An gurfanar da mutum 1,000 a kotu kan zanga-zangar Iran

.

Asalin hoton, Reuters

An gurfanar da mutum kimanin 1,000 a kotu, a Tehran, dangane da tayar da rikici a zanga-zangar adawa da gwamnati wadda ta mamaye Iran, a cewar mai gabatar da ƙara na birnin.

Ana zargin su ne da ayyukan zagon-ƙasa, ciki har da kisan jami'an tsaro da satar makamai.

Mahukunta dai ba su tabbatar da yawan mutanen da aka kama tun bayan fara zanga-zangar ba, sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun ce mutanen sun kai 14,000.

Wannan bayani na zuwa ne yayin da aka bizine yara biyu, waɗanda ake zargin jami'an tsaro da kashewa a arewa maso gabashin ƙasar ta Iran.

Wata ƙungiyar kare haƙkin bil'adama ta ce an kashe Kumar Daroftateh, mai shekara 16, ta hanyar harbin shi da bindiga lokacin zanga-zanga a birnin Piranshahr, inda daga baya ya rasu a asibiti.

Mutane sun rinƙa furta kalaman adawa da gwamnati a lokacin jana'izar tasa.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Kumar Daroftateh

Asalin hoton, Kurdistan Human Rights Network

A kudancin ƙasar kuwa, mutane sun taru a birnin Sanandaj wajen bizine Sarina Saedi, mai shekara 16.

Shaidu sun ce Sarina ta faɗi ne a lokacin zanga-zanga bayan harsashin jami'an tsaro ya faɗa a kanta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai wakilin BBC ya ce, a ƙoƙarin wanke jami'an tsaro daga lamarin an tursasa wa mahaifin Sarina yin bayani a talabijin, inda ya ce ita ce ta kashe kanta.

Kamfanin dillacin labarun kare haƙƙin bil'adama ta Iran (HRANA) ta ruwaito cewar mutum 284 ne aka kashe a ƙoƙarin jami'an tsaro na murƙushe zanga-zangar.

Haka nan an tabbatar da cewa jami'an tsaro 35 ne suka mutu zuwa yanzu. Zanga-zangar ta fara ne tun bayan da wata matashiya ta rasu a hannun jami'an hisbah, bayan zargin ta da rashin rufe jikinta yadda ya kamata.

Mahukunta dai na kallon zanga-zangar a matsayin wadda aka kitsa ta daga ƙasashen ƙetare.

Babban alƙalin ƙasar, Gholamhossein Mohseni Ejei, a ranar Litinin ya sha alwashin cewa 'kotuna za su gaggauta sauraren shari'o'in da suka jiɓanci zanga-zangar.'

Kamfanin dillancin labaru na Associated Press ya ruwaito Mohseni Ejei na cewa "za a hukunta dukkanin masu yunƙurin yin zagon-ƙasa ga gwamnatin ƙasar, waɗanda ke biye wa ƙasashen ƙetare."

Kamfanin dillacin labaru na Iran, Irna, ya ce kotun juyin-juya-hali na Iran ta fara shari'ar wasu mutum biyar a birnin Tehran, waɗanda laifukansu ke iya janyo masu hukuncin kisa.

.

Asalin hoton, WANA NEWS AGENCY VIA REUTERS

Sai dai zanga-zangar na ci gaba duk da barazanar gurfanar da mutane a kotu da kuma gargaɗi daga kwamandan dakarun juyin-juya-hali na ƙasar.

A ranar Asabar, manjo janar Hosseini Salami ya ce "yau ce rana ta ƙarshe ta wannan zanga-zanga" a wani jawabi da ya yi.

Ya ce "ka da wanda ya ƙara fitowa kan titunan."

A washe-gari an ga bidiyon ɗalibai da suka rinƙa yin zanga-zanga a faɗin ƙasar. An kuma nuno wani bidiyon na jam'ian tsaro a cikin farin kaya, suna kai farmaki kan dandazon masu zanga-zanga da barkono mai sa hawaye da sanduna a jam'iar Azad da ke birnin Tehran.

Zanga-zanga ta ɓarke a Iran ne bayan rasuwar matashiya Mahsa Amin a hannun jami'an hisbah na ƙasar.

An fara zanga-zangar ne jim kaɗan bayan bizine matashiyar, inda mata suka rinƙa yaga mayafansu domin nuna goyon baya ga marigayiyar.

Sai dai daga baya lamarin ya rikiɗe zuwa bore, irin wanda ba a ataɓa gani ba a ƙasar tun bayan kafuwar gwamnatin musulunci ta ƙasar.