Ko hatsarin jirgin ruwa a Baltimore zai shafi jigilar kaya a duniya?

Asalin hoton, Reuters
Daga Christy Cooney
BBC News
An fara nuna damuwa game da irin tasirin da hatsarin jirgin ruwan dakon kaya ya yi a Baltimore na Amurka kan jigilar kayayyaki zuwa lungu da saƙo na duniya.
Jirgin wanda aka yi wa laƙabi da Dali, ya yi karo da wata dirka daga cikin dirkokin gadar Francis Scott Key da tsakar dare ranar Litinin kuma ya karairaya ta.
Gadar ta kai har bakin shiga tashar ruwan Baltimore, wadda ita ce mafi hada-hadar motoci a Amurka kuma ta tara a yawan hada-hada a ƙasar.
Mutum shida ne ake fargabar sun ɓace zuwa yanzu.
Hukumomi sun ce za a dakatar da hada-hada a tashar - wadda ta kai yawa tan miliyan 47 daga ƙasashen duniya a shekarar da ta gabata - "har sai abin da hali ya yi".
Dakatarwar za ta yi "tasiri mai girman gaske ga harkokin fito na duniya", kamar yadda Marco Forgione darakta a cibiyar The Institute of Export and International Trade ya faɗa wa BBC.
Motoci sama da 750,000 ne suka bi ta Baltimore a shekarar da ta wuce, a cewarsa cikin shirin The World Tonight.
Wannan ya haɗa da kayayyakin Amurka, da Birtaniya, da Tarayyar Turai da ma kamfanonin General Motors da Ford da Jaguar Land Rover da Nissan da Fiat da kuma Audi.
Tashar ta Baltimore ce mafi yawan jigilar motoci a Amurka, kuma ita ce mafi girma a yawan kayan gine-gine da na gona da ake fito.
Kazalika ita ce ta biyu mafi girma a Amurka wajen jigilar gawayi a ƙasar.
Sakataren Sufuri na Amurka Pete Buttigieg ya faɗa a taron manema labarai cewa "babu tantama wannan lamari zai yi tasiri ga zirga-zirgar kaya".
"Ya yi wuri a iya yin hasashen lokacin da za a iya gyara hanyar da kuma buɗe tashar," a cewarsa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai yiwuwar a karkatar da kayayyakin da aka yi fito zuwa manyan tashoshin ruwa.
Tun da farko an bayyana damuwa cewa lamarin zai shafi jigilar iskar gas na LNG, amma kamfanin Cove Point LNG da ke ayyuka a Chesapeake Bay - wanda ke safarar tan 500,000 na LNG duk wata zuwa kasuwannin Birtaniya da Tarayyar Turai - ya ce karyewar gadar bai shafi harkokinsa ba.
Shugaba Biden ya faɗa wa manema labarai cewa Amurka za ta yi "duk mai yiwuwa don buɗe tashar da kuma aikin gina gadar cikin gaggawa", amma ya ce abin zai ɗauki lokaci.
Idan aka duba dukkan hada-hadar da ake yi, tashar Baltimore na samar wa mutum kusan 15,000 aikin yi kuma tana taimaka wa ƙarin wasu 140,000.
Bayan faruwar hatsarin, kamfanin fito na ƙasar Denmark Maersk - wanda jirginsa Dali ya yi hatsarin - ya ce "zai daina bin hanyar Baltimore gaba ɗaya a dukkan harkokinsa nan da wani lokaci".
Wasu kamfanonin jiragen ƙasa da na jigilar gawayi sun gargaɗi kwansotomominsu game da tsaikon da za a iya samu.

Asalin hoton, Reuters
Jami'an tsaron teku na Amurka sun dakatar da aikin ceton da suke yi inda suka koma neman mutanen da suka ɓace.
Yanzu abin da za a mayar da hankali shi ne bincike kan takamaimai abin da ya faru, inda tawagar ƙwararru za su shiga jirgin don bincika na'urar bayanansa da zimmar gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Har yanzu babu tabbas game da abin da ya haddasa hatsarin, amma hukumomi sun ce "matsalar lantarki jirgin ya samu" kuma ya yi kiran neman agaji kafin ya yi karo da gadar.
Hukuamar Maritime and Port Authority of Singapore, inda jirgin ya taso, ta ce lafiyar jirgin ƙalau ya zuwa lokacin da hatsarin ya faru.
Ta kuma ce jirgin ya bi ta tashohin ƙasashe biyu da aka duba lafiyarsa a watan Yuni da Satumban 2023.











