Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya
Wannan shafi ne da zai kawo muku sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin tarayya kai-tsaye
Miliyoyin ƴan Najeriya na kaɗa ƙuri'unsu domin zaɓar shugaban ƙasa da ƴan majalisun tarayya.
Wannan ne zaɓe irinsa na farko da jam'iyyu huɗu ke kan gaba a zaɓen, saɓanin a baya da jam'iyyu biyu ne suka fi fafatawa.
Baya ga jam'iyyun APC da Bola Tinubu yake yi wa takara, da PDP wacce Atiku Abubakar yake yi wa takara, akwai kuma jam'iyyar NNPP da Kwankwaso ke yi wa takara, sai kuma Labour Party, wacce Peter Obi ke yi wa takara.
Baya ga zaɓen shugabana ƙasa, ana kuma zaɓar ƴan majalisar dattijai 109 da kuma ƴan majalisar wakilan tarayya 360.
A ranar 13 ga watan Maris ne kuma za a gudanar da zaɓen gwamnoni.
Wannan ne karon farko da hukumar zaɓen ƙasar INEC take amfanin da na'urar BVAS wajen tantance masu kaɗa ƙuri'a. Abin da ake fatan zai rage aringizon ƙuri'u da maguɗi da ake zargin ana yi a zaɓukan baya.
Dokokin Najeriya sun tanadi cewa dole ne duk ɗan takara ya samu 25% na ƙuri'un da aka kaɗa a jihohi 24 daga cikin 36 na Najeriya da Abuja kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Idan babu ɗan takarar da ya cika wannan ƙa'ida, to dole ne a je zagaye na biyu cikin kwana 21.