Matan da suka aske gashinsu a duniya don adawa da gwamnatin Iran

Bayanan bidiyo, Matan da suka aske gashinsu a duniya don adawa da gwamnatin Iran
Matan da suka aske gashinsu a duniya don adawa da gwamnatin Iran

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mata a faɗin duniya suna zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran ta hanyar aske gashinsu suna nuna wa a shafukan sada zumunta.

Masu zanga-zangar sun fara ne bayan mutuwar Mahsa Amini a hannun hukumomi, wacce ƴan Hisban Iran suka tsare.

Waɗanda suka yanke gashin nasu sun haɗa da ƴan fim irin su Juliette Binoche da Marion Cottilard.

Amma kuma wannan salon nuna adawa yana shan suka a shafukan sada zumunta.