Abin da ya sa mazan Tajikistan ke zama masu tsattsauran ra’ayin addini

Muhammadsobir Fayzov, looking neatly presented in sunglasses and a light coloured shirt and black bodywarmer, touching the bonnet of a white car on a street with modern buildings

Asalin hoton, Muhammadsobir Fayzov / VK

Bayanan hoto, Muhammadsobir Fayzov, wanda iyalinsa suka ce yana aiki a matsayin mai aski, cikin wani hoto a shafinsa na sada zumunta da aka wallafa a manhajar VK ta yaɗa zumunta ta Rasha.
    • Marubuci, Grigor Atanesian
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian

Wasu ƙofofin ƙarfe biyu da aka dasa jikin bangon wani gida a ƙauyen Mahmadshoi-Poyon kusa da Dushanbe, babban birnin Tajikistan, lokacin da BBC ta kai ziyara, an datse ƙofofin.

A nan Muhammadsobir Fayzov ya girma. Ɗaya ne cikin ƴan Tajiksitan huɗu da ake zargi da kai hari a wani wajen waƙe-waƙe a birnin Moscow cikin watan Maris, inda aka kashe mutum aƙalla 145.

Masu gabatar da ƙara sun ce Fayzov, wanda a lokacin yake ɗan shekara 19, yana cikin wata ƙungiya da ke harbin masu zuwa wajen raye-raye tare da kai masu hari da wuƙa kafin su cinna wa ginin wuta.

Yan Tajikistan na cikin mutanen da aka zarga da kai hare-hare a baya-bayan nan a Iran da Instanbul kuma cikin waɗanda aka kama kan zargin kitsa hare-hare a Turai.

Ƙwararru sun ce matasan Tajikistan na shiga ƙuniyar IS-K, reshen kungiyar IS a Afghanistan wadda ke iƙirarin kai hari a Moscow. Amma me ya sa?

Brown metal gates in concrete wall of house where Muhammadsobir Fayzov lived
Bayanan hoto, Fayzov ya tashi a wani ƙauye kusa da Dushanbe, babban birnin Tajikistan - danginsa sun ce ba ya riƙo da addini kuma yana son ƙwallo

Dangin Fayzov na ɗari-ɗarin yin magana da ƴan jarida lokacin da muka kai ziyara. Ƴan sandan Tajikistan sun gayyaci mahaifiyarsa domin yi mata tambayoyi.

A tsaitsaye, ɗaya daga cikin ƴan uwansa ya yi bayani cewa Fayzov - mafi ƙarancin shekaru cikin yara biyar - ya je Rasha shekaru biyu da suka gabata kuma yana aiki a matsayin mai gyaran gashi a garin Teykovo a arewa maso gabashin birnin Moscow.

Ya ce ba ya riƙo da addini. Kakarsa, cikin kaduwa, ta ƙara da cewa mutum ne da ke son ƙwallon ƙafa.

A masallaci, Imam Saidrahman Habibov ya amince cewa Fayzov ba mutum ne mai addini ba amma wasu lokutan yana taimaka wa daya daga cikin ƴan uwansa sayar da carbi.

Danginsa fitattu ne a garin, yayin da mahaifin Fayzov ya taɓa koyar da harshen Rashanci a wata makaranta da mahaifiyarsa ke tafiyar da ɗakin karatunta.

Shugaban makarantar, Abdulaziz Abdulsamadov ya ce yana son lissafi kuma yana da burin zama likita.

"Zai yi wuya a ce ya yi abu makamancin haka, sai dai idan ya sauya sosai bayan da ya bar makaranta," ya ce.

Dalerjon Mirzoyev’s parents, Barot and Gulrakat, pictured with sad expressions outside a building with light coloured walls
Bayanan hoto, Gulrakat, mahaifiyar Dalerjon Mirzoyev (dama) ta ce mutum ne da "ba zai ma iya raunata ƙwaro ba"

Dalerjon Mirzoyev, 32, wani ne cikin mutum huɗu da ake zargi. Yana rayuwa da mai ɗakinsa da yara huɗu a Galakhona, wani ƙauye da ke wajen Dushanbe. "Ba ya iya kashe kaza, ba zai iya kashe ƙwaro ba," kamar yadda mahaifiyarsa Gulrakat ta faɗa mana.

Tsawon shekara 10, Mirzoyev yana aiki a Rasha tsawon wata shida na kowace shekara, a baya-bayan nan yana tuƙa tasi a Novosibirsk, kamar yadda iyalinsa suka faɗa wa BBC.

