Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Afirka ta fi tsadar sufurin jirgin sama?
Sufurin jiragen sama a nahiyar Afrika yana da tsadar gaske fiye da kowane wuri a duniya.
Matafiya na biyan kuɗin tikiti mai tsada da kuma ƙarin kuɗin haraji.
Yanzu, ta kai ga tafiya zuwa wata nahiya ta fi sauki maimakon zuwa wata ƙasa a Afrika.
Alal misali, shiga jirgi daga Berlin, babban birnin Jamus zuwa Istanbul, birni mafi girma a Turkiyya, ba zai wuci mutum ya biya kuɗin jirgi dalar Amurka 150 ba, a tafiya da ba ta fi sa'a uku ba.
Amma yin irin wannan tafiya, mu ce daga Kinshasa, babban birnin Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo zuwa Legas, birni mafi girma a Najeriya, mutum zai biya kudin da ya kai dalar Amurka 500 ko 850, a tafiya ta sa'a 20.
Hakan ya sanya yin kasuwanci a Afrika zamantowa abu mai wahala da kuma tsada - kuma ba matafiya masu hannu da shuni ne kaɗai abin ya shafa ba.
Cibiyar Kula da Sufurin Jirage na Ƙasa da Ƙasa - wadda ke wakiltar kamfanonin jirage kusan 300 wanda ke da kashi 83 na sufurin jirage a duniya - ya kalubalanci cewa muddin muhimman ƙasashe guda 12 a Afrika suka tsaya don gyara harkar kasuwancinsu, to za su iya samar da ayyukan yi guda 155,000 da kuma bunƙasa tattalin arzikinsu da sama da dalar Amurka biliyan 1.3.
"Harkar sufurin jirage na taimaka wa tattalin arzikin kowace ƙasa. Yana kuma samar da aikin yi," in ji Kamil al-Awadhi, mataimakin shugaba na ƙungiyar ta IATA a Afrika da kuma Gabas ta Tsakiya.
Adefolake Adeyeye, mataimakiyar farfesa a fannin dokokin kasuwanci a Jami'ar Durham da ke Birtaniya, ya amince cewa ɗaukacin nahiyar Afrika na samun koma baya da rashin ci gaba da ya kamata saboda rashin kyawun yanayin sufurin jiragen sama.
"Alamu sun nuna cewa sufurin jiragen sama yana bunƙasa tattalin arziki. Kamar yadda muka gani a wasu nahiyoyi, kyawun sufurin jiragen sama na kawo ci gaba da bunƙasar harkokin yawon buɗe ido, wanda kuma zai samar da ƙarin ayyukan yi," in ji ta.
Rashin kyawun hanyoyi da rashin jiragen ƙasa a yawancin ƙasashen Afrika, ya tilasta wa wasu komawa amfani da jiragen sama.
Batun sauyin yanayi da ya yi wa Afrika mummunan tasiri, na nufin cewa kowa na buƙatar taka tsan-tsan da gurɓacewar yanayi da ayyukan mutum kan haifar, don haka kuma kowa zai bukaci shiga jirgin sama.
Sai dai duk da cewa kashi 18 na al'ummar duniya na rayuwa a Afrika, tana da ƙasa da kashi biyu a ɓangaren sufurin jiragen sama a duniya, kuma a cewar Shirin Kula da Muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce nahiyar na da kashi 3.8 na hayaki da ake fitarwa.
Hakan ya bambanta da na Amurka da ke da kashi 19 da kuma China mai kashi 23.
Duk da cewa Afrika na da ɗimbin albarkatun ƙasa, amma ƙasashe 33 cikin 46 matalauta a duniya, a nahiyar suke, inda talauci ke ci gaba da zama babbar barazana ta kullu-yaumin ga miliyoyin mutane a faɗin nahiyar.
Amma ana ci gaba da samun masu rufin asiri da za su iya yin tafiye-tafiye da jiragen sama idan aka mayar da kuɗin daidai da na Turai ko kuma wasu wurare.
Ƙasashen Afrika na ta kokarin gyara ɓangaren sufurin jiragen sama tsawon gwamman shekaru, sai dai ba su kai ga nasara ba kawo yanzu.
