Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru 8 na mulkin Buhari

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta kare matakin da ta ɗauka na ciwo basussuka masu ɗimbin yawa a ciki da wajen kasar a shekaru takwas da ta shafe ta na mulki.
Basussukan da kasar ta ciyo ya sanya wasu ƴan Najeriya da masana tattalin arziki sun nuna damuwa a kan matsalolin da kasar za ta iya fuskanta sakamakon yawan basussukan.
Sai dai ministar kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi ta ƙasar, Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa BBC cewa gwamnati ta karɓo bashin ne domin hana ƙasar faɗawa cikin mawuyacin hali a lokacin da ta samu koma-bayan tattalin arziki a shekarun 2016 da 2020.
"Mun samu durƙushewar tattalin arziƙin ƙasa sau biyu, a 2016 da 2020 lokacin annobar korona, mun yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin ƙasar ba ta faɗa cikin mawuyacin hali ba".
"Saboda ƙasa mai girma irin Najeriya idan aka bar ta cikin wannan hali, abin zai ɓaci ne, nesa ba kusa ba", in ji ta.
'Mun rage dogaro kan man fetur'
Ministar ta kuma kara da cewa a lokacin da suka karɓi ragamar mulki a shekarar 2015 kasafin kuɗin kasar ya kai naira tiriliyan 4.5 amma a wannan shekarar kasafin kuɗin kasar ya kai naira triliyan 21.5.
A cewarta bayan gyaran da suka yi wa kasafin kuɗi daga watan Janairu zuwa Disamba sun kuma aiwatar da wasu tsare-tsare domin tabbatar da adalci wajen aiwatar da kasafin kudi:
"Mun shigo da hanyar gyara hanyoyin da ke barin ana ɓarnar kuɗin, kuma waɗannan mun yi su ne ta cikin tsarin shari'a da ake kira 'finance bill'."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Sun taimaka mana mun samu ƙarin kuɗin shiga wa gwamnatin tarayya, daga tiriliyan 3 zuwa tiriliyan 10.7 a bara''.
Zainab Shamsuna ta kuma ce gwamnati ta sauya fasalin kuɗin da ke shigowa.
A cewarta da farko kashi 70 cikin 100 na kasafin kuɗin kasar ya dogara ne a kan man fetur amma a yanzu kashi 65 cikin 100 na kasafin kuɗin ana samun sa ne daga ɓangaren da ba na man fetur ba.
Ministar ta kuma ce durkushewar tattalin arzikin da aka samu a lokacin ɓullar annobar korona ta sa gwamnati sake ciyo bashi
Sai dai a karkashin mulkin shugaba Buhari ne aka samu tashin farashin kayayyaki da faɗuwar darajar naira da kuma ta kara wa kasa dimbin bashi ko da yake ministar ta kare matakin.
"Ba mu ne kaɗai muke da bashi ba, babu kasar da ba ta neman bashi, mun kuma samu shugaban kasa da yake cewa ku amsa domin a yi manyan ayyuka’’.
Game da tashin farashin kayayaki kuwa ministar ta ce ba Najeriya kadai ba ce matsalar ta shafa.
A cewarta matsalar na da nasaba da yaƙin Ukraine da kuma annobar korona.










