Real ta lashe Champions League na 15 daga wasan karshe 18

Real Madrid ta lashe Champions League na 15 jimilla ranar Asabar 1 ga watan Yuni a Wembley, wadda ta buga wasan karshe na 18 a gasar.

Kungiyar dake Santiago Bernabeu ta doke Borussia Dortmund 2-0, wadda tuni ta ɗauki La Liga na bana, kuma na 36 a tarihi.

Wannn shi ne karon farko da Real Madrid da Borussia Dortmund suka fafata a wasan karshe a babbar gasar tamaula ta Turai, amma karo na 15 da za su kece raini.

Wasan karshe na 18 a Champions League da lashe kofi na 15 jimilla

Real Madrid ce kan gaba a yawan zuwa karawar karshe a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, kuma ita ce kan gaba a yawan lashe kofin a tarihi.

Real ta fara daukar kofin farko zuwa na biyar tare da jagorancin Di Stefano tsakanin 1956 zuwa1960.

Ƙungiyoyin da ta doke a lokacin sun hada da Reims 4-3 da Fiorentina 2-0 da Milan 3-2 da Stade de Reims 2-0 da kuma Eintracht Frankfurt 7-3.

Bayan da Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Benfica da kuma Inter a 1962 da kuma 1964, daga nan ta dauki na shida da ake kira La Sexta a 1966 bayan nasara a kan Partizan 2-1.

A 1981, Madrid ta kasa daukar Champions League, bayan rashin nasara a hannun Liverpool.

Daga lokacin kuma ta dunga lashe dukkan karawar da ta kai wasan karshe ta kuma doke Juventus ta dauki La Séptima a Amsterdam a 1998, bayan cin 1-0.

Haka kuma ta dauki na La Octava bayan doke Valencia 3-0 a Paris, sai ta ɗaga La Novena a wasan da ta doke Bayer Leverkusen 2-1 a Glasgow a 2002, shi ne lokacin da Zidane ya ci ƙwallo mai kayatarwa.

Sauran kofunan da ta lashe

A kakar 2014 tare da Ancelotti a kan ragama ta dauki La Decima a Lisbon da cin 4-1 har da ƙwallo mai kayatarwa da Ramos ya ci.

A 2016 Real Madrid ta doke Atletico ta dauki La Undecima a birnin Milan.

Haka kuma Real Madrid ta ɗauka a 2017, wato La Duodécima a birnin Cardiff bayan nasara a kan Juventus da cin 4-1.

A 2018, Real ta doke Liverpool da cin 3-1 ta lashe La Decimotercera.

Sai kuma a 2022, Real Madrid ta kara yin nasara a kan Liverpool da cin 1-0 a Paris ta dauki na 14 jimilla, wato La Decimocuarta.

A 2024, Real Madrid ta dauki Champions League na 15 jimilla.

Jerin wadanda suka lashe Champions League da yawa a tarihi

  • Real Madrid CF 15
  • AC Milan 7
  • FC Bayern Munich 6
  • Liverpool 6
  • FC Barcelona 5
  • Ajax Amsterdam 4
  • Inter Milan 3
  • Manchester United 3
  • Chelsea 2
  • FC Porto 2
  • Juventus FC 2
  • Nottingham Forest FC 2
  • SL Benfica 2
  • Manchester City 1
  • Borussia Dortmund 1
  • Olympique de Marseille 1
  • Crvena Zvezda 1
  • PSV Eindhoven 1
  • FCSB Steaua Bucarest 1
  • Hamburger SV 1
  • Aston Villa 1
  • Feyenoord Rotterdam 1
  • Celtic Glasgow 1