Harin da Iran ta kai wa Isra'ila ceto ne ga Netanyahu

File photo of Benjamin Netanyahu (17 March 2024)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaiministan Israeli Benjamin Netanyahu yana fuskantar matsayin lamba ta fuskoki daban-daban

By Jeremy Bowen

BBC international editor

'Yan kwanaki da suka gabata ne Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ke cikin matsin lamba iri-iri.

Bayan wasu ma'aikatan agaji bakwai daga ƙungiyar World Central Kitchen sun mutu dalilin wani harin Isra'ila a Gaza a ranar 1 ga watan Afrilu, daga baya Shugaban Amurka Biden ya fito ya nuna bacin ransa kan ƙawayensu na kodayaushe.

A dai wannan ranar, harin Isra'ila kan ofishin jakadancin Iran da ke Damascus da ya kashe wani babban janar ɗinta kuma akalla mutum shida suka mutu daga cikin jami'ai, hakan ya karya dokokin ƙasashen duniya na kai hari kan ofishin jakadancin ƙasashe.

A wani iƙirari da Isra'ila ta yi wanda bai samu karbuwa ba, wai Iran na yunƙurin mayar da ofishin ne kamar wata mahaɗar sojojinta. Iran ta yi alƙawarin kai harin ramuwar gayya, amma hare-haren da aka kai kan kwamandojinta a baya sun janyo cecekuce sama da ɗaukar mataki.

A wajen Iran, kashe ma'aikatan agaji ne ya shafi harin da aka kai wa ofishinta da ke Damascus.

Fadar White House ta fitar da sanarwar bacin rai daga Shugaba Biden. Ya ji "bacin rai ya kuma karya masa zuciya". Ba wai wannan lamarin ne ya janyo bacin ran ba kawai. Isra'ila ba ta yin wani ƙoƙari wajen kare ma'aikatan taimako da kuma fararen hula Falasɗinawa.

Palestinians return to Khan Younis, 7 April

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Isra'ila na amfani da makaman da Amurka ke ba ta wajen lalata Zirin Gaza
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Firaiminista Netanyahu ya yi alƙawarin abubuwa za su sauya. Amma duk da haka Isra'ila ba ta dakata ba.

Yayin da yake fuskantar ɓacin rai daga Fadar White House, a gefe guda kuma Netanyahu yana shan matsi daga masu ra'ayin riƙau na cikin gida da suke goyon bayan majalisar da ke neman rusa gwamnatinsa ta haɗin gwiwa.

Ba suna adawa ba ne kawai da kai kayan agaji cikin Gaza. Sun yi amannar wannan yaƙi ya janyo jan ƙafa daga damar da Isra'ila take da ita ta samun wuraren da take mamayewa a Gaza. Wuraren Yahudawa ne 'yan kama-wauri-zauna da suka tashi a 2005 a matsayin wani bangare na yarjejeniyar janyewa daga yankin.

Ya zuwa ƙarshen makon jiya, Amurka ta ƙara matsin lamba. A ranar Alhamis Samantha Power - wadda ita ce babbar jami'ar da ke lura da harkokin agaji a Amurka - ta ce mummunan abu ne a ce yunwa ta fara mamaye wasu bangarorin Gaza.

Abu ne a buɗe ga Isra'ila da kuma ƙawayenta da ma maƙiyanta cewa wata shidan da ta yi na takure Gaza ya janyo matsalar abinci a duniya. Wannan ya ƙara haifar da jita-jitar cewa Amurka za ta iya sanya sharudda kan yadda Isra'ila za ta yi amfani da makaman da take ba ta.

A ranar Asabar da safe, gabanin Iran ta kai wa Isra'ila hari, jaridar New York Times ta bayyana damuwar da ake sake fuskanta musamman tsakanin fitattun mutanen jam'iyyar Democrats a majalisar Amurka. Musamman suna son a dakatar da samar wa Isra'ila makamai kuma a kyale Benjamin Netanyahu.

Kanun labaran da suka wallafa shi ne, "sai an riƙa sanya wa taimakon soji da ake bai wa Isra'ila sharadi". Wannan kanun labarai bai yi wa Netanyahu dadi ba, kuma ana ganin zai taɓa "alaƙar Amurka" da Isra'ila.

Yadda Amurka ke taimaka wa Isra'ila da kuma 'yancin da take da shi na kare kanta "ba ya nufin Shugaba Biden ya kyale Netanyahu ya riƙa cin karensa babu babbaka". in ji rahoton.

