Sarauniya Elizabeth II: Abin da ya sa matasan Afirka ke kira ga Turawa su nemi afuwarsu

Matasan Afirka sun shaida wa BBC cewa suna bukatar gidan Sarautar Birtaniya ya nemi afuwar su saboda mulkin mallaka da kasar ta yi wa nahiyar.

A wani gidan rediyon da ke tsakiyar birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, MJ Mojalefa na gabatar da wani shiri game da mutuwar Sarauniya, wanda masu sauraro ke bugo waya domin bayyana ra'ayoyinsu.

DJ, mai shekara 22, ya bukaci 'yan uwansa matasa da su tuno da irin ukubar da Birtaniya ta jefa kasashen Afirka ciki har da Afirka ta kudu.

“Birtaniya [Sarauniya] ta yi mana mulkin mallaka, ba za mu iya sauya wannan dangantaka ba,” in ji wani wanda ya kira a waya yayin gabatar da shirin.

''Ya kamata mu manta, abin da ya faru, ya riga ya faru,” in ji wani kuma daban.

To amma a ganin MJ Mojafela, yana bukatar neman afuwa ne daga Sarki Charles lll.

''Mutane da dama sun ce Sarauniya ba ta nemi afuwarmu ba, to mu yanzu wannan afuwar muke so a zo a nema.”

Afirka ta kudu ta zama jamhuriyya a shekarar 1961. Daga nan aka shiga kangin wariyar launin fata na tsawon shekara 13.

Wannan batu ya bar mutanen Afirka ta kudu da dama da tunanin yadda za su manta da shi.

Yayin da yake magana game da yadda kakarsa ta sha bakar azaba a zamanin wariyar launin fata, Mayongo cewa ya yi abu ne da tabonsa ba zai taba warkewa ba daga zukatanmu.

To amma duka sun ce wannan ne lokacin da ya fi dacewa ga sabon Sarkin da ya gina sabuwar dagantaka da nahiyar.

De Oliveira, ya ce ''Muna tunanin sabuwar dangantakarmu da sabon Sarkin za ta ba shi damar sauke nauyin da ke kansa, na zuwa nahiyarmu domin mu yi sulhu da shi.

Da aka tambaye shi ko ya za a yi wannan sulhu? sai ya ce a dawo mana da ma'adinanmu da aka kwashe mana, ciki har da katon lu'u-lu'un da suka sace mana, wanda a yanzu yana daya daga cikin manyan sarkokin gidan sarautar Birtaniya.

Haka kuma masu kiraye-kirayen neman afuwar Afirka na ci gaba da fafutuka a arewacin birnin Nairobi na kasar Kenya.

A makon da ya gabata ne dai kasar ta samu sabon shugaban kasa, wanda kuma shi ne shugaban kasa na biyar tun bayan samun 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1963.

Duk da cewa hankulan 'yan kasar ya karkata ga batun sabon shugaban kasar, amma mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ll ne ya mamaye kanun labaran manyan jaridun kasar.

Lamarin da kuma ya sabunta muhawara game da dangantakar kasar da sabon Sarkin Birtaniya.

''Abin bakin ciki ne mun rasa rai,” in ji Nelson Njau mai shekara 30.

Ya ce: “Amma abin da suka yi wa kasashen Afirka na gurbata mana al'adunmu da sace mana dukiyarmu, da al'umarmu, tabbas ya kamata su zo su nemi afuwarmu.”

A kusa da shi Sammy Musyoka ne mai shekarar 29, jinjina kansa kawai ya yi yana mai ishara ga amincewa da maganar dan'uwansa, sannan ya ce ''Har yanzu muna jin radadin yadda suka yi mu'amala da mu a matsayin bayi''.

A shekarar 2013, gwamnatin Birtaniya ta amince ta biya tsofaffin Kenya har mutum 5,000 , fam miliyan 19.9 a matsayin diyya saboda ukubar da aka ba su lokacin mulkin mallaka.

To amma su tsoffin Kenya ba kamar matasan kasar ba, suna matukar nuna damuwarsu ga mutuwar Sarauniyar, saboda har yanzu tana da farin jini a zukatansu.

Caroline Murigo, mai shekara 50, ya ce mutuwar Sarauniyar abin bakin ciki ne, saboda ya santa.

''Ba mu ji dadin mutuwarta ba , amma ba yadda muka iya lokacinta ne ya yi, kuma muna yi wa sabon Sarki fatan alkairi, saboda zai amfani kasarmu,” in ji Mary Muthoni, mai shekarar 46.

Ta kara da cewa ''Za su taimaka mana mu inganta tattalin arzikinmu, da abubuwan more rayuwa a kasar.”

A Najeriya ma wata cocin Angalikan ce ta shirya taron addu'o'in tunawa da Sarauniyar a Abuja babban birnin kasar.

Shugaban Cocin Reverend Ali Buba Lamido, ya ce ''Cocin Angalikan ta samo asali ne daga Cocin Ingila, kuma tarihi ya nuna cewa Sarauniya ko Sarki shi ne babban shugaban Cocin, don haka ita ce shugabar Cocinmu.”

Wakiliyar BBC da ta halarci taron addu'o'in ta ce mutanen na cikin yanayi na alhini, to amma wasu da dama sun ki halarta, saboda tunawa da suke yi da mulkin mallaka da Sarauniyar ta jagoranta a Afirka.