'Wuraren gyaran gashi na taimaka mana wajen ɗebe wa kanmu kewa'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Turpekai Gharanai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan
"Ba a bari na bar gidana da kaina, amma na yi nasarar shawo kan mijina, kuma an ba ni izinin ziyartar wurin gyaran jiki da kwalliya sau biyu ko uku a shekara."
Tattaunawar da akan yi a wurin gyaran gashin ya isa ya ɗeba wa Zarmina mai shekaru 23 kewa da ƙunci - hakan na sanyawa ta ji tamkar ta samu 'yanci daga danniyar mutane da kuma ikon maza.
Ta yi aure tana da shekara 16. Duk da cewa ta yi nasarar kammala sakandare, dangin mijinta ba su yarda ta shiga jami’a ba.
Zuwa wajen gyaran gashi na daya daga cikin abu mai muhimmanci a rayuwarta amma sai ga Taliban ta umurce wuraren gyaran gashi su rufe daga ranar 24 ga watan Yulin 2023.
Bankwanan baƙin ciki
A ziyararta ta karshe, wata daya da ya gabata, Zarmina ta je gyaran gashin wadda a daidai lokacin ne labarin haramta wuraren gyaran gashin ya shigo.
Mahaifiyar 'ya'ya biyu ta ce "Da jin labarin, mai gidan gyaran gashin a nan take ta firgice kuma ta fara kuka. Ita ce mai ciyar da iyalinta."
Kimanin mata 60,000 ne ke aiki a wannan fanni a fadin Afghanistan.
"Ban iya kallon madubi ba a lokacin da ake min gyaran gira, kowa na zubar da hawaye, ko ina ya kasance shiru."

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Zarmina ta kasance tana zuwa wurin gyaran gashin tare da wata mata 'yar unguwarsu, sannan kuma ta kulla abota mai zurfi da daya daga cikin ma'aikatan gyaran gashi.
"A da dai, mata kan yi magana kan yadda za su yi tasiri ga mazajensu, wasu kuma suna korafi a kan wasu halaye na mazansu."
Amma rikicin tattalin arzikin ya rika kutsawa sannu a hankali bayan da Taliban ta karbi mulki a watan Agustan 2021.
"Yanzu mata kawai suna maganar rashin aikin yi da wariya da talauci ne."
Zarmina na zaune ne a Kandahar da ke kudancin Afganistan, matattarar 'yan mazan jiya na Taliban inda babban shugaban ke zaune.
Ta ce a nan ya zama ruwan dare maza kan hana ‘ya’yansu mata yin kwalliya ko kuma zuwa wajen masu gyaran gashi.
"Yawancin mata suna yawo da burka ko hijabi a nan, mun yarda da shi a matsayin wani bangare na al'adunmu."
Mijinta ya rasa aikinsa shekaru biyu da suka wuce wanda hakan ya sa ya nemi aiki a wani gari daban. Zarmina tana samun kuɗin kanta ta hanyar koyar da yara ƙanana.
Yayin da ta ke tafiya gida a wata rana cikin watan Yuni, ta ci gaba da waiwayawa tana kallon gidan gyaran gashin da sanin cewa ba ƙaramin asara ta yi ba - 'abin da ya zai cutar da 'yancin ta.
"Ni da kaina nake biyan kudin gyaran gashina kuma hakan yana ba ni ƙarfi da iko, ina da kuɗi amma yanzu ba daman kashe wa kaina saboda babu wajen gyaran jiki, hakan yana sa na ji ni tamkar wata talaka."
Kyau da kuma daraja
Madina ‘yar shekara 22 ce tana zaune a gidansu da ke a birnin Kabul lokacin da ta ji labarin haramta wuraren gyaran gashi da kwalliya.
"Kowace macen da na sani tana son inganta salonta, ina son sabbin kayan yayi da kuma yin kwalliya."