Wansa Ravshanjon shi ma an zarge shi da nuna tsattsauran ra'ayi. Dangin sun ce ba su ji ɗuriyarsa ba tun ƙarshen shekarar 2016, watanni bayan da shi ma ya koma Rasha.

Hukumomin Tajikistan sun ce ya je yi wa ƙungiyar IS aiki a Syria. Wasu rahotanni sun ce an kashe shi a 2020.

Two emergency workers in yellow jacks and hats in front of the burnt out remains of the Crocus City Hall concert venue, 23 March 23 2024

Asalin hoton, Russian Investigative Committee / Reuters

Bayanan hoto, Maharan sun buɗe wuta kan mahalarta taron raye-raye a ɗakin taro na Crocus City sannan aka cinna wa ginin wuta

Sauran mutanen biyu da ake tuhuma da hannu a harin na Moscow, Saidakram Rajabalizoda mai shekara 30 da Fariduni Shamsidin mai shekara 25, su ma suna zaune kusa da Dushanbe.

Rajabalizoda yana aiki lokaci zuwa lokaci a wurin gine-gine a Rasha tun lokacin da yake shekara 18. Kawunsa ya faɗa wa BBC cewa an haramta masa shiga ƙasar saboda karya dokokin shige da fice tsawon shekara biyar kuma ya dawo cikin watan Janairu.

Makusantan Shamsidin ba sa son yin magana da BBC amma mutane a ƙauyensa sun shaida mana cewa yana aiki a gidan gasa burodi kafin zuwa Rasha neman aiki.

Wani ɗan uwansa ya ce ya shafe kwanaki a gidan gyaran hali amma an yi kuskure a tuhumarsa. Mutanen yankin sun ce an kulle shi saboda cin zarafi mai nasaba da lalata.

Muhammadsobir Fayzov in white hospital clothing, open to the waist, with his eyes closed and a catheter drainage bag on his lap, in court in Moscow on 25 March 2024

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Lokacin da aka shigar da Muhammadsobir Fayzov harabar kotu a keken guragu, sai ya yi kamar ba shi da sauran numfashi

Da mutanen huɗu suka bayyana a kotu, idanun Mirzoyev da Rajabalizoda sun yi baƙi sannan fuskar Shamsidin a kumbure take.

Fayzov na kan keken guragu, kamar ba shi da rai, da ledar fitsari a jikinsa. Idanunsa a rufe amma ɗaya cikinsu da alama ya ji rauni ko ɓatan dabo.

An wallafa hotunan bidiyon yadda zaman yin tambayoyin ya kasance a Telegram. Ɗaya ya nuna wani ɓangare na kunnen Rajabalizoda da aka yanke aka kuma yi amfani da ƙarfi wajen turawa a bakinsa, sannan wani hoto da ya nuna an ɗosana wa Shamdidin wutar lantarki.

Saidakram Rajabalizoda with a large bandage on one ear, with his eye swollen and bruised

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Saidakram Rajabalizoda ya bayyana a kotu da bandeji a jikin kunnensa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Iyalai a Tajikistan da ƴaƴansu suka shiga kungiyar IS a Iraƙi da Syria za su iya cewa "yaron kirki ne, ba shi da addini sosai kuma ba ya jajiɓo wa kansa matsala," in ji Edward Lemon, wani ƙwararre kan tsakiyar siya a jami'ar A&M da ke Texas.

Yana ganin akwai dalilai da yawa na tattalin arziki da siyasa da kuma tarihi da suka haɗu suka sa matasan Tajikistan suka zama masu rauni a hannun masu tsattsauran ra'ayi da ke ɗaukansu aiki.

A wani jawabi na baya-bayan nan, shugaban Tajikstan Emomali Rahmon ya ce "farfagandar tsattsauran ra'ayi" a shafukan sada zumunta ta ƙara yawan matasan da ke shiga IS da sauran ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a shekaru 10 da suka gabata.

A wannan lokacin, fiye da ƴan Tajikistan 1000 aka kashe saboda shiga ayyukan ƙungiyoyin mayaƙa a ƙasashen waje sannan dubbai sun yi ɓatan dabo, in ji shi.

IS ta ƙwace yankuna da dama a Syria da Iraƙi a 2014 kuma ta zama alaƙaƙai saboda munanan hare-harenta har da sace-sace da kuma fille kan mutane.

Bayan da aka murƙushe ta a 2019, IS-K ta soma ɗaukan sabbin ma'aikata. Sunanta IS-Khorasan - wani daɗaɗɗen yanki ne da ya haɗa yankunan da a yanzu ya zama Afghanistan da Iran da Tsakiyar Asia.

