Zan gina Najeriya mai nagarta – Bola Tinubu

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bai wa al'ummar ƙasar tabbacin sadaukar da kansa ga hidimta wa jama'a iya ƙarfinsa.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar bayan da hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Gogaggen ɗan siyasar mai shekara 70, ya samu kashi 36 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa kamar yadda sakamakon da aka sanar a hukumance ya nuna.

A jawabin nasa, zaɓɓen shugaban ƙasar ya yi wa ƴan Najeriya alƙawarin cewa mulkinsa zai kawo zaman lafiya da haɗin kai da kuma ci gaba kuma nan gaba idan mutane suka duba ci gaba n da suka samu, za su yi alfahari da kasancewarsu ƴan Najeriya.

Ya yi alƙawarin zama shugaba mai adali da zai mutunta buƙatun jama'a tare da yin ƙoƙari wajen gina Najeriyar da kowa zai yi alfahari da ita.

Ya ce "Ina cikin farin ciki na zaɓa ta da kuka yi a matsayin shugan Najeriya na 16 domin hidimtawa jamhuriyarmu da muke ƙauna. Wannan wani lokaci ne na haskakawar kowanne mutum da kuma ƙara tabbatar da dimokraɗiyyarmu. Ina muku godiya,"

Da take magana kan abokan takararsa da suka fafata a zaɓen, Tinubu ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gina ƙasar tare.

"Ko magoyin bayan Bola Ahmed Tinubu ne ko Atiku ko Obi ko Kwankwasiyya ko kuma wani ɓangare na siyasa, na san ka yi zaɓe ne domin ci gaban Najeriya da kyakkyawan fata ga ƙasar, ina muku godiya saboda nuna sadaukarwa ga dimokraɗiyyarmu,"

"Kun miƙa yardarku da amincewa kan burin da Najeriya ke da shi na dimokraɗiyya domin ciyar da ita gaba da kuma tunanin samun haɗin kai, da adalci da zaman lafiya da haƙuri da juna. Sabunta kwarin giwa ya tabbata a Najeriya.

Bola Tinubu ya kuma yaba wa INEC saboda gudanar da zaɓe mai adalci. A cewar shi, "Kurakuran da aka samu na da alaƙa da wasu lambobi ne da basu da yawan da za su lalata sakamakon ƙarshe na zaɓen. A kowanne mataki na zaɓukan, mun amince da duka ayyukan da aka yi da suke da muhimmanci da rayuwar dimokraɗiyyarmu."

'Waɗanda sakamakon zaɓen bai yi wa ɗaɗi ba su je kotu'

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriyar ya buƙaci mutanen da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen su garzaya kotu.

Ya ce "na san zai yi wahala ga wasu ƴan takarar su amince da sakamakon zaɓen. Haƙƙinku ne ku je gaban shari'a. Ya kamata a miƙa ƙorafe-ƙorafen sakamakon zaɓen ga kotu ba wai a tada rikici ba."

Ya tabbatar akwai rarrabuwar kai a tsakaninsu wanda a cewarsa, bai kamata a samu ba. "Mutane da dama sun fusata kuma ba su ji daɗi ba; Ina kira a gare ku. Mu mayar da hankali ga ci gaban Najeriya." in ji Tinubu.

Ya ce "Muna son ya zama kyakkyawan fatan da muke da shi ga ƙasar nan ya zama a gaba a wannan lokaci. Mu yi abin da zai mantar da mu damuwa ya samar da nutsuwa ga ƙasarmu."

Saƙon Tinubu ga matasan Najeriya...

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriyar ya bai wa matasa tabbacin cewa yana sane da matsalolin da suke fuskanta.

"Ga ku matasa wannan ƙasa, Na ji ku kwarai. Na san abin da yake damunku, kowa na fatan samun gwamnati mai kyau, a samu bunƙasar tattalin arziƙi da ƙasa mai aminci da za ta kare ƙimarmu a yau da gobe,"

"Na san cewa ga mafi yawanku Najeriya ta zama wani wuri da kuke fuskantar ƙalubale wanda ya hana ku cimma abin da kuke son cimmawa a rayuwarku,

"Sake fasalin ƙasarmu na buƙatar haɗin kai daga garemu baki ɗaya. Musamman matasa. Mu yi aiki tare za mu kai ƙasar nan inda ba ta taba zuwa ba a baya.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta tabbatar da jami'oi sun samu gashin kansu tare da mayar da hankali sosai ga batun ilimi da kuma magance yajin aikin da ƙungiyoyin malamai suke yawan zuwa.