Ana haka sai harin da Iran ta kai wa Isra'ila ya taimaka wa firaiminista damar sake farfaɗowa.

A wani mataki na ƙarfafa gwiwa ta fuskar taimakon haɗin gwiwar soji, Amurka da ƙasashen Yamma da kuma ƙawayenta sun taimaka wajen harbo makamai 300 da Iran ta harba wa Isra'ilar.

Babu wani shugaba daga ƙasashen Larabawa da ya soki hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza sai sarkin Jordan. Amma an yi amfani da sararin samaniyar Jordan wajen dakile hare-haren da suka nufi Isra'ila.

Kiraye-kirayen da ake yi na gindaya wa Isra'ila sharuda lokacin ba ta taimakon makamai sai ya sauya zuwa maganar goyon baya.

Sai Netanyahu ya samu wata sabuwar dama a siyasance, kuma maganar Gaza ta bar kanun labarai na kwana ɗaya ko biyu.

Matsin lambar da yake fuskanta ta sauya. Ba wai an bar ta ba ne har abada, wataƙila mataki na gaba ga Isra'ila ya ninka waɗannan damuwa.

Shugaba Biden ya bayyana a zahiri abin da yake tsammain zai faru nan gaba. Isra'ila za ta ayyana kanta a matsayin wadda ta yi nasara a wannan mataki, amma ba za ta mayar da martani ba. Ya kuma bayyana cewa goyon bayan Amurka ga Isra'ila abu ne tabbatacce.

Tun a watan Oktoba Isra'ila take samun makamai da doyon bayan diflomasiyya wadanda suka sanya ta matawa da kira da bacin ran da Biden yake nunawa na a mutunta dokokin duniya da kuma kare fararen hula.

Kwanaki kaɗan bayan harin sojojin haɗin gwiwa daga ƙawayenta kuma maƙiyan Iran, Isra'ila ta nuna yadda ta yi watsi da duka shawarar Biden ta kada ta rama harin, kuma irin wannan ra'ayin sauran ƙasashen da suka taimaka mata a daren Asabar suke da shi.

Kamar Biden, Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak da Shugaban Faransa Emmanuel Macron sun kai jiragensu sun kuma dakile hare-haren da Iran ta kai, sun yi Allah-wadai da su, sannan sun nemi Isra'ila da ka da ta mayar da martani.

Israeli war cabinet

Asalin hoton, Israeli Government Handout

Wani abu da Netanyahu yake gani a tsawon lokacin da yake kan iko shi ne, Iran ita ce ta fi zama abokiyar hamayya mafi haɗari ga Isra'ila, ita ce a bayan shirin lalata ƙasar Yahudawa. Kuma Isra'ilawa da dama suna da wannan tunani.

Yanzu, bayan shekaru masu yawa da aka kwashe ana adawa da juna tun bayan Juyin Juya halin Isalama a 1979, a karon farko Iran ta kai wa Isra'ila hari na kai-tsaye.

Isra'ila ta ce tambayarta ba ta maganat ko za ta kai hari ba ce, yaushe za ta kai kuma ta yaya.

Majalisar yakin Isra'ila na ci gaba da muhawara kan yadda za a kai harin ba tare da nuna karfi sosai ba.

Netanyahu da muƙarabban gwamnatinsa na shirin dauke kai daga fatan abokansu wadanda suke taimaka musu a yaƙi da abokan hamayyarsu. Abokan adawarsa na cikin gida na fatan ganin an kai hari mummmuna ga Iran. Wani daga cikinsu na cewa Isra'ila ta kai hari na "rashin imani".

A daidai wannan lokacin ana ci gaba da fuskantar mummunan yanayin agaji a Gaza. Da hankalin duniya ya kauce daga kansa amma yanzu ya koma. Har yanzu sojojin Isra'ila na ci gaba da yaki a Gaza kuma suna kashe fararen hula.

A gefe daya kuma, mummunan rikici tsakanin Falasɗinawa da Yahudawa ya ɓarke a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Yakin Isra'ila da Hezbollah zai iya ƙaruwa shi ma.

Iran ta yi alƙawarin mayar da wani harin na ramuwar gayya matuƙar Isra'ila ta rama harin da ta kai mata.

Shugaban sojin Iran Hossein Baqeri ya ce abin da za a gani na hare-hare zai ba da mamaki sama da wanda aka gani a baya-bayan nan.

Wadannan wasu matakai ne da suke ƙara fadada yaƙi a Gabas ta Tsakiya da kuma ƙara jefa duniya cikin rikice-rikice masu zurfi.