Netanyahu ya yi turjiya ga takunkumin Amurka a kan sojin Isra’ila

Asalin hoton, REUTERS
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ƙalubalantar duk wani matakin ladabtarwa a kan rojojin ƙasar sa, bayan rahotanni sun nuna cewa Amurka na shirin daina bayar da tallafi ga ɗaya daga cikin cibiyoyin sojin.
Da yake jawabi a ranar Lahadi, ya ce "Zan yaƙi wannan yunƙuri da dukkan ƙarfi na".
Tun da farko dai jaridar Axios ta wallafa wani labari da ke cewa Amurka na shirin ɗaukar matakan ladabtarwa a kan rundunar Netzah Yehuda ta dakaraun sojin Isra’ila a bisa zargin keta haƙƙin ɗan Adam a gaɓar yamma da kogin Jordan.
BBC ta gano cewa Amurka na shirin ɗaukar matakin ne a ƙarƙashin dokar ƙasar da tayi tanadin janye tallafi daga duk wata runduna da aka samu da keta haƙƙin ɗan Adam.
Ko a makon jiya da aka tambaye shi a kan rahotannin da ke nuna Amurka za ta hukunta rundunar da ta keta haƙƙin ɗan Adam, ta hanyar janye tallafi, sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken ya ce: "N a riga na sha alwashi; ku jira ku ga matakan da za a ɗauka nan da kwanaki".
Washington wadda itace babba a jerin ƙawayen Isra’ila, ba ta taɓa dakatar da tallafi ga dakarun Isra’ilan ba a tarihi.
Rundunar sojin Isra’ila ta jajirce cewa dakarun ta dake Netzah Yehuda basu karya wata doka ba.
Kamfanin dillacin labaru na Reuters ya ruwaito rundunar sojin Isra’ila tana cewa "Rundunar mu bata da wata masaniya a kan wannan zargi, amma za ta ci gaba da gudanar da bincike a kan duk wani abu da ya saɓawa doka da ƙa’idar aiki.’’
Ministan tsaron Isra’ila, Yoav Gallant ya yi kira ga Amurka ta janye wannan aniya, yana mai cewa duniya tana kallon alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu da muhimmancin gaske.
Sanarwar Mr Gallant ta ce: "duk wani yunƙuri na sukar cibiyar sojin Isera’ila zai shafi rundunar sojin ƙasar bai ɗaya. Kuma bai dace a samu aminan juna da irin wannan hukunci ba ".
Wata majiya daga Amurka ta ce nan da kwanaki ake sa ran Mr Blinken ya sanar da takunkumin da za a ƙaƙabawa cibiyar sojin Isra’ilan ta Netzah Yehuda.












