Biden ya haƙura da takarar shugabancin Amurka

Asalin hoton, ..
Shugaban Amurka Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin ƙasar a wa'adin mulki na biyu.
Cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban ya ce ya yi hakan ne domin ''masalahar jam'iyyarsa da kuma ƙasarsa''.
Ya ce cikin shekara uku da rabi da ya yi yana jagorantar Amurka, ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.
''A yau Amurka na da ƙarfin tattalin arziki a duniya, mun kafa tarihi a fannin zuba jari domin sake gina ƙasarmu''.
''A lokacin da muka ɗauka muna mulki mun samar da muhimman abubuwa ciki har da dokar mallakr bindiga''.
Shugaban ya kuma goyi bayan mataimakiyar Kamala Haris a matsayin wadda za ta yi takarar shugabancin ƙasar a madadinsa.
''A yau ina son in jaddada cikakken goyon bayana ga Kamala a matsayin 'yar takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyarmu, lokaci ya yi da za mu haɗa kai wuri guda domin kayar da Donald Trump'', kamar ya wallafa a shafinsa na X.
To sai dai akwai wasu jiga-jigan jam'iyyar da ake ganin za su iya samun tikitin takarar, ciki har da gwamnonin jihohin California da Michigan da Illinois da Pennsylvania da ma sakataren sufurin kasar.
Akwai kuma mai dakin tsohon shugaban kasar, Michelle Obama da ake ganin za ta iya kayar da Donald Trump, kodayake ita ta ce ba ta da sha'awar tsayawa takara.
Shugaba Biden ya ce zai yi wa ƙasar jawabi game da batun cikin makon da za a shiga.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A makon da ya gabata ne gwaji ya tabbatar da cewa shugaban ya kamu cutar korona, inda ya killace kansa a gidansa da ke Delaware, to sai dai a ranar Juma'a ya ce ya samu sauƙi, kuma zai ci gaba da yaƙin neman zaɓen sa cikin makon mai zuwa.
A baya dai shugaban ya ce ''Allah ne kawai'' zai hana shi tsayawa takara bayan da aka yi matsa masa lamba kan ya haƙura da takarar, to sai dai daga baya ya ce zai iya haƙura da takarar bisa sharaɗin lafiya..
A baya-bayan nan shugaban na fuskantar kiraye-kiraye daga manyan 'yan jam'iyyarsa kan ya haƙura da takara saboda shekarunsa da kuma rashin kataɓus a muhawarar da ya yi da ɗan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump.
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa manyan 'yan jam'iyyar Democrats biyu a majalisar dokokin ƙasar - shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan ƙasar, Chuck Schumer da shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan ƙasar Hakeem Jeffries - sun gana da shugaban asirce domin bayyana masa damuwarsu game da takarar tasa.
Ita ma tsohuwar kakakin majalisar wakilan ƙasar, Nancy Pelosi, rohotonni sun ambato ta tana shaida wa shugaban cewa ba zai iya doke Trump a zaɓen watan Nuwamba ba.
Martanin Trump
Dan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump ya shaida wa kafar yada labaran CNN cewa Kamala Haris za ta fi masa saukin kayarwa fiye da Biden a zaben watan Nuwamban da ke tafe.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, tsohon shugaban na Amurka ya ce dama can Biden bai cancanci zama shugaban Amurka ba.










