Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne sabon Gwamnan CBN Olayemi Cardoso?
A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin Dr Olayemi Micheal Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).
Hakan na nufin zai maye gurbin Godwin Emefiele, wanda aka dakatar kuma yake fuskantar tuhumar almundahanar kuɗi kusan naira biliyan bakwai a gaban kotu.
A watan Yuni ne Tinubu ya dakatar da Emefiele, sannan 'yan sandan farin kaya na DSS suka kai shi gaban kotu a watan Yuli bisa tuhumar sa da mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba.
Naɗin Mista Cardoso na zuwa ne wata uku bayan naɗa Folashodun Shonubi a matsayin gwamnan CBN na riƙo.
Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu mutum huɗu da shugaban ya amince da su domin naɗawa a matsayin mataimakan gwamnan CBN.
Ko wane ne Olayemi Cardoso?
Tsohon kwamashinan kasafi na Tinubu
Mista Olayemi Cardoso ya shafe fiye da shekara 30 yana jagoranci ne a fannin harkokin kuɗi da tattalin arziki a ciki da wajen Najeriya.
Haifaffen jihar Legas ne da ke kudancin ƙasar kuma ya riƙe muƙamin gwamnati a matsayin kwamashinan kasafi da tsare-tsare na farko a jihar - lokacin da Bola Tinubu ke gwamna daga 1999 zuwa 2005.
Ya yi karatun firamare da sakandare a yankin Ikoyi na Legas, kafin ya samu shaidar digiri a fannin shugabanci daga Jami'ar Aston da ke Birtaniya a shekarar 1980.
Mista Cardoso ya fara aiki a sashen bankuna tare da bankin Ctibank, inda har ya zama mataimakin shugaba. Ya kafa bakin Citizens International Bank, kuma ya shugabance shi tsawon shekara takwas.
Bayan haka, ya zama mamba na majalisar ƙoli ta kamfanoni masu zaman kansu da dama kamar kamfanin hada-hadar man fetur na Chevron da kuma Texaco.
A wajen Najeriya kuma, ya yi aiki da Bankin Duniya, da Ford Foundation, da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Ya yi aiki a matsayin mamba na majalisar bayar da shawara kan harkokin kasafi da tattalin arziki a ofishin mataimakin shugaban Najeriya daga 2015 zuwa 2019.
Ya samu lambobin yabo da yawa a rayuwarsa, ciki har da digirin-digirgir kan jagoranci a kasuwanci daga Jami'ar Aston da ke Birtaniya.
Ya samu shaidar digirinsa na biyu a kan harkokin mulki daga Jami'ar Harvard Kennedy.