'Yadda surukata ta ɓata cikin laka bayan mahaukaciyar guguwa'

Asalin hoton, Getty Images
Jikokin Violet Frank guda biyu suna tuna mata surukarta da ta ɓata, bayan afkuwar mummunar guguwar da ta yi sanadin rugujewar ɗaruruwan gidaje.
Ana fargabar cewa za a saka sunanta cikin mutum sama da 300 da suka mutu lokacin da wata mahaukaciyar guguwa ta afka wa Malawi a farkon makon nan.
Surukar ta je zama tare da Violet kwanaki kaɗan bayan mahaifiyarta ta gamu da ibtila'in zaɓtarewar laka.
"Tana tare da ɗana a gidansu na aure da ke yankin Chilobwe.
Ya fito daga cikin gidansu lokacin da ya ji makwabtansa na ihu, abubuwa kuma na ta faɗuwa a wajen gidansu,'' in ji Violet.
"Cikin sa'a, ya samu tsira da rayuwarsa. Nan da nan aka ɗauke shi zuwa asibiti. Amma ba mu san wajen da matarsa take ba."
Lokacin da muka je wurin Violet, mun samu tana duba sauran abin da ya rage a gidan ɗanta.
Wani katon dutse ne ke tsaye a tsakiyar gidan, abubuwa duk sun lalace.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mitoci kaɗan daga gidan matar, wasu jami'an ceto ne ke fitar da wata gawa daga ɓaraguzai da kuma laka. Sai dai ba surukar Violet ba ce.
Ta tambayi ɗaya daga cikin jami'an da su taimaka wajen neman surukarta, amma ba ta samu amsa daga gare su ba.
"Idan ka faɗa wa jami'an ceto wajen da za a nemo mutanen da ba a gani ba, ba sa zuwa wurin. Suna aikin ceto ne kawai a wuraren da guguwar ba ta yi tsanani ba'', in ji ta.
Ta ƙara da cewa ''to amma ya ya ga batun mutanen mu? Yaushe za su je domin cetonsu?"
Yankin Chilobwe na ɗaya daga cikin yankunan da mahaukaciyar guguwar da ta faɗa wa cibiyar kasuwancin Malawi na Blantyre ta fi shafa.
Shawarar da yawancin mazauna yankin suka samu daga wajen hukumomi kafin afkuwar guguwar shi ne su zauna cikin gidajensu, sai dai hakan bai taimaka ba.
Ba a dai san hakikanin gidajen da guguwar ta lalata ba a Chilobwe, amma mun ga manyan duwatsu da itatuwa da suka ruguza gidajen mutane.
Mamakon ruwan sama ya shafe wasu gidaje da dama, inda wasu kuma suka binne a karkashin kasa.
Yankuna kaɗan ne harkokin kasuwanci ke ci gaba da gudana, amma mutane ba sa cikin jin daɗi saboda ibtila'in da ya faɗa wa ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa ana ci gaba da harkoki - amma ba kamar yadda aka saba ba, inda al'ummomi ke taimakawa domin nemo waɗanda suka ɓata.
Mutanen da ruwa bai tafi da gidajensu ba suna ɗauke da faretani da kuma shebur-shebur domin tono waɗanda ke binne a ƙarƙashin ƙasa.
Lokacin da muka samu Richard Galeta, mai shekara 34, yana sanye da fararen kaya, wanda masu sa-kai ke sakawa domin taimakawa wajen binne waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Richard ya binne matarsa da ɗansa a ranar Laraba.
"Ina aiki tukuru domin su. A yanzu da ba sa raye, ban san me zan yi ba," in ji shi.
"Abu na ƙarshe da na faɗa wa matata shi ne cewa zan ba ta kuɗi a wannan mako domin ta kai wa iyayenta ziyara. Amma a yanzu, ni ne zan ziyarce su domin faɗa musu mummunan labarin da ya faru."
A yanzu yana rayuwa ne a cikin wani sansanin wucin gadi da aka kafa a cikin wata makarantar furamare da ke yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Richard ya ce rayuwarsa na cikin mawuyacin hali.
Ya zargi waɗanda ke ba da agaji da rashin ba da kulawa sosai ga waɗanda suka haɗu da ibtila'in, inda ya ce babbar matsala a yanzu ita ce ta samun wadataccen abinci.
"Ƙungiyoyi da dama sun kawo mana abinci. Sai dai abincin ya ɓaci a cikin na'urorin da aka adana da shi da ke cikin ajuzuwa,'' in ji Richard.
Malinga Namuku, wanda ke kula da sansanin ƴan Malawi da ƙungiyar bayar da agaji na Red Cross ta kafa, ya ce suna bai wa mutane abinci.
To amma ya ce a wasu lokuta ƴan sa-kai na wahala wajen tantance waɗanda suka samu abinci da waɗanda ba su samu ba, "Amma muna iyakar kokarinmu."
Akwai yara da dama a sansanin da ke yin guje-guje da wasa da balan-balan.
Idan ka gan su, ba su ɗauki abin da ya faru a matsayin bala'i ba. Amma masana sun ce sai nan gaba za su gane hakan.
Dakta Charles Mwansambo, sakataren lafiya na ƙasar Malawi, ya ce batun lafiyar ƙwaƙwalwar waɗanda suka tsira, shi ne hukumomi za su duba a cikin makonnin da ke tafe.
Sansanin na ɗauke da mutum 5, 000, inda wasu da dama ke ci gaba da zuwa tare da fatan samun wurin zama.
Yawancin mutanen da ke zama a cikin sansanin ba su da wurin zuwa kuma suna da buƙatar agaji, saboda sun kasa gane 'yan uwansu.
Yanayi a wurin ya janyo wahala wajen nema da kuma ceto mutane. A wasu ranaku, jami'an ceto na tsayawa da aikinsu saboda ruwan sama ko kuma hazo.
Waɗanda ke bayar da taimako wajen aikin ceto sun haɗa da 'yan sanda da sojoji da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Ƴan sanda na amfani da karnuka wajen gano gawarwaki.
Ya zuwa ranar Juma'a, sama da mutum 300 ne aka tabbatar da mutuwarsu a Malawi, inda aka samu ƙarin wasu a makwaɓtan ƙasar Mozambique, sannan mutane sama da 80,000 suka bar gidajensu.
Ana hasashen cewa alkaluman waɗanda suka mutu zai ƙaru a cikin makonni masu zuwa, yayin da hazo ke tafiya wanda kuma zai bai wa masu ceto damar ci gaba da aikinsu.
Akalla mutum 200 aka ruwaito cewa sun ɓata - ciki har da surukar Violet. Tana fatan cewa ko gawarta za a gane saboda yi mata jana'iza yadda ya kamata.











