Taƙaitaccen motsa-jiki mai taimakawa masu ciwon suga - Bincike

Wani bincike da aka gabatar a wurin taron gidauniyar masu ciwon suga, ya nuna cewa yin tattaki na tsawon minti uku a duk rabin sa'a kan taimaka wajen daidaita sinadarin suga a cikin jini.

Binciken, wanda ya yi nazari a kan mutum 32 masu cutar, hawa na ɗaya (type 1) ya nuna cewa sidanarin sugansu yakan ragu, idan suka yi sassarfa ko taƙaitaccen motsa-jiki a cikin duk sa'a bakwai.

Gidauniyar masu ciwon suga ta Burtaniya ta ce ''taƙaitaccen motsa-jiki yakan taimaka wajen rage kamuwa da cutar.

Akwai masu ciwon suga kusan mutum 400,000 a Burtaniya.

Cutar na faruwa ne a lokacin da ƙwayoyin garkuwar jiki suka auka wa sidanarin insulin da ke samar da ƙwayoyin halittun jiki a tumburƙuma.

Hakan sai ya sa tumburƙumar ta daina samar da sinadarin insulin - lamarin da zai janyo ƙaruwar sinadarin suga a cikin jini.

Ana buƙatar mutane su riƙa shan maganin da zai taimaka wajen samar da sinadarin na insulin a kai - a kai.

'Yin waya ana tattaki'

A lokuta da dama cutar kan zo da matsaloli masu yawa, kamar matsalar ƙoda da ta ido da kuma ciwon zuciya.

Dakta Elizabeth Robertson, daraktar bincike a gidauniyar ciwon siga ta Birtaniya, wadda ta ɗauki nauyin nazarin, ta ce ga mutanen da ke ɗauke da cutar matakin type 1, ba abu ne mai sauki ba daidaita sinadarin sigarsu.

Ta ƙara da cewa binciken ya gano wasu abubuwan da za su taimaka wa mutane wajen raguwar hatsarin kamuwa da cutar, kamar yin waya yayin da ake yin tattaki, da ware lokaci na tashi domin kewayawa domin gujewa dogon zama ga masu aikin zama.

"Za mu ci gaba da faɗaɗa binciken domin gano tsawon wane lokaci wannan hanya za ta amfanar."

Shugaban binciken Dakta Matthew Campbell, na jami'ar Sunderland, ya ji daɗin sakamakon binciken wanda ya nuna tasirin motsa jiki na ɗan gajeren lokaci.

Ya ƙara da cewa ga mutanen da ke ɗauke da ciwon siga nau'in type 1, 'taƙaitaccen motsa-jiki' zai zama wani mataki mai muhimmanci wajen taƙaita cutar.

Ga sauran mutane da ba sa ɗauke da cutar, yin hakan zai taimaka musu wajen daidaita adadin sidanarin glucose a jikinsu.

A farkon binciken wanda kawo yanzu ba a wallafa ba, mutum 32 masu ɗauke da cutar nau'in type 1 sun kwashe sa'o'i bakwai a zaune.

A ɗaya ɓangaren kuma sun kasance a zaune. A ɗaya ɓangaren kuma an umarce su da su tashi su kewaya na mintuna uku cikin kowanne minti 30, a tsawon sa'o'in bakwai.

An kuma ci gaba da lura da yawan sinadarin sigarsu cikin sa'o'i 48 tun daga lokacin da suka fara zaman, an kuma ba su abinci iri ɗaya a tsawon sa'o'in bakwai kuma bai sauya musu sinadarin insulin ba.

Bayan binciken, sakamakon ya nuna cewa, mutanen da suka riƙa ɗaukar hutun minti uku cikin kowanne mintuna 30 sinadarin sigarsu ya ragu zuwa kashi 6.9 mmol/L. har tsawon kwana biyu.

Su kuma waɗanda ba su ɗauki hutu ba, sinadarin sigarsu ya ƙaru da kashi 8.2 mmol/L.

Yin tattaki kan taimaka wajen ƙara yawan lokacin sinadarin sigar zai ɗauka a jikin mutum.

Dakta Campbell ya ce yana fatan kammala faɗaɗa binciken domin gano amfanin wannan hanya.

Ya ƙara da cewa ''Haƙiƙa sakamakon hanya ce mai sauƙi da za ta ƙarfafa wa mutane gwiwa wajen ɗaukar matakan kariya.''

Mene ne ciwon suga?

Ciwon Suga cuta ce da ke sa sinadarin siga da ke cikin jinin mutum ya ƙaru sosai.

Ciwon suga ya kasu gida biyu:

type 1 - Inda ƙwayoyin garkuwar jiki ke farwa tare da lalata ƙwayoyin da ke samar da sinadarin insulin.

type 2 - Inda jiki ke gaza samar da wadataccen sinadarijn insulin, ko kuma ƙwayoyin halittar jiki ke gaza jin sinadrin na insulin.

Cutar suga nau'in type 2 ta fi zama gama-gari fiye da type 1.