"Ya kamata Afirka ta samar da kyakkyawan tsari domin shawo kan matsalolin sufurin jiragen sama idan suna son tattalin arzikin nahiyar ya bunƙasa," a cewar Zemedeneh Negatu, shugaban wata cibiya mai suna Fairfax da ke da zama a Amurka.
Ya ce har yanzu an tsara sufurin jiragen sama a Afrika ne kan yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashe, inda wasu ƙasashe ke kasa tafiyar da harkar yadda ya kamata, yayin da wasu kuma ke yin asara.
"Kowace gwamnati a Afrika na son ta ga tutarta a jikin jirgi a filin jiragen sama na Heathrow ko JFK, amma ya kamata su gane cewa hakan ba mafita ba ce."
Mr Zemedeneh ya kirayi kamfanonin jirage a Afrika da su yi koyi da takwarorinsu na Turai da kuma haɗa kai, kamar kamfanin jirgin Faransa da KLM na Netherlands, da kuma kungiyar jiragen sama na Sifaniya da suka samu haɗin gwiwa da kamfanin jiragen Birtaniya da Iberia.
Ya ce ko da a cikin kasuwannin Turai, haɗakar kamfanoni jiragen sama shi zai sa su tsira da kuma sauƙaƙa harkar sufuri.
Tsarin da Afrika take amfani da shi, ba shi da karfi duk da cewa ƙasashe 35 sun rattaba hannu kan tsarin ƙasuwa bai-ɗaya ta sufurin jiragen sama, wanda tsari ne da Kungiyar Haɗin Kan Afrika ta kawo don daidaita harkar da kuma samar da saukin farashin tikiti, wanda sai da ya ɗauki tsawon shekaru kafin a aiwatar da shi.
Jami'in cibiyar IATA, Mista Awadhi ya ce gwamnatoci suna jan kafa wajen yin aiki tare.
"Akwai rashin jituwa tsakanin ƙasashe, inda kowacce ke ganin ita ta san yadda za ta kula da harkar." In ji shi.
"Da yake abu ne na kasuwanci, daga baya tsare-tsaren gwamnatoci maras kyau na gurgunta harkar sufurin jiragen. Hakan na nufin babu alfanun sai kowa ya samar da kamfanin jirgin sama."
Akwai kamfanin jirgin sama ɗaya tilo a nahiyar Afrika da ke samun ci gaba, wato kamfanin jirgin sama na Habasha, wanda ya kamata sauran ƙasashe su kwaikwaya.
A cikin shekaru 15 da suka gabata, kamfanin ya ɗauki ma'aikata kusan 4,000. A yanzu kuma sun kai 17,000.
Duk da yake kamfanin jirgin na ƙasar ce, amma an sake masa mara yana harkar ba tare da wani katsalandan gwamnati ba.
Kamfanin jiragen na Ethiopia ya ninka yawan jiragensa na ɗaukar kaya da na fasinjoji kuma ya sanya Addis Ababa a matsayin cibiyar jiragen, wanda ke kawo kuɗaɗen ƙasar waje cikin ƙasar da kuma bunƙasa ɓangaren sufurin jiragen ƙasar.
Yayin da aka shiga ƙarnin shekara ta 2000, Habahsa ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afrika matalauta a duniya, amma a yanzu tana ɗaya daga cikin ƙasar da tattalin arziƙinta ke saurin haɓaka.
Mr Zemedeneh, wanda Ba'Amurke ne ɗan asalin Ethiopia da kuma ya taka rawa a matsayin mai bayar da shawara ga kamfanin jiragen Ethiopia, ya ce kamfanin ya yi rawar gani a ci gaban da aka samu.
"Kamfanin jiragen Ethiopia na samar da kuɗaɗen shiga da ya kai na miliyoyin dala a ƙasar, kuma hakan ya sanya ƴan ƙasar na tinkaho ganin cewa sun samar da kamfanin zirga-zirga na ƙasa da ƙasa," in ji shi.
Matafiya daga Afrika za su yi fatan cewa ci gaban da aka samu a ɓangaren sufurin jiragen ƙasa, zai rage tsadar kuɗin zirga-zirga kamar na Habasha da kuma nahiyar Asia - sannan za su iya zuwa duk inda suke so a cikin sauri da kuma sauki.