Trump zai gana da Putin kan yakin Ukraine a Alaska

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaba Trump na Amurka ya ce zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, domin tattaunawa kan yakin Ukraine.

Shugabannin biyu za su yi ganawar ta gaba da gaba a karon farko tun bayan 2019, a jihar Alaska ta Amurka, ranar Juma'a – 15 ga watan nan na Agusta 2025.

Shugabannin biyu za su yi wannan ganawa ne bayan wa'adin da Amurka ta sanya wa shugaban na Rasha ya amince da yarjejeniyar dakatar da bude wuta ko ta kara sanya masa takunkumi, ya wuce ba tare da wata sanarwa ba a ranar Juma'a.

Gwamnatin Rasha ta ce a shirye take da wannan tattaunawa ta koli, kuma ta kara da cewa ita ma tana gayyatar shugaban na Amurka zuwa kasarta a wata rana nan gaba

Tun farko da yake magana kan shirin ganawar a fadarsa ta White House, Mista Trump ya ce yarjejeniyar za ta kunshi musayar wasu yankuna a tsakanin Rashar da Ukraine:

''Muna duba yankin da ake yaki a kansa tsawon shekara uku da rabi inda Rashawa da yawa suka mutu 'yan Ukraine da yawa suka mutu, la'akari da haka muna duba yadda za mu dawo da wasu.

''Da musayar wasu, abu ne mai sarkakiya gaskiya – ba abin da yake da sauki. Abu ne mai sarkakiya amma duk da haka za mu dawo da wasu – za mu yi musaya – za mu yi musayar wasu yankunan domin amfanin su biyun.'' In ji Trump.

Rasha ta kafe cewa lalle tana son cikakken iko da yankuna hudu na Ukraine da kusan a yanzu take iko da su, yayin da ita kuwa Ukraine din ke cewa dole ne ta kasance a wajen duk wata tattaunawa a kan sallama wasu yankuna.

Fadar gwamnatin Amurka na kokarin ganin ta shawo kan shugabannin Turai sun aminta da yarjejeniyar dakatar da bude wutar da za ta kai ga Ukraine din ta sallama wa Rasha wasu yankunan nata.

Abin da ba a sani ba shi ne ko hakan za ta samu daga bangaren Ukraine da shugabanin na Turai.

Rasha ta mamaye yankin Crimea na Ukraine a 2014, sannan ta kaddamar da mamaya gaba daya a watan Fabarairu na 2022.

Ana ganin Rasha ta kasa cimma gagarumar nasara a kan Ukraine din a fagen-daga, amma duk da haka ta kame kusan kashi 20 cikin dari na yankin kasar ta Ukraine – kuma duk irin martanin hare-haren da Ukraine ke yi wa sojojin na Rasha da suka kama wadannan yankuna Ukraine din ta kasa kora su baya.

A karkashin yarjejeniyar da za a yi ita ma Rasha sai ta hakura da wasu yankunan Ukraine da ta kame – yankin Kherson da Zaporizhzhia, inda a yanzu sojojinta suke.