Asalin hoton, Getty Images
Ta ce zuwa gidan gyaran gashi yana taimaka wa aurenta, inda ta ce kullum ji take yi kamar sabuwar amarya.
“Hakika mijina yana son ganin gashina a gyare da kuma kitso kala-kala.
"Kodayaushe shi ne yake kai ni gidan gyaran gashin kuma yana jira a bakin kofa har a gama min." in ji Madina
"Kullum cikin yaba kwalliyata yake yi idan na yi, wanda hakan ke sa na ji daɗi."
Burinta ita ce ta zama lauya amma Taliban ta hana mata zuwa jami'a. Ba ta iya samun aiki ba saboda an hana mata aiki da yawa.
Madina tana rufe kanta da gyale idan za ta fita daga gida. Mijinta da matan danginta ne kawai ke iya ganin gashinta.

Asalin hoton, Getty Images
Ta tuna zamanin da aka yi gabanin Taliban ta karbi mulki, tana mai cewa mata a lokacin suna da ƴanci.
Madina ta kasance tana raka mahaifiyarta gidan gyaran jiki tun tana karama ta tuno yadda mata ke bayyana tarihin rayuwarsu a fili.
"Ma'aikatan mata a cikin gidan gyaran gashin ba sa sanya siket ko wando kadai, duk suna cikin hijabi."
Kuma kowa a tsorace yake.
"Babu wanda ya san masu goyon bayan ƴan Taliban kuma babu wanda ke son ya ce komai game da siyasa."
A da ana bari angwaye suna kallon amarensu a lokacin da ake musu kwalliya. Madina kuma ta tuna da wasu maza suna daukar hotuna ma a cikin gidan gyaran jikin. Amma yanzu duk an haramta hakan.
Amma aƙalla Madina tana da abubuwan tunawa masu faranta rai a lokacin aurenta, wadanda har abada ba za ta iya mantawa da su ba.
Ta ce "Na je gidan gyaran jiki na yi gyaran fuska, an yi min kwalliyar amare kafin aurena a bara."
"Lokacin da na kalli kaina a madubi, na yi kyau sosai, kwalliayar ta canza ni, ba zan iya kwatanta farin cikina ba a ranar."
Magani a kaikaice
Ga Somaya mai shekaru 27 daga birnin Mazar-i-Sharif da ke arewa maso yammacin ƙasar, gidan gyaran jiki da kwalliya ya zama dole.

Asalin hoton, Getty Images
Shekaru uku da suka wuce, ta gamu da kone-kone a fuskarta tare da rasa gira da gashin ido, bayan da wani na'urar dafa ruwa da ke ɗakinta ya fashe.
"Ba zan iya jurewa kallon fuskata ba, na yi muni da yawa," Somaya ta ce cikin hawaye.
"Na ɗauka kowa na kallo na kuma suna min dariya saboda bani da gira, na yi wata biyu ban fita ba, nayi kuka sosai a lokacin."
Maganin asibiti ya warkar da raunukan fuskarta da kuma gidan gyaran jiki da ya taimaka wajen dawo mata da gane ƙimar kan ta.

Asalin hoton, Getty Images
"Na je gidan gyaran jiki inda akayi wa fuskata kwaskwarima kuma ya sa na yi kyau sosai," in ji ta.
"Da na kalli girata sai na fara kuka, hawaye ne na farin ciki, gidan gyaran jiki ya dawo min da rayuwata."
Bayan da Taliban ta karɓi mulki, an rufe wuraren gyaran jiki da dama a garinta.
Fastocin da ke tallata gidajen gyaran jikin, an lalata su saboda suna ɗauke da fuskokin mata da kwalliya.
Ƴan Taliban sun hana nuna fuskar mata ba tare da sun rufe da burka ba, inda idon ta kawai za a iya gani.
Somaya tana da Mastas digiri a fannin ilimin halayyar ɗan adam kuma tana aiki a matsayin mai ba da shawara kan lafiyar kwakwalwa.
Ta ga yawan mata da ke neman kulawarta na karuwa tun bayan da kungiyar Taliban ta sanya takunkumi.

Asalin hoton, Getty Images
Ba ita kaɗai ba ce take amfani da gidan gyaran jiki don magani.
A wannan ƙasa da yaki ya ɗaiɗaita, mata da yawa suna fama da taɓo a fuska da raunuka, kuma ba su da halin biyan makudan kuɗi wajen sake gina jikinsu ba.
"A wajen mu mata, gidan gyaran gashi ya fi wuraren yin kwalliya, yana taimaka mana mu ɓoye baƙin cikinmu, ya ba mu kuzari da fata."
(An canza duka sunaye)











