Mece ce ƙwayar mifepristone kuma a ina aka haramta zubar da ciki?

Mifepristone and Misoprostol pills are pictured Wednesday, Oct. 3, 2018, in Skokie, Illinois. (Erin Hooley/Chicago Tribune/Tribune News Service via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amurka ta amince da amfani da ƙwayar maganin tun shekara ta 2000
    • Marubuci, Natasha Preskey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Wasu kotunan Amurka na yunkurin yanke hukuncin cewa ko likitocin hana zubar da ciki da masu fafutuka za su iya hana amfani da ƙwayoyi zubar da ciki na mifepristone saboda dalilai na lafiya.

Kwayar zubar da cikni ta kasance doka a Amurka tun shekara ta 2000 kuma an sassauta ka'idojin maganin a hankali tun daga 2016. Sauye-sauye na baya-bayan nan ga dokokin Hukumar Abinci da Magunguna (FDA) sun bayar da izinin aika kwayoyin zubar da ciki ta hanyar imel kuma a aika su a cikin kantinan sayar da magani ba tare da takardar yadda za a yi amfani da shi ba daga likita.

Demonstrators hold up signs during a protest in front of the Supreme Court during the "Bans Off Our Mifepristone" action organized by the Woman's March outside of the Supreme Court on March 26, 2024 in Washington DC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar goyon bayan zubar da ciki a wajen Kotun Kolin Amurka

Wannan ne ƙarancin samun damar zubar da ciki wanda za a iya soke shi idan shari'ar ƙungiyar likitoci da masu fafutuka ta yi nasara.

Jihohi da dama sun gabatar da kusan haramcin zubar da ciki tun bayan da aka soke hukuncin Roe v Wade wanda ya ba da damar zubar da ciki a shekarar 2022.

Ana sa ran yanke hukunci kan batun kwayar zubar da ciki a karshen watan Yuni.

A ina ne aka haramta zubar da ciki a faɗin duniya?

Wasu ƙasashe 21 sun saka haramcin zubar da ciki gaba ɗaya, a cewar bayanai daga cibiyar kare hakkin masu haihuwa.

Ƙarin ƙasashe da dama sun sanya tsauraran dokoki kan dalilan da za su sa a zubar da ciki, kuma suna barin a yi haka ne kawai don ceton rayuwar mahaifiya ko kuma wadda aka yi wa fyaɗe.

A Afrika, yawancin ƙasashe suna da dokokin da suka takaita zubar da ciki, duk da cewa wasu - ciki har da Afrika ta Kudu da Mozambique ba su takaita ba.

Sai dai Kongo, Senegal, Saliyo, Mauritania, Madagascar da kuma Masar sun haramta zubar da ciki gaba ɗaya.

Map showing 'Legal status of abortion around the world'

Ƙasashe da dama a Turai sun ba da damar zubar da ciki ne saboda dalilai na tattalin arziki (idan aka yi la'akari da tasirin haihuwar yaro daga wajen mai juna biyu, ciki har da zamantakewarsu ko kuma tattalin arziki). Sauran ƙasashe ciki har da Australiya da New Zealand su ma suna barin a zubar da ciki ne kawai idan buƙatar hakan ta taso.

A Amurka, lamarin yana cike da sarkakiya. Dokokin sun bambanta daga jiha zuwa jiha tun bayan da aka soke tabbacin haƙƙin zubar da ciki har zuwa lokacin tayin (kimanin makonni 24) a 2022.

Mene ne mifepristone kuma a ina ake amfani da shi a duniya?

A woman holds a sign during a demonstration called to commemorate the International Women's Day on 8 March 2024 in Buenos Aires, Argentina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An amince da ƙwayar maganin a ƙasashe 96 - na baya-bayan nan a Argentina

Mifepristone shi ne kwayar magani na farko da aka yi amfani da shi a mataki na biyu wajen zubar da ciki. Yana aiki ne ta hanyar toshe mahaifa, wanda kuma ake buƙata domin samun ciki.

Daga nan kuma ake amfani da kwayar maganin na biyu, misoprostol, domin wanke mahaifa. Binciken da Amurka ta yi, ya nuna cewa ƙwayoyin maganin mai mataki na biyu yana aiki da kashi 95 a kowane lokaci.

An fara amincewa da Mifepristone ne a Faransa a 1988, kuma a cewar bayanai daga cibiyar Gyunity, ta ce a yanzu an amince da kuma amfani da ƙwayoyin a ƙasashe 96 - na baya-bayan nan su ne Argentina, Ecuador, Japan da kuma Niger a bara.

Boxes of mifepristone

Asalin hoton, Reuters

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta lissafa zubar da ciki ta hanyar amfani da ƙwayoyin mifepristone da misoprostol a matsayin ka'idoji na zubar da ciki mai haɗari.

Ta ce za a iya shan kwayoyin ko da ba a wajen likita ba idan mata suka samu bayanai da suka dace da kuma kulawar lafiya idan akwai buƙatar hakan.

A Amurka, an amince da amfani da mifepristone har zuwa makonni goma bayan ɗaukar ciki, sai dai a wasu ƙasashe da dama, ana amfani da maganin ne bayan makonni 13 zuwa 26.

Shin amfani da mifepristone yana da illa?

Anti-abortion advocate Melanie Salazar of San Francisco poses for a portrait outside the Supreme Court in Washington, DC, on 26 March 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu adawa da zubar da ciki sun gudanar da zanga-zanga a wajen Kotun Kolin Amurka a Washington

Ana sa ran jin raɗaɗi da kuma zubar jini bayan shan kwayar mifepristone kuma alamu ne da ke nuna cewa maganin yana aiki (duk da cewa babu tabbas).

Wasu abubuwa da ake ji bayan shan maganin sun kunshi kasala, mura, amai da gudawa, ciwon kai da kuma jiri.

WHO ta ce ƙwayoyin mifepristone da misoprostol ba su da haɗari kuma sun kunshi magunguna da ke cikin jerin da ake buƙata.

Binciken da Amurka ta yi, ya nuna cewa maganin mai mataki biyu na buƙatar ƙarin sa ido na likitoci na kasa da kashi ɗaya.

Anti-abortion activists protest against the availability of abortion pills at neighbourhood pharmacies

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu adawa da zubar da ciki sun buƙaci a takaita damar samun maganin zubar da ciki na mifepristone

Masu gwagwarmayar adawa da batun zubar da ciki sun ce zubar da ciki yana da haɗari kuma ba ya aiki a kowane lokaci.

Sai dai, iƙirarinsu bai samu goyon bayan ƙungiyoyin lafiya da ke sahun gaba ba, kamar WHO da kuma ƙungiyar likitoci ta Amurka.

A cewar Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA), ta ce mutum biyar cikin miliyoyin mutane masu amfani da maganin zubar da ciki na mifepristone ne ke mutuwa.

Wani bincike da Ƙungiyar Likitoci ta Amurka ta yi a 2001, ya gano cewa kusan mutum 20 ne ke mutuwa cikin miliyoyin mutane masu amfani da ƙwayar penicillin.