Muhimman abubuwa bakwai da jawabin shugaba Buhari ya ƙunsa

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi ga al'ummar ƙasar.
Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar ƙasar ke cikin taraddudi game da shirin sauya fasalin kuɗi na Babban Bankin Ƙasar.
BBC ta zaƙulo maku wasu daga cikin muhimman abubuwan bakwai da shugaban ya faɗa a cikin jawabin nasa.
‘Ina sane da wahalhalun da mutane ke ciki, kuma za a magance su’
A farkon jawabin nasa, shugaba Buhari ya ce ya yanke shawarar yin jawabin ne domin nuna cewa yana sane da halin da ake ciki kuma domin ya nuna tausayawarsa kan wahalhalun da al’umma suka tsinci kansu a ciki sanadiyyar kokarin aiwatar da sabon tsarin kuɗi da ƙasar ta ɓullo da shi.
Ya ce “na yi takaicin hakan matuƙa kuma ina tausaya maku kan abubuwan da ke faruwa waɗanda ba haka muka so ba.”
A sake fito da tsofaffin N200 domin ci gaba da cinikayya
Shugaban na Najeriya ya ce yanzu haka a ƙoƙarin sauƙaƙa wa mutane wahalhalun da suke ciki kan ƙarancin takardun kuɗi, ya buƙaci CBN ya fito da tsofaffin takardun N200.
Ya ce “na bai wa CBN umurnin sake fito da tsofaffin takardun kuɗi na N200 domin a ci gaba da hada-hada da su, lokaci guda tare da sababbin takardun kuɗi na N200, da 500, da 1,000 har nan da kwana 60, daga 10 ga watan Fabrairu zuwa 10 ga watan Afrilun 2023, lokacin da za su daina aiki.”
CBN zai ci gaba da karɓar tsofaffin takardun N1,000, 500
Shugaban ya kuma yi ƙarin haske kan makomar takardun kuɗi na N500 da 1,000, inda ya ce “bisa dogaro da sashe na 20(3) na dokar CBN ta 2007, za a ci gaba da karɓar takardun kuɗi na N1,000 da 500 a Babban Bankin Najeriya da kuma cibiyoyi na musamman.”
Yaƙi da rashawa da inganta tattalin arziki
Shugaba Buhari ya ce “ina son na ƙara tabbatar wa al’ummar Najeriya cewa har yanzu babbar manufarmu ita ce ƙarfafa tattalin arziƙi, da inganta tsaro, da toshe hanyoyin zurarewar kuɗi ta hanyoyin da ba su dace ba.”
"Zan ci gaba da kare alƙawarin da na ɗauka na kare muradun Najeriya da al’ummarta a kowane lokaci.”
End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
‘Na umurci CBN ya samar da isassun kuɗi’
Domin maganace wahalhalun da al’umma ke fuskanta kan sauya fasalin na naira, a cewar shugaba Buhari “na umurci Babban Bankin Najeriya ya yi duk mai yiwuwa wajen wayar da kan al’umma game da wannan tsari, da kuma samar da isassun takardun kuɗi ga al’umma ta duk hanyar da ta dace, haka nan a tabbatar al’umma sun samu damar ajiye kuɗaɗensu a banki.”
“Na kuma umurci CBN ya haɗa hannu da hukumomin yaƙi da rashawa domin ganin an hukunta duk waɗanda suka yi yunƙurin yin zagon-ƙasa ga shirin.”
Rage hauhawar farashi
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tsarin na sauya fasalin kuɗi zai taimaka wajen rage hauhawar farashi. Ya ce hakan zai faru ne sanadiyyar raguwar yawan zagayawar takardun kuɗi a hannun al'umma.
Zaɓen 2023
Shugaban na Najeriya ya kuma tunatar da al’ummar Najeriya cewa babban zaɓen ƙasar na ƙaratowa, inda ya ce “a ranar 25 ga watan Fabarairun 2023 ne za a zaɓi sabon shugaban ƙasa da wakilan majalisar dokoki. Ina sane cewa wannan sabon tsarin kuɗi ya taimaka wurin rage tasirin kuɗi a harkar siyasa.”
“Wannan wani ci gaba ne idan aka kwatanta da baya, kuma babban abin alfahari ne ga wannan gwamnati a matsayin tushen tabbatar da zaɓuka na gaskiya da adalci.”
"Ina ƙarfafa wa ƴan Najeriya gwiwa su fita su zaɓi ƴan takaran da suke so ba tare da jin tsoro ba, domin za a samar da tsaro, kuma ƙuri’arku za ta yi tasiri.”











