Munanan ɗabi’u da ke jawo wa ƴan Najeriya baƙin jini a ƙasashen ƙetare

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
Hana 'yan Najeriya biza ko sanya masu sharuɗɗai masu tsauri kafin samun bizar shiga wata kasa na sake zama babban kalubale ko barazana ga ƴan kasar.
A lokuta da dama akan samu ƙasashe ƙetare da ke sanya sharuɗɗa masu tsauri kafin samu biza, muddin mutum ya kasancewa ɗan Najeriya.
Shekaru da dama a baya kusan ana iya cewa matsalar biza ga ‘yan Najeriya ba ta bambanta da na sauran mutanen da suka kasance daga nahiyar Afirka ba.
Akwai ƙasashen da cikin sa'o'i ko ta intanet ka na iya shiga ka cike bayanan samun biza nan take, ba tare da nuna wani bambanci kasancewa ɗan Najeriya ba.
Amma a yanzu abubuwan sun sauya, kusan kowacce kasa na nuna fargabar bai wa ɗan Najeriya biza, kama daga na Afirka zuwa Gabas ta Tsakiya da Turai.
End of Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa
Mene ne ya sauya a yanzu?

Asalin hoton, others
A wannan lokaci dai haramcin biza baki ɗaya da Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ta yi wa ƴan Najeriya ya fi ja hankali sosai, da haifar da martani tsakanin ƴan kasar da Dubai ya zame musu wurin hutu da harkokin kasuwanci.
Kafin wannan lokaci, UAE ta sha sanya sharuɗɗa masu tsauri kan ƴan Najeriya da ke son zuwa kasar saboda wasu ɗabi'u da ta ce ƴan kasar na nunawa ko aikatawa a can.
Akwai lokacin da sharuɗɗan ke cewa "ba a amincewa 'yan kasa da shekara 40 shiga kasar ba, sai dai idan tafiyar ta kasance tare da iyali".
Sanna baya ga Dubai akwai ƙasashe irinsu Turkiyya da Kenya da a baya samun bizar su baya wahala ga ƴan Najeriya, amma a wannan lokaci matakan sun kasance masu tsaurin gaske muddin mutum fasfo din Najeriya ya ke amfani da shi.
Hakazalika tafiya Turai ko wasu yankunan gabas ta tsakiya da su Indiya, sharuɗɗan na da wahalar gaske kafin ɗan Najeriya ya samu biza.
To ko me ke haifar da irin wannan matsala ga ‘yan Najeriya? Baba Yusuf, wani masanin lamuran yau da kullum ne da ke da kamfanin kansa a Dubai, kuma a tattaunawarsa da BBC ya fayyace wasu daga cikin manyan dalilan.
Tarbiyya da al’adu

Asalin hoton, BABA YUSUF
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Baba Yusuf wanda ya mallaki takardar zama ɗan kasa a Dubai, ya ce taɓarɓarewar tarbiyya da al’adu na daga cikin dalilan da ke jefa 'yan Najeriya cikin irin wannan kangi idan suka fita ƙetare.
Ya tunasar da cewa watanni biyu da suka gabata aka soma tsaurara irin wannan matakai a Dubai.
Har aka zayyana wasu sharuɗɗai kamar haka: "shaidar takardar ajiyar asusun banki na wata shida, da mutanen da suke da kasa da 40 ba sa shiga daular, sanan mara iyali a ƙasar ko wanda zai je ba tare da iyali ba, ba za a ba shi biza ba".
Kafin wannan lokaci kuma an rinƙa samun rashin jituwa tsakanin ofishin jakadacin Najeriya da UAE.
Baba Yusuf, ya ce akwai aiki ja a gaban Najeriya saboda a galibin ƙasashe ana ganin yadda tsirarun ‘yan ƙasar ke ɓata suna Najeriya da muggan ɗabi’u.
Ya kuma nuna akwai bukatar tun daga filin jirgi sama a tabbatar ana tantace mutane yadda ya dace, da bin ka’idojin bincike domin sanin irin mutanen da ke fita ƙetare da sunan Najeriya.
Baba Yusuf na ganin dai akwai jan aiki a wuyan gwamnatin Najeriya saboda akwai wasu halayya da tabarbarewar tarbiyya da muddin ba a tashi tsaye ba, zai yi wahala Najeriya ta iya tsame kanta a cikin wannan matsala.
Kungiyoyin asiri da ayyukan damfara
Masanin ya kuma ce akwai matsalar kungiyoyin asiri na ‘yan Najeriya da suke fitowa da adduna suna aikata muggan laifi, da ya kasance sabon abu ko baƙo ga ‘yan ƙasar UAE.
Sannan akwai raɗe-raɗin wani ɗan yankin Emirati da ake zargin ‘yan Najeriya da kashe shi tare da kuma ɓoye gawarsa.
Sannan akwai masu ayyukan damfara da su ma ke tadawa hukumomin Dubai hankali, an yi kokari daƙile irin waɗannan ayyuka amma kullum sake girmama su ke yi.
Sannan ko ‘yan kwanaki da suka gabata, an samu faɗa tsakanin ‘yan kungiyoyi asiri da suka sasari junansu a filin jirgin saman Dubai, wadannan abubuwan da kuma ke sake kazancewa ne dalilan hukumomin UAE.
Harkokin kasuwanci
Hadaddiyar Daular Larabawa dai kasa ce da ta fi fice a fanin kasuwanci inda 'yan Najeriya galibi ke yawan zuwa domin saro kayayyaki ko ƙulla harkokin cinikayya.
Sai dai da wannan haramci Baba Abbas na ganin za a soma ganin sauyi muddin ba a gaggauta warware wannan takaddama ba.
"Tabbas wannan mataki zai shafi harkokin kasuwancinsu, da kamfanoni da kuma abokan mu’amala".
Sannan Ya ce shi bai yi mamakin waɗannan matakai ba, saboda tun shekarun baya da suka wuce sun hango haka.
"Dubai birni ne da aka sha wahala wajen ginashi, amma wasu mutane kalilan ke neman rusa kimarsa a idon duniya, wanda kuma su hukumomi ba za su taɓa lamunta ba".
Ya ce babu mamaki matakin UAE a yanzu kokari ne na ganin sun zauna da hukumomin Najeriya domin samar da mafita da hana irin wadannan ɓata gari shiga ƙasarta.










