Wane ne zai iya maye gurbin Biden a matsayin ɗan takarar Democrats?

Vice-President Kamala Harris

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Ana Faguy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin ƙasar a wa'adin mulki na biyu.

Cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban ya ce ya yi hakan ne domin ''masalahar jam'iyyarsa da kuma ƙasarsa''.

Ya ce cikin shekara uku da rabi da ya yi yana jagorantar Amurka, ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.

''A yau Amurka na da ƙarfin tattalin arziki a duniya, mun kafa tarihi a fannin zuba jari domin sake gina ƙasarmu''.

Ga muhimman 'yan jam'iyyar Democrat da za su iya maye gurbin Biden.

Mataimakiyarsa, Kamala Harris

Mataimakiyar Shugaban ƙasar, Kamala Harris, wadda ke kan gaba - na ci gaba da samun tagamashi tsakanin 'yan jam'iyyar na ta maye gurbin Mista Biden.

A matsayinta na mataimakiyarsa, ta zama jagorar yaƙin neman zaɓen gwamnati, musamman a makonnin baya-bayan nan.

Ms Harris ta tabbatar da kasancewarta aminiya mai aminci ga shugaban, kuma ta yi kakkausar suka wajen kare shi bayan muhawararsa da Trump.

Bayan muhawarar ta yarda cewa shugaban ya kasance "cikin sanyan gwiwa a lokacin farawar" amma ta ce ya bayar da amsoshi masu mahimmanci fiye da Trump.

Kwanaki bayan muhawarar, yayin da aka ci gaba da nuna damuwa kan ƙarfin shugaban ƙasar na tsayawa takarar, Ms Harris ta jaddada goyon bayanta ga Mista Biden.

“Kun ga , Joe Biden shi ne ɗan takararmu. A baya mun kayar da Trump haka kuma yanzu ma za mu sake kayar da shi, a wannan karon,” kamar yadda ta bayyana ranar Talata.

“Ina alfaharin kasancewa a matsayin mai rufa masa baya takararsa."

Sunan Ms Harris ya ƙara fitowa fili a lokacin da Biden ya zaɓeta a matsayin mataimakiyarsa, to sai dai ta yi fama da ƙarancin ayyukan a lokacin mulkin.

Kashi 51 cikin 100 na Amurkawa ba su goyon bayan Ms Harris ba, yayin da kashi 37 cikin 100 ke goyon bayanta, kamar yadda alƙaluman ƙuria'r jin ra'ayin jama'a da FiveThirtyEight ta gudanar ya nuna.

Gwamnar Michigan, Gretchen Whitmer

Michigan Governor Gretchen Whitmer

Asalin hoton, Getty Images

Gretchen Whitmer, gwamnar Michigan, har tsawon wa'adi biyu, na ɗaya daga cikin 'yan jam'iyyar Diomkrats da ke samun karɓuwa a baya-bayan nan, inda masu sharhin siyasa ke ganin cewa za ta iya tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2028.

A baya ta yi wa Biden yaƙin neman zaɓe, kuma ba ta jin wani ɗar a harkokin siyasarta.

Ta taɓa bayyana wa jaridar New York Times cewa tana fatan ganin shugaban ƙasa daga cikin matasa a 2028, to amma ba ta bayyana cewa ko za ta iya tsayawa a lokacin ba.

A 2022, ta jagoranci yaƙin neman zaɓe wanda ya sa jam'iyyar Dimokrats ta mamaye majalisar dokokin jihar Michigan da kuma samun nasarar kujerar gwamna.

Hakan ya ba ta damar gudanar da wasu tsare-tsare da dokokin jihar, ciki har da dokar zubar da ciki da dokar mallakar bindiga.

Gwamnan California, Gavin Newsom

California Governor Gavin Newsom

Asalin hoton, Getty Images

Gwmanan California, Gavin Newsomna ɗay daga cikin ƙusoshin gwamnatin Shugaba Biden. A baya-bayan na ya sha fitowa a kafofin yaɗa labarai yana yaba wa Biden.

To sai dai Mista Newsom na ra'ayinsa na ƙashin kai a siyasance.

An taɓa bayyana shi cikin mutanen da ake ganin za su iya tsayawa takara a 2028, to amma yanzu mafi yawa daga cikin masu sharhin siyasa na ganin zai iya zama cikin masu karɓa daga hannun Biden.

Mista Newsom ya gina kansa a shekarun baya-bayan nan ta hanyar kafofin yaɗa labarai da muhawarar da yi tsakaninsa da gwamnan Florida, Ron DeSantis a shekarar da ta gabata.

A baya-bayan nan ya je Washington don ganawa da Mista Biden da wasu manyan gwamnonin jam'iyyar Dimokrats.

Shi ne kuma ya jagorancin gangamin yaƙin neman zɓen Biden na ranar 4 gta watan Yuli a Michigan.

Sakataren sufuri, Pete Buttigieg

Pete Buttigieg sits in front of microphone

Asalin hoton, Getty Images

Sha'awar takarar sakataren sufuri Pete buttiheig, ba ɓoyayyen al'amari ba ne.

Ya yi takara shugaban ƙasa a 2020, kuma ana bayyana shi a matsayin jami'an gwamnatin Biden da suka fi taka rawar gani.

Mista Buttigieg ya samu nasarar magance matsalolin da suka taso a fannin sufuri a matsayinsa na sakataren ma'aikatar.

Ya taimaka wajen magance matsalar gocewar jirgin ƙasa ajihar Ohio da karyewar gadar Baltimore da kuma rikicin kamfanin jirgin sama na 'Southwest Airlines' a 2022.

Gwamnan Pennsylvania, Josh Shapiro

Pennsylvania Governor Josh Shapiro

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnan Pennsylvania, Josh Shapiro ya ci gaba da samun tagomashi tun bayan zaɓensa a 2022 a jihar maras tabbas ga duka 'yan takara, wadda kuma Mista Trump ya cinyeta da 'yar ƙaramar tazara a zaɓen 2016.

Gwamnan - wanda ya baya ya riƙe muƙamin babban lauyan gwamnatin jihar - ya yi aiki da jam'iyyun ƙasar biyu a lokacin da yake riƙe da muƙamin.

Ya shiga kanun labarai a shekarar da ta gabata, lokacin da ya gaggauta sake gina gadar babbn titin Philadelphia da ta karye - wata babbar nasarar siyasa da wani gwamna ya samu a wa'adin farko.

Gaggauta gyarar ya samu yabo daga mutane da dama a matsayin gagagrumin aikin ci gaba da ya kai ga lissafa shi cikin wadanda za su iya tsayawa takara a 2028.

Gwamnan Illinois, JB Pritzker

Illinois Governor JB Pritzker

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnan Illinois, JB Pritzker, ya samu karɓuwa tsakanin 'yan jam'iyyar Dimokrat a baya-bayan nan musamman yadda ya riƙa kare Biden yana sukar Trump.

Biliniyan ɗan kasuwar - mamallakin otal ɗin Hyatt - ya yi ta wallafa saƙonnin suka ga Trump a ashafukan sada zumunta.

Bayan Muhawarar 'yan takarar, ya kira Trump da ''maƙaryaci'' sannan ya ce yana fuskantar ''tuhuma 34 a kotu''.

Kamar Ms Whitmer, Mista Pritzker yana da tarihin kammala ayyukan da ya shiya gudanarwa a kan lokaci , lamarin da ya sa jam'iyyar Democrat ke lissafa shi cikin waɗanda take alfahari da ayyukansu, kamar 'yancin zubar da ciki da mallakar bindiga.