Imam Saidrahman Habibov pictured inside a mosque with wooden pillers and prayer mats on the floor
Bayanan hoto, Imam Saidrahman Habibov ya ce Fayzov ba mutum ne mai addini ba

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke jan ra'ayin matasan Tajikistan wataƙila na iya zama yadda addinin musulunci ke tafiya bisa tsarin doka, duk da cewa an amince da shi a matsayin addinin ƙasar a hukumance kuma galibin al'ummar Tajikistan musulmai ne.

Bayan rugujewar tarayyar Soviet, mummunan yaƙin basasa ya ɓarke a 1992, tsakanin ɓangaren hamayya ƙarƙashin jam'iyyar IRPT da kuma gwamnati ƙarƙashin Mista Rahmon.

Bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a 1997, ya ci gaba da zama shugaban ƙasa sai dai IRPT ta ci gaba da fuskantar matsin lamba da wariya. Gwamnati ta ayyanata a matsayin ƙungiyar ta'addanci a 2015.

A watan Mayu aka haramta amfani da hijabi bayan da aka haramta ajiye gemu mai tsawo ba a hukumance ba - tsawon lokaci.

President Emomali Rahmon in white clothing with his hands up in prayer, performing the Hajj

Asalin hoton, ©Tajik President’s Press Service

Bayanan hoto, Ana sa ido sosai kan yadda ake tafiyar da addinin Islama a Tajikistan amma Shugaba Emomali Rahmon ya yi aikin hajji sau huɗu
People add flowers to large display of tributes, on front of a building labelled Crocus City Hall

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Harin da aka kai kan Crocus City Hall shi ne mafi muni da aka taɓa kai wa Rasha tsawon shekaru

Talauci ma wani ɓangare ne na abin da ya yi tasiri. Duka mutanen huɗu da ake ƙara na tallafa wa iyalai masu yawa da suka dogara kan kuɗaɗen da ake biya can a gida.

Tajikistan ce ƙasa mafi talauci a tsakiar Asia kuma dubban ƴan ƙasar na zuwa Rasha neman aiki - galibi a ayyukan da ba na hukuma ba sannan suna jurewa mawuyacin yanayin aiki da ƙyama da ƙalubale.

Babban nauyi ne aka ɗora kan matasa sannan ma'aikata yan ci-rani da dama na rungumar addini domin samun sauƙi, in ji Mista Lemon.

Sannan sai su zama masu rauni idan aka zo batun ɗaukan aiki da tura saƙonni na masu tsattsauran ra'ayi.

Men in t-shirts or shirts and trousers arrive to pray at a mosque in Dushanbe, Tajikistan, 2019

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Galibin al'ummar Tajikistan musulmai ne amma saka hijab da tara gemu abubuwa ne da aka tsawatar a kai

Hare-haren da aka kai kan wasu majami'u biyu da wuraren ibada a yankin Dagestan na Rasha a ranar 23 ga watan Yuni sun gamu da raɗe-raɗi kan ko masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama na da laifi.

Sai dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin harin. Hukumomin Rasha sun ce an kashe mahara biyar, har da ƴan uwan shugaban yankin Sergokalinsky na Dagestan.

Sai dai ana ci gaba da bayyana fargaba a wajen Rasha. Bayan harin na Crocus, IS-K ta fitar da wani hoto da ya nuna wani dishi-dishin hoto na London da Madrid da Paris da Roma. "Bayan Moscow, wane ne na gaba?,".

Fariduni Shamsidin appears at Basmanny District Court in Moscow on 24 March 2024

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Fariduni Shamsidin ya bayyana a kotu da fuska a kumbure

Bayan bayyanarsu ta farko a kotu, mutanen huɗu sun bayyana a hoto a watan Mayu.

Sun ce dukkansu an an shirya harin ne a Ukraine amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'Adama sun ce bai kamata a yadda da bayaninsu ba kasancewar bayanan da ke nuna an azabtar da su.

Ministan harkokin wajen Tajikistan ya bayyana damuwa kan yadda ake kula da mutanen da aka kama da kuma mummunar fahimtar da ake yi wa ƙasarsa da al'ummarta, a cewar rahotanni daga kafafen yaɗa labaran yankin.

Da aka tuntuɓe shi game da zargin azabtarwar a lokacin, kakakin Kremlin Dmitry Peskov bai ce komai ba.

Ba a sanar da ranar sauraron shari'ar ba.

Ƙarin rahoto daga Sohrab Zia.