Wane tasiri janyewar Shugaba Biden za ta yi kan zaɓen Amurka?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Amurka Joe Biden ya sa kallo ya koma sama game da babban zaɓen ƙasar.
Bayan kwashe makonni yana dagiya kan cewa shi ne zai tsaya wa jam'iyyar Democrats takara, a ranar Lahadi ya bayyana cewa ya janye aniyarsa ta tsayawa takara.
Ga tasirin da ake tunanin wannan mataki zai kan manyan masu ruwa da tsaki a cikin zaɓen: wato mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris, da Jam'iyyar Democrats da kuma Donald Trump.
Ganganci ne tsayar da Kamala Harris amma ƴan Democrat da yawa na son hakan
Aniyar da Shugaba Biden ya bayyana ta mara wa Kamala Harris baya ya ƙara ƙarfafa yiwuwar ta ta samun tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Ya ce zai ba ta goyon baya ɗari bisa ɗari, tare da bayyana zaɓen da ya yi mata a matsayin mataimakiyarsa shekara huɗu da suka gabata a matsayin mafi kyawun zaɓi da a rayuwarsa.
Akwai yiwuwar cewa ƴaƴan jam'iyyar Democrats da dama za su bi zaɓin shugaban ƙasar domin gudun yin wani abu za zai ƙara dagula al'amura yayin da suke da ƙasa da wata guda kafin babban taron jam'iyyar na ƙasa.
Akwai dalilai da dama da za su sanya hakan.
Bisa ƙa'idar kundin tsarin mulki ita ce ta farko a jerin waɗanda za su iya gadon shugaban ƙasar.
Amma miƙa ragamar yin takarar shugabancin ƙasa ga mace baƙar fata zai iya zama gurguwar shawara. Kuma da zarar aka yi hakan za ta kasance ɗaya daga cikin masu juya kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe kimanin dala miliyan 100 da aka tara zuwa yanzu.
Mene ne haɗurran? Ra'ayin jama'a ya nuna cewa Kamala Harris ba ta da farin jini sosai, kamar shi Biden kansa.
Kuma idan aka kwatanta ta da Donald Trump, kusan kamar yadda suke ne da shugaba Biden.

Asalin hoton, Reuters
Abu na biyu shi ne Kamala Harris ta samu tangarɗa a muƙaminta na mataimakiyar shugaban ƙasa. A farkon wa'adin mulkinsu an ɗora mata nauyin magance matsalar ƴan ci-rani da ke shiga Amurka ta kan iya da Mexico.
Wannan ya kasance gagarumin aiki a kanta, kuma wasu kura-kurai da aka samu da wasu kalamai da ta furta sun janyo mata suka.
Kuma ita ce mai kula da batun ƴancin zubar da ciki na gwamnatin, wanda wani lamari ne da ta yi ƙoƙari a wannan fannin. To amma abubuwan da suka faru tun farko ba za a manta da su ba.
Abu na ƙarshe shi ne - Kamala Harris ta taɓa yunƙurin tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2020, inda ta yi mummunar shan ƙasa.
Tsayar da Kamala a yanzu abu ne mai cike da haɗari sai dai kuma babu wata hanya mai sauƙi a yanzu. Kuma yiwuwar samun nasarar Donald Trump a zaɓen na ci gaba ƙarfi.
Za a iya samun hatsaniya a lokacin babban taron Democrat
Shekaru masu dama da suka gabata, babban taron jam'iyyun Amurka kan zamo lami.
Babban taron jam'iyyar Republican da aka gudanar a makon da ya gabata, inda a lokacin aka tsayar da Donald Trump shi ma haka ya wakana.
To amma da alama babban taron jam'iyyar Democrats da zai gudana nan da wata ɗaya mai zuwa a Chicago zai sha bamban.
Koda kuwa jam'iyyar ta Democrats ta yanke sahwarar mara wa Kamala Harris baya, zai yi wahala ta cimma nasarar yin yadda taso baki ɗaya.
Kuma idan Kamala ta kasa haɗa kan jam'iyyar, to kuwa taron zai zamo babu tabbas.
Zai zamo babban taron jam'iyya wanda ba a taɓa ganin irin sa ba a tarihi.
An rikirkita shirin ƴan Republican
An tsara babban taron jam'iyyar Republican na bana ne ta yadda babban abin da ya mayar da hankali shi ne tallata manufofin jam'iyyar da kuma sukar mutum ɗaya tilo, wato Shugaba Biden.
Sai dai yanzu da Biden ya yi watsi da batun takararsa, ya rikirkita wa Trump da muƙarrabansa shirinsu baki ɗaya.
Taron ya yi ƙoƙarin bayyana ɗan takarar Republicans a matsayin jarumi, hatta shigowarsa wurin taron ma abin kallo ne, gabanin shigowar fitaccen ɗan wasan damben nan na duniya Hulk Hogan.

Asalin hoton, Reuters
A bayyana take yadda aka so a fito da Trump a matsayin jarumi tare da kwatanta Biden a matsayin mai rauni.
To amma duk yadda za ta kasance a yanzu ɗan takarar Democrats zai zamo mutum ne mai ƙarancin shekaru fiye da na shugaban ƙasar.
Saboda haka kwatanta Trump a matsayin mai kuzari da Kamala ko wani daga cikin ƴan takarar Democrat a yanzu ba zai yi aiki ba.
Idan Kamala ta zama ƴar takarar shugaban ƙasa, to tabbas ƴan jam'iyyar Republican za su yi ƙoƙarin yin amfani da abubuwan da ake kallo gazawa ne na gwamnati mai ci wajen sukar ta.
Kuma duk wanda Democrats za su tsayar, babu shakka ƴaƴan jam'iyyar Republican za su zarge shi da hannu a yin rufa-rufa kan gazawar Biden sanadiyyar tsufa - da cewa sun saka ƙasar cikin haɗari.
A yanzu dai babu wanda ke da tabbas kan abin da zai faru.











