Ƴan adawa na zanga-zanga a Georgia

Asalin hoton, Getty Images
Dubban masu zanga-zanga a Tbilisi babban birnin Georgia sun shafe dare suna tattaki a ginin majalisar dokokin ƙasar.
Sun kudiri aniyar hana ƴan majalisar damar shiga cikin zauren a yau domin hana su zartar da wani ƙudirin doka a kan ɗaukar nauyin ƙungiyoyin kare yancin ɗan Adam. Wanda suka ce zai yi hannun riga da turbar dimokuraɗiyya.
Sai dai sun fusnkanci turjiya daga ɗaruruwan ƴan sanda.
Matasan Georgia ne suke jagorantar zanga-zangar da aka shafe makonni ana yi, saboda tsoron da suke cewa ƙudirin dokar zai iya kawo cikas ga shirin ƙasar na shiga ƙungiyar tarayyar Turai a nan gaba.
Bidiyon da aka yaɗa ta kafar sada zumunta ya nuna yadda zanga-zangar ke gudana cikin dare, ga ɗimbin mutane suna rera taken ƙasar.
Amma wasu hotunan da suka bayyana sun nuna wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya, kuma sun rufe fuskkokin su, waɗanda kuma babu tabbacin abin da suke kitsawa.
A gefe guda kuma ƴan sanda ne cikin kayan sulke da motocin fesa ruwa, da zummar tarwatsa masu zanga-zangar idan har suka nemi hana ƴan majalisar shiga zauren don zartar da wannan ƙudirin doka.
Gwamnati dai ta ce akwai buƙatar wannan ƙudirin doka, idan har ana son tsaftace ayyukan ƙungiyoyinn fararen hula a ƙasar.
Masu zanga-zangar dai sun fito kan tituna ne domin amsa gayyatar jam’iyyun adawa, masu ganin kudirin a matsayin barazana.
Gwamnatin ta yi gargaɗin cewa za a kama duk wanda ya shiga duk wani abu da ya haifar da rikici.
Duk da haka, waɗannan mutanen sun ce suna murna da shigar su zanga-zangar.
Lasha, ya ce: "Ina da yaƙinin ba zasu zartar da wannan ƙudiri ba. Za mu ci gaba da zanga-zanga har iya ƙarfin mu. Za mu ci gaba da zanga-zanga har zuwa lokacin zaɓe."
Telka, ta ce: "Ina so Georgia ta kasance cikin Turai. Bana son zama a cikin Rasha. Kuma ina fata cewa a zamanin mu, za mu cimma nasarar ganin haske da samun ilimi. Kuma buri ne shi ne samun ilimi a Turai ba a Rasha ba. Don haka nake tambayar wannan gwamnatin, shin menene kuke jin tsoro cikin wannan lamari?"
Ana dai kamanta wannan ƙudirin doka da irin dokokin Rasha, kuma tuni Amurka da ƙungiyar tarayyar Turai suka yi tir da ita.











