Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda gungun ƴandaba suka mamaye Haiti
- Marubuci, By Vanessa Buschschlüter
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Online Latin America and Caribbean editor
Dubban fursunoni ne suka tsere bayan da gungun ƴan bindiga suka fasa gidajen yarin da ake tsare da su, a ƙasar da ba ta da zaɓabɓen jami'i da kuma shugaban gungun ƴan bindiga wanda ya fito fili yana yi wa Firaiminista barazana.
Abubuwan da ke faruwa a Haiti suna tayar da hankali har ma ga waɗanda ke bin yadda ayyukan gungun ƴan bindiga ke ƙaruwa a ƙasar a baya-bayan nan.
A nan, za mu yi duba ga yadda ƙungiyoyin bindiga suka mamaye muhimman yankuna a babban birnin ƙasar, da ma yankunan karkara.
Ƙungiyoyin ƴan bindiga sun taka mummunar rawa a tarihin ƙasar ta Haiti.
A cikin shekaru 29 na mulkin kama-karya na François Duvalier, wanda aka fi sani da Papa Doc, da ɗansa Jean Claude "Baby Doc" Duvalier, rundunar 'yan sanda da ake kira Tonton Macoutes sun yi amfani da matsanancin tashin hankali don kawar da duk wani da ke adawa da gwamnatin Duvalier.
An tilasta wa ɗansa Jean gudun neman mafaka a 1986, amma ƙungiyoyin sun ci gaba da yin iko iri-iri, wasu lokuta 'yan siyasar da suka kulla kawance da su ne ke ba su kariya da kuma karfafa musu gwiwa.
Ɓarkewar tashin hankali na baya-bayan nan ya faru ne bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaba Jovenel Moïse a ranar 7 ga Yulin 2021.
Ƙungiyar sojojin hayar Colombia ce ta harbe shugaban ƙasar a gidansa da ke wajen birnin Port-au-Prince bayan da ya fara yin Alla-wadai da abin da ya kira 'baƙaken dakaru' a cikin Haiti.
Yayin da aka kama ƴan Colombia da kuma sauran wasu da ake zargi, binciken da aka gudanar kan kisan da aka yi masa bai gano wanda ya tura aka kashe shi ba.
Rikicin ƴan bindiga ya zama ruwan dare lokacin mulkin shugaba Moïse, sai dai giɓin shugabanci da kisan sa ya haifar, ya janyo waɗannan gungun ƴan bindiga kwace iko da muhimman yankuna da kuma zama masu tasiri.
Kuma ba su dauki kujerar shugaban ƙasar da wata daraja ba.
Biyo bayan tsaikon da aka samu na gudanar da zaɓukan ‘yan majalisu, wa’adin dukkanin zaɓabbun jami’ai ya kare, wanda hakan ya sa yanzu ba a san inda hukumomin ƙasar suka dosa ba.
Tun bayan kisan Jovenel Moïse, Ariel Henry ne ke jagorantar ƙasar ta Haiti.
Shugaba Moïse ne ya naɗa Mista Henry a matsayin Firaiminista jim kaɗan kafin a kashe shi, amma ba a zaɓe shi ba, don haka wasu ke nuna shakku kan sahihancinsa.
Masu adawa da shugabancin Ariel Henry na ƙaruwa yayin da zaɓen da ya yi alkawarin gudanarwa ya kasa yiwuwa
Ba ya ga haka, rashin tsaro ya ƙaru, abin da ya tilastawa dubun-dubatar ƴan Haiti tserewa gidajensu.
Ɗaya daga cikin wanda ke adawa da Mr Henry shi ne Jimmy Chérizier, wani tsohon jami'in ɗan'sanda wanda ya zama shugaban ƴan bindiga bayan da aka kore shi daga aiki.
Jimmy wanda aka fi sani da Barbecue, ya jagoranci G9, kawance na ƙungiyoyi tara da aka kafa a 2020 wanda aka ruwaito yana da alaƙa da jam'iyyar marigayi Moïse' ta Tèt Kale.
Tun da farko, Barbecue ya yi adawa da Firaminista Henry.
Shugaban 'yan ƙungiyar ya yi amfani da kisan Moïse, domin karfafa gwiwar mabiyansa su shiga abin da ya kira "tashin hankali na halal".
Hare-hare da kuma wawason abinci sun yaɗu, musamman ma a Port-au-Prince, babban birnin ƙasar, inda Barbecue yake da karfi.
A watan Oktoban 2021, an hana Ariel Henry ajiye fure a wajen wani abin tunawa, lokacin da wasu ‘yan ƙungiyar Jimmy Chérizier ɗauke da muggan makamai suka fito kwatsam suka yi ta harbi a iska.
Sanye da wata riga mai launin fari tare da mambobin ƙungiyarsa, daga nan ya yi gaba don ajiye furen - wani abin nuna iko.
