ɗaya.
Equatorial Guinea da Zambia suna yanke hukuncin ne kawai idan an aikata mugun laifi.
A watan Afrilun 2023, Majalisar dokokin Malaysia ta kaɗa ƙuri'ar cire hukuncin kisa ga laifuka 11 cikin har da kisan kai da ta'addanci.
A watan Yulin 2023, Majalisar Ghana ta yi kuri'ar soke hukuncin daga tsarin kasar.
Wadanne hanyoyi ƙasashn duniya ke bi don aiwatar da hukuncin kisan?

Asalin hoton, Getty Images
A Saudiyya ne kawai aka yanke kai a matsayin hanyar aiwatar da hukuncin kisa a 2022.
Wasu hanyoyin sun hada da rataya da allura da kuma harbe mai laifi.
Jihar Alabama ta Amurka ta yanke wa wani mutumi mai suna Kenneth Smith hukuncin kisa ta hanyar shaƙa masa iskar nitrogen bayan samun shi da laifin kisan kai.
Shi ne mutum na farko da aka yanke wa hukuncin ta irin wannan hanyar.
Lauyansa ya bayyana hukuncin da wanda ba a saba gani ba.
Jihar Alabama da wasu jihohin Amurka biyu sun yanke shawarar amfani da iskar nitrogen wajen hukuncin kisa, saboda sinadarin allurar Lethal yanzu yana wahalar samu.










