Newcastle ta ci ƙwallo takwas mafi yawa a Premier kawo yanzu

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United ta je gidan Sheffield United ta sharara 8-0 a wasan mako na shida ranar Lahadi a gasar Premier League.
Jerin wadanda suka ci wa Newcastle United kwallayen da lokacin da suka zura a raga
- Minti na 21 Sean Longstaff
- Minti na 31 Dan Burn
- Minti na 35 Sven Botman
- Minti na 56 Callum Wilson
- Minti na 61 Anthony Gordon
- Minti na 68 Miguel Almiron
- Minti na 74 Bruno Guimaraes
- Minti na 87 Alexander Isak
Kungiyar St James Park ta zama ta farko a tarihin Premier League da 'yan wasa takwas da-ban-da ban da suka zura kwallo a raga a wasa ɗaya a gasar.
Tun farko ƙungiyoyi biyu ne ke riƙe da tarihin 'yan wasa bakwai da kowanne ya zura kwallo a raga a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Mai riƙe da tarihin ita ce Chelsea da ta doke Aston Villa a Disambar 2012 da wanda Manchester United ta caskara Southampton a Fabrairun 2021.
Cikin wasa shida da fara kakar nan Newcastle ta yi rashin nasara a hannun Manchester City a Etihad da Liverpool a St James Park da wanda Brighton ta yi nasara a kanta.
Wadda ta hada maki tara ta fara da doke Aston Villa da Brentford da kuma Sheffield United.
Newcastle, wadda wannan sakamakon ya sa ta yi sama zuwa mataki na takwas a teburin Premier ta ci kwallo 16 aka zura mata tara, kenan tana da rarar kwallo tara kenan.
Ita kuwa Sheffield tana ta karshen teburi ta 20, wadda ba ta ci wasa ko daya ba da canjaras daya da cin kwallo biyar aka sharara mata 17.
Wannan shi ne wasan da aka ci kwallaye da yawa a gasar Premier, kuma wadda ƙungiyar waje ta shararasu.
Haɗuwa ta ƙarshe da suka yi a Premier League 2020/2021
Premier League Ranar Laraba 19 ga watan Mayun 2021
- Newcastle 1 - 0 Sheff Utd
Premier League Talata 12 ga watan Janairun 2021
- Sheff Utd 1 - 0 Newcastle
Ranar Laraba 27 ga watan Satumba Newcastle za ta karɓi baƙuncin Newcastle United a League Cup, kwana uku tsakani ta fuskanci Burnley a Premier League.
Haka kuma Newcastle za ta karɓi bakuncin Paris St Germain a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League ranar Laraba 4 ga watan Oktoban 2023.