Ƙungiyarsa ta G9 ta kasance tana kazamin yaƙi da G-Pèp, wata ƙungiya ƴan bindiga da suke adawa da juna waɗanda aka ruwaito suna da alaƙa da ɓangarorin da suka nuna adawa da kisan shugaba Moïse.
Faɗa da kuma gumurzu tsakanin ƙungiyoyin biyu kan yankuna ba sabon abu bane kuma ya tashi daga yankunan makwabta matalauta zuwa tsakiyar Port-au-Prince.
An rufe makarantu da kuma asibitoci sannan sama da mutum 10,000 suka tsere gidajensu a 2023, a cewar Kungiyar Kula da Kaurar Jama'a ta Duniya (IOM).
Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta shaida wa BBC cewa sai da jami'anta suka tattauna da ɗaruruwan ƙungiyoyin ƴan bindiga kafin su samu damar kai kayan agaji.
A wani abu na ƙara karfafa ikonta, ƙungiyar G9 ta kuma toshe hanyar shiga tashar mai ta Varreux a 2022, wanda ya haifar da ƙarancin mai tare da hana isar da kayayyaki, kamar magunguna da ruwan sha.
Rundunar 'yan sandan ƙasar Haiti - wadda bisa kididdigar shekarar 2023 kawai tana da jami'ai 9,000 da ke aiki a ƙasar mai mutum miliyan 11 - ta yi kokarin tunkarar 'yan ƙungiyar, waɗanda ke ɗauke da manyan makamai da aka shigo da su ba bisa ka'ida ba daga Amurka.
An kiyasta cewa kashi 80 na babban birnin ƙasar na karkashin ikon gungun ƴan bindiga kuma mutane da ke rayuwa a waɗannan yankuna sun fuskanci cin zarafi, a cewar shugabar hukumar bayar da agajin jin kai na MDD, Ulrika Richardson.
Ms Richardson ta ce an samu ƙaruwar cin zarafi na jima'i da kashi 50 tsakanin 2022 zuwa 2023, inda ƴan bindigar suka fi afka wa mata da ƴan mata.
Mista Henry ya sha yin kiran neman taimako daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin kawo karshen rikicin, sai dai har yanzu Bahamas, Bangladesh, Barbados da Chadi ne kaɗai suka faɗa wa MDD a hukumance cewa suna da shirin aika jami'an tsaro.
Sai dai har yanzu babu waɗanda suka isa ƙasar.
A wannan lokaci na ƙaruwar tashin hankali, Mista Henry ya kai ziyara zuwa Kenya domin neman taimakon jami'ai a can da su yi alkawarin cewa za su tura jami'an ƴansanda 1,000 zuwa Haiti.
Yayin da ƴan ƙasar Haiti ke matukar buƙatar ƙarin tsaro, wasu na nuna damuwa kan batun aika jami'an tsaron ƙasashen waje.
Haiti, wadda ta samu 'yancin kai daga Faransa bayan nasarar da aka samu na daina bautar da mutane a shekara ta 1791, Amurka ce ta mamaye ta daga 1915 zuwa 1934.
Shiga tsakanin sojojin Amurka na baya tsakanin 1994 da 2004 ya kuma sa mutane da yawa na yin taka-tsan-tsan da duk wani batu na shiga tsakanin waje.
Wasu masu sukar Mista Henry na fargabar cewa yana son ya yi amfani da ƴan'sandan Kenya domin ƙara samu karfi, daidai lokacin da zanga-zangar kiran ya yi murabus ke ƙaruwa.
Jimmy "Barbecue" Chérizier na ɗaya daga cikin mutanen da suka zargi Ariel Henry da kokarin assasa ikonsa ta hanyar gayyato jami'an tsaron ƙasashen waje.
A 2022, shugaban ƙungiyar ƴan bindigar ya gabatar da shirinsa na "zaman lafiya", yana mai ba da shawarar cewa a yi wa mambobin ƙungiyarsa afuwa tare da kafa "majalisar masu hikima" tare da wakilai daga yankuna 10 na Haiti.
A lokacin, ya bayar da shawarar cewa a bai wa ƴan ƙungiyarsa mukamai a cikin gwamnati.
Tun wancan lokacin, ya ci gaba da matsa lamba, inda yake kokarin gabatar da kansa a matsayin mai son kawo sauyi wanda ke da burin kawar da abin da ya kira "shugaba da ba halastacce ba".
A ranar 1 ga watan Maris, Chérizier ya ce zai ci gaba da "yaƙi da Ariel Henry".
"Yaƙin zai ɗauki tsawon lokaci," in ji shi.
Kawo yanzu dai ba a san inda Mr Henry yake ba, sai dai ganin dubban fursunoni da suka tsere da kuma kiran da shugaban G9 yake yi a fili na cewa ya sauka daga mulki, yunkurin Firaministan na assasa doka cikin gaggawa ya ƙara yin nisa.