Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ta yi tafiyar awa bakwai saman raƙumi tana naƙuda
- Marubuci, Charlene Anne Rodrigues
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Lokacin da naƙuda ta kama Mona, ba ta da wani zaɓi sai raƙumi.
Mona mai shekara 19 ta yi tunanin tafiyar kilomita 40 zuwa asibiti, za a ɗauki sa’a huɗu daga gidanta da ke kan tsaunuka.
Amma saboda rashin kyawon hanya – maimakon haka an ɗauki tsawon awa bakwai cikin tsananin zafin naƙuda da kuma yanayi marar kyau.
“Duk takun ɗaya na raƙumin, nakan shiga tashin hankali,” in ji ta.
Lokacin da raƙumin ya maƙale, Mona ta ƙarasa ne da ƙafa tare da mijinta.
A lardin Mahweet da ke arewa maso yammacin Yemen, asibitin Bani Saad ne kaɗai cibiyar kiwon lafiya da dubban mata suka dogara.
Daga gidan Mona a ƙauyen Maaqara, ana iya zuwa asibitin da ke kan tsaunuka saman raƙumi da kuma a ƙafa.
A yayin da ta ke kan raƙumi, Mona ta yi fargabar lafiyarta da kuma rayuwar jaririnta.
“Hanyar ba kyau,” in ji ta, tana tuna “wahala da tashin hankalin da ta shiga tsawon tafiyar da ta yi.”
“Akwai lokacin da nakan yi addu’ar Allah ya ɗauki raina ya kare jaririna don na kauce wa zafin ciwo.”
Mona ta kasa iya tuna lokacin da ta isa asibitin, amma tana iya tuna farin cikin da ta ji bayan jin kukan jaririnta a hannun ungozoma da kuma likitan tiyata.”
Ita da mijinta suka raɗa wa jaririnta sunan Jarrah, sunan likitan da ya yi mata tiyata wanda ya ceci rayuwarta.
Hanyoyin zuwa asibitin daga ƙauyukan da ke kusa ƙanana ne. Wasu an toshe su saboda shekaru takwas na yaki da aka shafe tsakanin dakarun da ke samun goyon bayan Saudiyya da kuma mayaƙan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.
Mata da dangi da kuma ƴan sa-kai kan taimaka wa masu ciki tsawon sa’o’i cikin tsaunika zuwa asibiti.
Salma Abdu mai shekara 33, da suka raka wata mai juna biyu, ta ce a kan hanyarsu ta ga wata mata mai ciki da ta mutu a cikin dare a kan hanya.
Salma ta yi kira ga mutane su tausayawa mata da yara.
“Muna buƙatar hanyoyi da asibitoci da wuraren shan magani. Kamar a maƙale muke a wannan tsaunin. Waɗanda ke da sa’a ne ke haihuwa lafiya, bayan sun ci uƙuba da bala’i a hanya,” in ji ta.
Wasu iyalai suna da halin biyan kuɗin asibiti amma ba su da halin isa wurin.
Duk mace ɗaya tana mutuwa cikin sa’a biyu lokacin haihuwa daga matsalolin da za a iya karewa, a cewar Hicham Nahro na hukumar kula da yawan jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) a Yemen.
Mista Nahro ya ce yawanci mata a ƙauyukan Yemen ba su zuwa awo ko neman shawarar likita sai lokacin da suka fara jini ko kuma suna cikin tsananin ciwo.
Kusan rabin yawan haihuwar da ake yi ne ke samun taimakon likita, kuma kashi ɗaya cikin uku ne ake haihuwa a asibiti, a cewar UNFPA. Kuma yawancin al’ummar Yemen na rayuwa ne nesa da asibiti.
Tun kafin yaƙi cibiyoyin kiwon lafiya a Yemen na fuskantar matsala. Rikicin, ko da yake ya tarwatsa da lalata asibitoci da hanyoyi, wanda ya kasance babban ƙalubale ga mutanen ƙasar.
Akwai ƙarancin ƙwararrun likitoci, da kayan aiki da kuma magani, kuma aikin gyaran hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa ya tsaya.
Asibiti ɗaya cikin biyar ne kawai kan iya bayar da cikakkiyar kulawa ga mace mai juna biyu da kuma jarirai, a cewar UNFPA.
‘Na zata ƙarshen rayuwata ke nan’
Labarin Mona ɗaya ne daga cikin irin matsalolin da mata ke fuskanta a Yemen. Mallakar mota abu ne mai wahala a Yemen, inda kashi 80 na ƴan ƙasar ke dogaro da tallafi.
Mijin Hailah ya yi amfani da ƴan kuɗin da yake da su waɗanda ya tara lokacin yana Saudiyya domin tabbatar da ya kai matarsa asibiti a babur.
Bayan isarsu asibitin Hadaka a Dhamar, nan take aka shiga da Hailah ɗakin tayata.
“Na zata ƙarshe na kenan,” in ji ta ƴar shekara 30. “Ban yi tsammanin da ni da jaririna za mu rayu ba.”
An sanar da ita tare da gargaɗi a watannin farko na juna biyu cewa haihuwa a gida yana da matsala zai iya sa zubar da jini sosai da sauran matsaloli.
Likita a asibitin ya ce Hailah da jaririyarta an ceci rayuwarsu ne a ƙurararren lokaci.
Ta raɗa wa jaririyarta sunan Amal.
“Na kusan rasa jaririyar da kuma rayuwata saboda wannan yaƙin, amma wannan jaririyar ta ba ni ƙwarin gwiwa,” in ji ta.
Yayin da ake fuskantar ƙarancin tallafi na ƙasashen waje, cibiyoyin lafiya kamar asibitin Bani Saad na fuskantar ƙalubale. Ma’aikata a asibitocin na fargaba game da makomar mata da jaririransu domin aikin yana masu yawa har su rasa wanda za su fara ceto.